Cikin 2024, wani matashi ya yi wa wani kwatancen hanyoyi da garuruwan da zai keta domin shiga ‘uwa-duniya’ daga Kano zuwa Algiers, babban birnin ƙasar Aljeriya da ke Afrika ta Arewa. Kwatancen wanda ya yi masa a shafin Tiktok ya ɗauki hankalin mutane da dama, aka riƙa mamakin irin yadda dubban matasan Arewa ke tafiyar kasada da saida rai, domin fita zuwa wasu ƙasashe da niyyar “neman kuɗi.”
Bari ku ga wannan kwatance mai dogon zango: “To maigida kana cewa za ka je Alje. To ni ba zan maka kamasho ba. Amma ga hanya: Idan kana Kano, ka tafi Tashar Kuka (Ƙofar Ruwa). Daga Tashar Kuka za ka je Daura. Daga Daura za ka je Kwangwalam. Daga Kwangwalam za ka shiga Maimujiya. Daga Maimujiya za ka je Ɗanbarto. Daga Ɗanbarto za ka je Matamai.
“Daga Matamai za ka ce Kanche. Daga Kanche za ka shiga Damagaram. Daga Damagaram za ka shiga Baƙin Burji. Daga Baƙin Burji za ka shiga Majiya. Daga Majiya za ka shiga Tarnet. Daga Tarnet za ka je Takoukou. Daga Takoukou za ka je Adarbishou. Daga Adarbishou za ka je Agadez. Daga Agadez za ka je Gidan Daka. Daga Gidan Daka za ka je Arle. Daga Arle za je Asamakar. Daga Asamakar za ka je Din. Daga Din za ka je Ingizam. Daga Ingizam za ka je Tamarasin. Daga Tamarasin za ka je El-Mingel.
“Daga El-Mingel za ka je Moulayesen. Daga Moulayesen za ka je Insalaa. Daga Insalaa za ka je Al-munayya. Daga Al-munayya za ka je Wurgila. Daga Wurgila za ka tafi Taburtu.
“Daga Taburtu za ka tafi Magayyar. Daga Magayyar sai Buskina. Daga Buskina za ka tafi Batana. Daga Batana za ka tafi Al-manila. Daga Al-manila za ka tafi Kwastantina. Daga Kwastantina za ka je Stiff. Daga Stiff sannan ka je Alje. Sannan aikin da ka ga dama sai ka yi. Wannan ita ce shawarar da zan baka.”

Daga lokacin da wannan matashi ya bayar da wannan shawara a Tiktok, Allah kaɗai ya san adadin matasan da suka nausa zuwa Aljeriya daga Arewacin Nijeriya. Wasu dubban kuma Libya suke tururuwar shiga. Tafiya ce ake yi kusan kashi 70 cikin 100 duk a Sahara. Daga Kano zuwa birnin Alje dai ƙididdiga ta nuna tafiyar kilomita 3462 ce a mota. Wato kwatankwacin ka tashi daga Kano ka je Abuja sannan ka dawo har sau huɗu sannan ka koma Kaduna.
Dubban matasan Arewa na cikin Aljeriya a birane da ƙananan garuruwan da ba su kai Bichi, Bakori, Kankiya, Gumel ko Daura ba. Yawancin su duk aikin ƙarfi suke yi, mai kama da bauta, wanda a nan Nijeriya su ke ƙyamar yi, domin a ganin su ƙasƙanci ne. Kuma ba ka da wani zaɓi, tilas ka yi aikin, domin ba ka da kusan naira 600,000 ɗin da za ta maida ka gida.
Babban tashin hankalin shi ne yadda dandazon ‘yan mata har da zawarawa da ɗaiɗaikun matan aure duk ba a bar su ba. Sai tururuwar zuwa Libya da Algeriya ake yi. Lamarin ya ƙara muni bayan cire tallafin fetur, yayin da aka shiga halin ƙuncin rayuwa a farkon hawa mulkin Shugaba Bola Tinubu. Daga a baya tsadar rayuwa da matsalar tsaro ce suka haifar da ficewar matasan Arewa zuwa Libya da Aljeriya a zamanin mulkin marigayi Muhammadu Buhari. Koda yake akwai da yawa waɗanda suka raina ƙananan sana’o’in da suke yi a Arewa, suka bi romon-kunne da romon-bakan labaran samun kuɗin da ake cewa ana yi a can.

