• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ministan Kuɗi ya ƙaryata zargin ɓoye kuɗaɗen shiga na ƙasa

Wakilin Mu by Wakilin Mu
April 20, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Ministan Kuɗi ya ƙaryata zargin ɓoye kuɗaɗen shiga na ƙasa
Ƙaramin Ministan Kuɗi, Mista Taiwo Oyedele

Ƙaramin Ministan Kuɗi, Mista Taiwo Oyedele

Gwamnatin Tarayya ta mayar da martani kan wasu rahotannin kafafen yaɗa labarai da suka yi iƙirarin cewa wai ana karkatar da kuɗaɗen shiga na ƙasar nan ko kuma ana yin “karkashe kuɗi a ɓoye.”

Waɗannan rahotanni dai sun biyo bayan fassarar da aka yi wa sabon rahoton Bankin Duniya kan tattalin arzikin Nijeriya.

Ƙaramin Ministan Kuɗi, Mista Taiwo Oyedele, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa waɗannan rahotanni ba gaskiya ba ne, kuma sun samo asali ne daga rashin fahimtar yadda tsarin kasafin kuɗi da rabon kuɗi yake aiki.

Ina Kuɗaɗen FAAC Suke Tafiya?

Ministan ya fayyace cewa kuɗaɗen da ake cirewa daga asusun tarayya (FAAC) ba ɓacewa suke ba, ana amfani da su ne wajen kashe kuɗi da doka ta amince da su da suka haɗa da: zuba jari da tanadi don samar da gobe mai kyau; harkar tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya; kuɗin da ake bai wa hukumomin tara haraji; turawa ma’aikatu da rassan gwamnati (MDAs) kuɗaɗen da ya kamata a mayar masu.

Oyedele ya jaddada cewa tura wa jihohi da sauran matakan gwamnati kuɗaɗe ba wai sace su ba ne; harka ce ta tsarin mulki da ya wajaba a biya.

Ministan ya zargi wasu masu sharhi da amfani da tsofaffin bayanai yayin da suka yi kunnen uwar shegu da sababbin gyare-gyaren da gwamnati ta fito da su a farkon shekarar 2026.

Ya ce: “Dokar da Shugaban Ƙasa ya sanya wa hannu kwanan nan don kare kuɗaɗen man fetur za ta ƙara gaskiya a harkar kuɗi, kuma ana sa ran za ta ƙara kuɗaɗen da ake rabawa da kimanin kashi 0.4% na arzikin ƙasa (GDP) a kowace shekara.”

Ministan ya ce babban saƙon rahoton Bankin Duniya shi ne cewa Nijeriya na kan hanya madaidaiciya.

Ga wasu daga cikin nasarorin:

 1. Haɓakar Tattalin Arziki: Ɓangarori daban-daban na bunƙasa.

2. Saukar Farashin Kaya: Ko da yake har yanzu akwai tsada, matakan da ake ɗauka sun fara rage raɗaɗin hauhawar farashi.

 3. Rage Basussuka: A karon farko cikin shekaru goma, bashin da ake bin Nijeriya idan aka kwatanta da arzikin ƙasa ya ragu.

Gwamnatin Tarayya ta ce tana nan kan bakan ta na tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkar kuɗi.

Ta buƙaci manema labarai da jama’a da su rika tantance bayanai kafin yaɗawa don gudun janyo rudani a ƙasa.

Tags: kuɗaɗen shigaMinistan KuɗiTaiwo Oyedelezargi
Previous Post

Ɗan bindiga a Amurka ya kashe yara 8, ciki har da 7 daga cikin ‘ya’yan sa

Next Post

Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma

Related Posts

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai

May 12, 2026
Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

May 12, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙwaƙudumar kasa biyan tulin bashin da manyan bankuna suka bayar laifin daraktoci da manyan masu hannayen jarin su ne, ba laifin CBN ba

May 8, 2026
Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya

May 7, 2026
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda ƙarfin laƙani da dafa’in CBN ke hana girgizar tattalin arzikin duniya yi wa Nijeriya barazana

May 6, 2026
Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris

May 5, 2026
Next Post
Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma

Isra’ila ta tabbatar da sahihancin hoton soja yana bugun gunkin Yesu da guduma

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!