Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa fiye da ‘yan mata masu tasowa 40,000 a faɗin jihar sun amfana da wani tsari na musamman na koyon dabarun rayuwa, yayin da Gwamna Uba Sani ke shirin tabbatar da koyar da dabarun rayuwa a matsayin tsari na dindindin a dukkan makarantun sakandare na gwamnati.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta fitar, ta ce gwamnan na shirin gabatar da Ƙudirin Dokar Zartarwa ga Majalisar Dokokin jihar domin sanya koyon dabarun rayuwa a matsayin darasi tilas kuma na dindindin cikin manhajar makarantun sakandare na jihar.
Ana aiwatar da shirin koyon dabarun rayuwar ne ƙarƙashin Shirin AGILE (Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment) da Bankin Duniya ke tallafawa. Zuwa yanzu, shirin ya kai ‘yan mata 40,536 da maza 1,864, tare da horas da malamai 1,141 a matsayin masu jagoranci (mentors) a manyan makarantun sakandare a jihar.
Kwamishinan Ilimi, Farfesa Abubakar Sani Sambo, shi ne ya bayyana hakan a wani taron bitar dabaru da aka gudanar a Abuja kan yadda za a tabbatar da koyar da dabarun rayuwa a tsarin ilimi.
Da yake magana a madadin Gwamna Uba Sani, ya ce gwamnatin jihar ta ƙudiri aniyar wucewa ilimi na karatu kawai zuwa gina basirar tunani, juriyar zuciya, ƙwarewar jagoranci da alhakin zamantakewa, musamman ga ‘ya’ya mata.
Ya bayyana cewa wannan gyara alama ce ta sauyawa daga tsarin ilimi na gargajiya mai mayar da hankali kan “tunani” zuwa tsarin ilimi mai faɗi wanda ke ƙunshe da “aiki da ji”, domin shirya ɗalibai yadda ya kamata don fuskantar ƙalubalen rayuwa ta zahiri.
Manhajar dabarun rayuwar ta ƙunshi darussa kan ƙarfafa gwiwa, lafiya da abinci mai gina jiki, lafiyar haihuwa, hana tashin hankalin da ya shafi jinsi, sauyin yanayi da shigar kowa cikin al’umma.
Ma’aikatar ta ce sakamakon farko da aka samu ya haɗa da ƙaruwar ƙwarin gwiwar ɗalibai, raguwar yawan ƙin zuwa makaranta, ƙaruwar rajista, da sauye-sauyen ɗabi’a masu kyau, ciki har da ƙaruwar mutunta juna da tausayin juna a tsakanin ɗalibai.
Mai Kula da Shirin AGILE a Jihar Kaduna, Hajiya Maryam Sani Ɗangaji, ta tabbatar da cewa an aiwatar da shirin a dukkan manyan makarantun sakandare ba jihar.
Haka kuma, Daraktar Zartarwa ta Cibiyar Ilimin ‘Ya’ya Mata, Dakta Habiba Mohammed, ta bayyana tsarin Kaduna a matsayin abin koyi ga gyaran ilimi mai ɗorewa da ya mayar da hankali kan ‘ya mace.
Dangane da ƙudirin dokar da ake shirin gabatarwa, Shugaban Kwamitin Ilimi na Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Hon. Emmanuel Bako Kantiok, ya tabbatar da cewa a shirye majalisar take ta hanzarta amincewa da ƙudirin da zarar an kammala tattaunawa da masu ruwa da tsaki.
A cewar Ma’aikatar Yaɗa Labarai, dokar da ake shirin yi za ta kafa ingantaccen tsarin doka da kasafin kuɗi na musamman, domin tabbatar da cewa koyar da dabarun rayuwa—musamman ga ‘ya mace—zai ci gaba da kasancewa wani muhimmin ɓangare kuma tilas a tsarin ilimin gwamnati na Jihar Kaduna har zuwa shekaru da dama masu zuwa.







