Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya kafa sabon gidan rediyo mai suna Majority FM 89.5 domin yaƙin neman sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.
Gidan rediyon yana cikin ofishin ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors da ke Fatakwal, Jihar Ribas.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara ƙaimi wajen shirye-shiryen siyasa domin yaƙin neman sake zaɓen Shugaba Tinubu a shekarar 2027 a yankin Kudu-maso-kudu.
A cikin wani bidiyo da ke yawo a intanet, an ga Wike yana duba sabon gidan rediyon, yana zagaya cikin situdiyo tare da ganawa da ma’aikata.

Majiyoyi sun bayyana wa Leadership cewa an tsara tashar ne domin ta zama wata muhimmiyar kafar yaɗa saƙonni ga ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors, wadda aka fi sani da goyon bayan ta ga gwamnatin Tinubu.
“Wannan tashar za ta riƙa karɓar saƙonni daga dukkanin unguwanni 666 na Jihar Ribas. Mun shirya domin wannan aiki, mun shirya domin 2027,” inji Wike yayin ƙaddamar da tashar.
Jaridar ta ce masu sa ido kan harkokin siyasa sun ce kafa Majority FM na ƙara tabbatar da tasirin Wike a sabuwar tafiyar siyasar jihar gabanin babban zaɓen 2027.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Wike da ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan yadda za a tafiyar da tashar rediyon.








