• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Tinubu ya umurci masu riƙe da muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara su yi murabus kafin 31 ga Maris

ALI KANO by ALI KANO
March 17, 2026
in Siyasa
A A
0
Tinubu ya bayyana sunayen ƙasashen da ya tura jakadu 65 a duniya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umurci duk masu riƙe da muƙaman siyasa a ƙarƙashin gwamnatin sa da ke da niyyar tsayawa takara a zaɓuɓɓukan gama-gari na 2027 da su yi murabus daga muƙaman su kafin ko a ranar 31 ga Maris, 2026.

Wannan umurni ya yi daidai da tanade-tanaden Sashe na 88(1) na Dokar Zaɓe ta 2026, tare da jadawalin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC) ta fitar dangane da zaɓen fidda gwani na jam’iyyun siyasa kafin zaɓuɓɓukan 2027.

A cikin wata takarda da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya rattaba wa hannu, wadda Babban Sakatare na Babban Ofishin Ayyuka, Dakta Ibrahim Abubakar Kana, ya fitar, an bayyana cewa sharaɗin yin murabus ya shafi dukkan nau’o’in masu riƙe da muƙaman siyasa na shugaban ƙasa da ke son shiga zaɓen fidda gwani ko neman takara a kowane muƙamin zaɓe.

Waɗannan sun haɗa da: Minista, Ƙaramin Ministoci, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa, Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa, Mataimaki na Kusa ga Shugaban Ƙasa, Darakta-Janar, da Shugaban Hukuma (CEO) na hukuma, kamfani, da cibiyar gwamnati na tarayya, tare da duk sauran masu riƙe da muƙaman siyasa na shugaban ƙasa.

Saboda haka, ana buƙatar duk wanda wannan umurni ya shafa da ya gabatar da takardun murabus ɗin sa ta hannun Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya kafin ko a ranar 31 ga Maris, 2026, ba daga baya ba.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa wannan mataki yana da muhimmanci domin tabbatar da cikakken bin dokokin zaɓe, ƙarfafa gaskiya a harkokin siyasa, da kuma samar da dama bai-ɗaya ga duk masu neman takara kafin zaɓuɓɓukan.

Ya kuma buƙaci duk masu ruwa da tsaki da su lura da wannan umurni tare da tabbatar da cikakken bin sa, yana mai jaddada ƙudirin gwamnatin sa na ƙarfafa cibiyoyin dimokiraɗiyya da kuma inganta sahihancin zaɓuɓɓuka a Nijeriya.

Tags: murabussiyasatakaraTinubuzaben2027
Previous Post

Babban Hafsan Sojin Ƙasa (COAS) ya buƙaci sojojin Nijeriya su mutunta haƙƙin ɗan’adam da tsaron jama’a

Next Post

Tinubu ya sauka a London domin ziyarar aiki

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC
Siyasa

Sanata Barau ya haɗa malamai sama da 2,000 domin tallata Tinubu, Gwamna Abba da ’yan takarar APC

November 24, 2026
Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf
Siyasa

Kwankwaso ya tura ni wajen Tinubu bayan mun yi alƙawarin komawa APC, inji Abba Yusuf

November 23, 2026
Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa
Siyasa

Rikicin ADC: INEC ta bayyana dalilin da ya sa Mark da Aregbesola ke ci gaba da kasancewa a cikin bayanan ta, yayin da ɓangaren Nafiu Gombe ke nuna rashin amincewa

November 20, 2026
Next Post
Tinubu ya sauka a London domin ziyarar aiki

Tinubu ya sauka a London domin ziyarar aiki

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!