• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Yadda Al-Barnawi ya sa na shiga Boko Haram — Wanda ake zargi

Shari'ar harin ginin Majalisar Ɗinkin Duniya

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
January 21, 2026
in Tsaro
A A
0
Yadda Al-Barnawi ya sa na shiga Boko Haram — Wanda ake zargi
Khalid Al-Barnawi, jagoran 'yan ta'adda

Khalid Al-Barnawi, jagoran 'yan ta'adda

Ɗaya daga cikin waɗanda Hukumar Tsaro ta Farar Hula (DSS) ta gurfanar tare da Khalid Al-Barnawi da wasu mutum uku bisa zargin hannu a harin bam na ranar 26 ga Agusta, 2011, da aka kai wa ginin Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) a Abuja, ya bayyana wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja yadda ya shiga ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram.

A zaman shari’ar da aka ci gaba da yi yau Laraba kan Al-Barnawi da wasu mutum huɗu, wanda ake tuhuma na biyu, Mohammed Bashir Saleh, a cikin wani bidiyon da aka kunna a gaban kotu, ya ce ya haɗu da Al-Barnawi ne a Bauchi jim kaɗan kafin harin ginin MDD ɗin, kuma daga wannan lokaci alaƙar da ke tsakanin su ta ƙarfafa har ta kai shi shiga Boko Haram.

Hukumar DSS ta kama Al-Barnawi ne a watan Afrilun 2016 a Lokoja, Jihar Kogi, shekaru biyar bayan harin bam ɗin da aka kai ginin MDD a Abuja — wanda shi ne harin farko irin sa da aka taɓa kai wa dukiyar wata hukumar ƙasa da ƙasa a Nijeriya — wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 20 tare da jikkata sama da 70.

Al-Barnawi, wanda kuma ake kira da sunaye daban-daban kamar Kafuri/Naziru/Alhaji Yahaya/Mallam Dauda/Alhaji Tanimu, DSS ta gurfanar da shi ne tare da Mohammed Bashir Saleh; Umar Mohammed Bello wanda aka fi sani da Datti; Mohammed Salisu; da Yakubu Nuhu wanda aka fi sani da Bello Maishayi.

A zaman shari’ar ranar Laraba, kotu ta kalli wani bidiyo na ƙarin zaman tambayoyi da aka yi da Saleh, sannan aka fara yi wa shaidar tuhuma ta uku tambayoyi a ci gaba da shari’a cikin shari’a (“trial-within-trial”) da ake gudanarwa domin tantance ko bayanan furucin da ake zargin waɗanda ake tuhuma sun bayar sun kasance na son rai ne ko akasin haka.

A yayin yi masa tambayoyi ta bakin lauyan wanda ake tuhuma na farko (Al-Barnawi), F.K. Kaigama, shaidar da aka bayyana da suna “TSR3” ta ce yana aiki a Sashen Fasaha na DSS, kuma daga cikin ayyukan sa akwai girka na’urorin ɗaukar sauti da bidiyo a ɗakin tambayoyi.

Shaidar ta ƙara da cewa yana ɗaukar sauti da bidiyo na waɗanda ake zargi a lokacin zaman tambayoyi.

Da aka tambaye shi sauran ayyukan sa, ya ce: “Baya ga waɗannan ayyuka, ina kuma gudanar da binciken na’urar kwamfuta (computer forensics), binciken wayoyin salula, binciken wurin aikata laifi kamar tattara hoton yatsu (fingerprints) daga wurin laifi da kuma nazarin su a ɗakin gwaje-gwaje.”

Shaidar ta ce ba wai kawai ya girka na’urar ɗaukar sauti da bidiyo ba dangane da wanda ake tuhuma na farko; ya ƙara da cewa shi ne ya ɗauki sauti da bidiyon zaman tambayoyin da aka yi wa wanda ake tuhuma na farko kai-tsaye yayin da suke faruwa.

Ya ce abu na uku da ya yi dangane da wanda ake tuhuma na farko shi ne ɗaukar sauti da bidiyon zaman karɓar bayani, da kuma ɗaukar sauti da bidiyon fassarar bayanan da wanda ake tuhuma na farko ya bayar.

Da aka tambaye shi ko akwai wani mutum mai suna James a Sashen Fasaha inda yake aiki, shaidar ta ce akwai James da dama a Sashen Fasaha na DSS.

A wannan mataki, Mai Shari’a Emeka Nwite ya bayar da umurnin ɗage ci gaba da shari’ar bisa dalilin cewa yana da wasu ayyuka a gaban sa.

Bisa amincewar lauyoyin ɓangarorin da ke shari’ar, Mai Shari’a Nwite ya ɗage shari’ar zuwa ranar 2 ga Maris domin ci gaba da yi wa shaidar tuhuma ta uku (PW3) tambayoyi a shari’ar “trial-within-trial”.

Tags: BokoHaramDSSKhalidAlBarnawiMaiShari'aEmekaNwiteMajalisarƊinkinDuniya
Previous Post

Ingantacciyar sadarwa muhimmin ginshiƙi ne na samun nasarar ƙidayar jama’a – Minista

Next Post

Abubakar Malami ya musanta zargin tallafa wa ta’addanci, ya yi tir da ‘shari’a a kafafen yaɗa labarai’

Related Posts

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma
Tsaro

Zargin juyin mulki: Sojoji sun ƙaddamar da Babbar Kotun Soja, sun fara shari’ar jami’an da ake tuhuma

April 25, 2026
Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos
Tsaro

Sojoji sun kama ɗan tasi da ɗimbin alburusai da kayayyakin haɗa bamabamai a hanyar Kaduna zuwa Jos

April 17, 2026
‘Yan sanda sun miƙa wani da ake zargi da kisan kai ga hukumomin Birtaniya
Tsaro

‘Yan sanda sun miƙa wani da ake zargi da kisan kai ga hukumomin Birtaniya

April 16, 2026
Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su
Tsaro

Sojoji sun ragargaji maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Bauchi, sun kamo iyalan su

April 15, 2026
Nijeriya ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba – Gwamnatin Tarayya
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta kare harin jirgin sama a Jilli, ta ba da umurnin bincike

April 14, 2026
An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno
Tsaro

An kashe kwamanda da sojoji shida ta hanyar bam a Borno

April 13, 2026
Next Post
Abubakar Malami ya musanta zargin tallafa wa ta’addanci, ya yi tir da ‘shari’a a kafafen yaɗa labarai’

Abubakar Malami ya musanta zargin tallafa wa ta’addanci, ya yi tir da 'shari’a a kafafen yaɗa labarai'

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!