Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) sun ƙulla wata babbar yarjejeniya da nufin inganta jin daɗin malamai, tabbatar da zaman lafiyar aiki da kuma kawo ƙarshen yawan yajin aikin da ya shafe shekaru yana durƙusar da jami’o’in ƙasar nan.
An bayyana yarjejeniyar ta shekarar 2025 tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU a ranar Laraba a Abuja, inda Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya bayyana ta a matsayin wani sabon shafi a tarihin ilimin gaba da sakandare a Nijeriya.
A cewar sa, yarjejeniyar ba rubutun takarda ba ne kawai, illa alamar dawo da amana, girmamawa da ƙwarin gwiwa ga tsarin jami’o’in ƙasar nan bayan shekaru na rashin tabbas da yajin aiki.
Ministan ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa ɗaukar mataki na musamman wajen fuskantar matsalar da ta daɗe tana addabar jami’o’i, tana lalata jadawalin karatu tare da rusa makomar miliyoyin ɗalibai.
“Wannan ne karon farko da Shugaban Ƙasa mai ci ya tsaya tsayin daka wajen fuskantar wannan ƙalubale kai-tsaye, ya ba matsalar kulawar shugabancin da ta dace,” inji Alausa.
Ya ce gwamnatin ta zaɓi tattaunawa maimakon rikici, gyara maimakon jinkiri, da warware matsala maimakon surutu.
Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa shi ne ƙarin albashin malaman jami’a da kashi 40 cikin 100, wanda Hukumar Albashi, Kuɗaɗen Shiga da Albashi ta Ƙasa (NSIWC) ta amince da shi.
Sabon tsarin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026.
A ƙarƙashin sabon tsarin, albashin malamai zai haɗa da CONUASS da kuma ingantaccen alawus na kayan aikin koyarwa da bincike (CATA).
An ƙarfafa CATA domin tallafa wa wallafa mujallu, halartar tarurruka, amfani da intanet, rajistar ƙungiyoyin ƙwararru da rubuce-rubucen littattafai, domin ƙara gogayya da rage guduwar ƙwararru zuwa ƙasashen waje.

Haka kuma yarjejeniyar ta sake tsara alawus-alawus guda tara na Earned Academic Allowances, inda aka fayyace su sarai tare da danganta su kai-tsaye da ayyukan da ake yi kamar kula da ɗaliban digirin digirgir, aikin asibiti, jarrabawa da shugabancin harkokin ilimi.
A wani sabon salo da ba a taɓa gani ba a tsarin jami’o’in Nijeriya, Gwamnatin Tarayya ta amince da wani alawus na musamman ga manyan malaman jami’a, wato Farfesoshi da Ƙananan Farfesoshi (Readers).
A ƙarƙashin wannan tsari, Farfesoshi za su riƙa karɓar naira miliyan 1.74 a shekara (naira 140,000 a wata), yayin da Readers za su karɓi naira 840,000 a shekara (naira 70,000 a wata).
Ministan ya ce an samar da wannan alawus ne domin ƙarfafa bincike, tsara takardu da inganta gudanarwa, ta yadda manyan malamai za su fi mayar da hankali kan koyarwa, renon matasa da ƙirƙire-ƙirƙire.
Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin Shugaba Tinubu za ta aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata a ƙarƙashin Shirin Sabunta Fata, tare da ci gaba da tattaunawa da gyare-gyare a fannin ilimi.
Masu ruwa da tsaki na ganin yarjejeniyar za ta kawo sabon zamani na kwanciyar hankali da inganci a jami’o’i, tare da dawo da daidaito a jadawalin karatu da kuma sabunta fata ga ɗalibai da iyaye.
Ministan ya yaba wa tawagogin tattaunawar ɓangarori biyu, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Yayale Ahmed daga ɓangaren Gwamnatin Tarayya da Farfesa Pius Piwuna daga ASUU, tare da tsohon shugabancin ASUU na Farfesa Emmanuel Osodeke, bisa rawar da suka taka wajen samar da wannan nasara.
A ƙarshe, Alausa ya ce tarihi ba zai tuna wannan rana a matsayin ranar ƙaddamar da yarjejeniya kawai ba, har ma ranar da Nijeriya ta zaɓi tattaunawa, gaskiya da jajircewar shugabanci a matsayin hanyar warware matsalolin da suka daɗe suna addabar ƙasa.
Da yarjejeniyar ta kammala, al’ummar Nijeriya na fatan cewa zamanin rufe jami’o’i na dogon lokaci zai zama tarihi, yayin da ake sa ran samun kwanciyar hankali, ƙwarewa da gogayya da jami’o’in duniya a fannin ilimi.







