• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Friday, May 15, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

‘Ku mara wa Tinubu baya’ — Soludo ya roƙi Inyamirai kada su ɓata ƙuri’un su a 2027

ALI KANO by ALI KANO
March 17, 2026
in Siyasa
A A
0
‘Ku mara wa Tinubu baya’ — Soludo ya roƙi Inyamirai kada su ɓata ƙuri’un su a 2027
Farfesa Charles Soludo yana rantsuwar kama aiki a matsayin Gwamnan Jihar Anambra yau a garin Awka

Farfesa Charles Soludo yana rantsuwar kama aiki a matsayin Gwamnan Jihar Anambra yau a garin Awka

Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya buƙaci al’ummar yankin Kudu-maso-gabas da su mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a zaɓen gama-gari na 2027.

Soludo ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin rantsar da shi karo na biyu, wanda aka gudanar a dandalin Dakta Alex Ekwueme Square da ke Awka, babban birnin Jihar Anambra.

Alƙalin Alƙalan Jihar Anambra, Onochie Anyachebelu, shi ne ya rantsar da Soludo tare da karɓar rantsuwar aiki da ta biyayya da ƙarfe 11:47 na safe.

Haka kuma Anyachebelu ya rantsar da mataimakin gwamnan jihar, Onyekachukwu Ibezim, da ƙarfe 11:52 na safe.

Taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da tsofaffin shugabannin ƙasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.

Da yake jawabi ga mahalarta taron, Soludo ya ce bai kamata ‘yan yankin Kudu-maso-gabas su “ɓata” ƙuri’un su kan wasu ’yan takara ba a zaɓen na shugaban ƙasa da ke tafe, yana mai cewa ya dace su mara wa Tinubu baya.

Soludo ya nuna cewa makomar siyasar Inyamirai tana da matuƙar muhimmanci, amma ya nuna cewa lokacin da yankin zai fitar da shugaban ƙasa bai zo ba.

Gwamna Soludo tare da maiɗakin sa da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, da Mataimakin Shugaban Ƙasa Sanata Kashim Shettima a wurin bikin rantsarwar yau a Awka

Gwamnan ya ce yankin yana da ƙwarin gwiwa ga gwamnatin Tinubu, yana mai nuni da abin da ya bayyana a matsayin sauye-sauye masu kyau da ke shafar yankin Kudu-maso-gabas.

“Shugaba Tinubu mutum ne mai zurfin tunani, jarumi kuma mai kishin ƙasa. Muna da yaƙinin zai kawo gagarumin sauyi ga Nijeriya da yankin Kudu-maso-gabas,” inji shi.

Gwamnan ya kuma buƙaci abokan hamayyar sa na siyasa a Anambra da su ajiye bambance-bambancen su su haɗa kai domin cigaban jihar.

Ya ƙara da cewa duk da cewa fafatawar siyasa a jihar ta ƙare, ya kamata a mayar da hankali yanzu kan mulki nagari.

A nasa jawabin, Shettima ya yaba da jagorancin Soludo, yana mai bayyana shi a matsayin bawan jama’a wanda ke aiki bisa tunani da gaskiya.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya jaddada shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya na yin aiki tare da gwamnatin Jihar Anambra, yana mai cewa ya kamata mulki ya fi mai da hankali kan jin daɗin al’umma fiye da siyasar jam’iyya.

Shettima ya kuma buƙaci mazauna jihar da su mara wa ƙoƙarin gwamnati baya na mayar da Anambra cibiyar tattalin arziki da zuba jari a Nijeriya.

Tags: rantsarwaShettimaSoludoTinubuzaben2027
Previous Post

Tinubu ya sauka a London domin ziyarar aiki

Next Post

CAF ta ƙwace kofin zakarun AFCON na 2025 daga Senegal, ta bai wa Morokko

Related Posts

An kama Bello Boɗejo, shugaban Fulani Kuma ɗan takarar kujerar Sanata na APC a Taraba
Siyasa

An miƙa ɗan takarar Sanata kuma shugaban Fulani, Bello Boɗejo ga EFCC

May 10, 2026
Tinubu ya taya Garo murnar zama mataimakin gwamnan Kano
Siyasa

Tinubu ya taya Garo murnar zama mataimakin gwamnan Kano

May 5, 2026
Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Next Post
CAF ta ƙwace kofin zakarun AFCON na 2025 daga Senegal, ta bai wa Morokko

CAF ta ƙwace kofin zakarun AFCON na 2025 daga Senegal, ta bai wa Morokko

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!