• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Ingantacciyar sadarwa muhimmin ginshiƙi ne na samun nasarar ƙidayar jama’a – Minista

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
January 21, 2026
in Labarai
A A
0
Ingantacciyar sadarwa muhimmin ginshiƙi ne na samun nasarar ƙidayar jama’a – Minista
Daga hagu: Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, da Shugaban Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa (NPC), Dakta Aminu Yusuf, a lokacin ziyarar a yau Laraba

Daga hagu: Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, da Shugaban Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa (NPC), Dakta Aminu Yusuf, a lokacin ziyarar a yau Laraba

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na gudanar da ƙidayar jama’a ta ƙasa wadda za ta kasance mai sahihanci, gaskiya kuma mai karɓaɓɓiya a idon duniya, inda ya bayyana cewa ingantacciyar sadarwa da haɗin gwiwar hukumomi su ne ginshiƙan samun nasarar aikin.

Ministan ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Laraba, yayin da ya karɓi Shugaban Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa (NPC), Dakta Aminu Yusuf, wanda ya jagoranci tawagar shugabannin hukumar a wata ziyarar girmamawa da suka kai masa.

A cewar Idris, sahihan bayanai su ne tushen tsare-tsaren ƙasa, yana mai jaddada cewa ba tare da cikakkun bayanan yawan jama’a ba, ba za a iya tsara cigaba mai ma’ana da kuma tasiri ba.

Ya tabbatar wa da shugabannin NPC cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai da hukumomin ta—ciki har da Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), Gidan Talbijin na Ƙasa (NTA), Hukumar Rediyon Tarayya ta Nijeriya (FRCN), Muryar Nijeriya (VON) da Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN)—a shirye suke tsaf wajen wayar da kan ’yan Nijeriya da kuma jagorantar yaɗa saƙonni a faɗin ƙasar nan da zarar Shugaban Ƙasa ya ayyana ranar ƙidayar.

Ministan ya jaddada cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana da niyyar gudanar da ƙidayar da ’yan Nijeriya da al’ummar duniya za su yarda da ingancin ta, yana mai cewa gwamnatin na bai wa tsari, bin doka da sahihanci fifiko fiye da yin gaggawa.

Minista tare da jami’an NPC

Ya sake nanata cewa ayyanawar Shugaban Ƙasa ita ce tushen doka ta gudanar da ƙidayar jama’a, yana mai tabbatar da cewa Shugaba Tinubu yana daidaita dukkan abubuwan da ake buƙata yadda ya kamata domin aikin ya cika ƙa’idojin duniya.

Ministan ya yi kira ga NPC da ta ci gaba da amfani da kafafen yaɗa labarai na gwamnati wajen wayar da kan jama’a, yayin da ya ba da tabbacin cewa ma’aikatar sa za ta sauke nauyin da ke kan ta na tallata shirye-shirye da manufofin gwamnati bisa muradin ƙasa.

Tun da fari, sai da Shugaban Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa (NPC), Dakta Aminu Yusuf, ya yaba wa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai bisa goyon baya da jagoranci da take bayarwa a ƙoƙarin wayar da kan jama’a gabanin ƙidayar da aka ɗage.

Ya ce hukumar tana cikin shirin ko-ta-kwana, inda ake ci gaba da inganta tsare-tsare, kayan aiki, fasahar sadarwa (ICT) da ma’aikata domin tabbatar da inganci, gaskiya da sahihanci da zarar an bayyana sabuwar ranar ƙidayar.

Dakta Yusuf ya kuma buƙaci a ci gaba da ba su damar yin amfani da kafofin yaɗa labarai na gwamnati domin zurfafa fahimtar jama’a kan muhimmancin shiga ƙidayar, rajistar haihuwa da mutuwa, da muhimman ƙididdiga, yana mai bayyana cewa amincewar jama’a ita ce jigon nasarar tafiyar da al’amurran ƙididdiga a Nijeriya.

Tags: DaktaAminuYusufMohammedIdrisNPCWayarDaKaiziyaraƘidayarJama'a
Previous Post

Abin burgewa: Sarki Sanusi ya fara halartar lacca a matsayin ɗalibin jami’a a Kano

Next Post

Yadda Al-Barnawi ya sa na shiga Boko Haram — Wanda ake zargi

Related Posts

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya
Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi kira da a gudanar da watsa shirye-shirye cikin ɗa’a domin kare dimokiraɗiyya

September 29, 2026
Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
Next Post
Yadda Al-Barnawi ya sa na shiga Boko Haram — Wanda ake zargi

Yadda Al-Barnawi ya sa na shiga Boko Haram — Wanda ake zargi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!