Irin wahalar da matasan Arewa ke sha a hannun Larabawa a garuruwan Aljeriya, ba ta da bambanci da irin wadda masu zuwa Libya ke sha. Da mai gadi ko ɗan aikin gida da wanda ake kaiwa gona ya yi aiki, duk kusan wahalar su ɗaya. “Ni dai ban taɓa ganin maƙetacin mutum kamar Balarabe ba. Idan kana yi masa aiki ya tsani ya ga kana zaune kana hutawa. Idan babu wani aiki, ya ga damar ya ce ka fito da buhunan siminti da ke a cikin sito duka. Bayan ka gama kuma ya ce ka sake mayar da su. Shi dai ba ya so ka huta, domin wai duk wata zai biya ka albashi.” Inji wani matashi mai suna Sa’idu da ya ɗanɗana abin da kira azaba a hannun wani Balarabe.
Shiga Libya Cikin Buhun Ƙaya
“Ina tabbatar maka masu tafiya Aljeriya ba su kai masu shiga Libya shan wahala ba. Mu dai daga Kano motar zuwa Daura muka hau. Daga Daura muka shiga Nijar. To daga can aka loda mu cikin wata buɗaɗɗar mota aka haɗa mu da lodin jogon kaji masu yawan gaske.” Cewar wani matashin da ya ce na sakaya sunan sa, a lokacin da na yi hira da shi ta wayar tarho daga Libya.
“Za ku yi kwanaki kuna lafiya cikin sahara, kowa da guzirin ruwan sha a jarka. Idan aka zo shiga Libya, za ku kwanta ƙasa cikin Hilux, sai a lulluɓe ku da barguna. Daga nan sai a yi ta loda damman ƙaya a kan ku, don kada jami’an tsaron su su gane an ɗauko baƙi daga waje.
“To wanda zai shiga Libya da dare zai shiga, an lulluɓe shi. Kuma wallahi ko za a wuce gari goma, kai dai ba za ka ga ko gari ɗaya ba. Sai an je garin da za a sauke ku sannan a fito da ku. Ni ɗin nan ga shi na kai shekara ɗaya da rabi a Libya, amma garin da nake kaɗai na taɓa gani,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa matasa da dama suna mutuwa a cikin Sahara, saboda tsakanin wahala. Kuma idan ana gudu cikin Sahara, idan fasinja ya faɗo ƙasa, diraba ba shi tsayawa a ɗauke shi. “Na san dai ka san Abdulhadi. To shi ma muna nan tare da shi. Kuma da ya zo ya ce min mutum huɗu ya mutu a cikin motar su a Sahara. Sai dai su tone yashin Sahara su binne gawa bayan sun yi mata Sallah, su ƙara gaba. Ni dai Allah ya taimake ni, kanikanci nake yi a nan Libya.
Wani abin ɗaure kai shi ne, ana tururuwar zuwa Libya da Aljeriya ne daga Arewa da kuma Nijar, saboda su kuma matasan su duk sun gudu zuwa Turai, musamman Spain da Faransa. Dalili kenan za ka ga matasan Arewa da ke Aljeriya masu shafukan Tiktok na nuno garuruwan da suke ciki fayau babu matasan ƙasar. A Kano, musamman a unguwanni irin su Rijiyar Lemo da wasu da dama, zuwa Libya da Aljeriya ya ma zama kamar gasa.

Ba Libya da Aljeriya kaɗai matasan Arewa ke ta kwarara ba. Dubbai na yin tafiyar ci-ranin gajeren zango zuwa Benuwai, Taraba, Legas, Edo kai har Bayelsa. Masu tafiya Benuwai da Taraba dai akasari noma suke yi. Masu nausawa Legas har Bayelsa da wasu garuruwan kudu maso gabas kuwa hayar okada suke yi. Haka kuma garuruwan Jihar Neja irin su Suleja, Tafa, Zuba da sauran su, cike suke danƙam da matasan Arewa ‘yan ci-rani, kamar yadda wasu dubbai ke cikin garuruwan Jihar Nasarawa, musamman Nyanya, Maraba da Karu. Shi ma gundumar FCT Abuja garuruwan kewaye da birnin tarayya cike suke da matasan Arewa, musamman Dutsen Alhaji, Deidei, Gwarimpa, Lugbe, Karmo, Mpape, Gwagwalada, Kuje da duk wani gari ko ƙauyen da ke kusa ko nesa da Abuja.
Yadda Ake Mutuwa A Hanya Saboda ‘Mutuwar’ Son Shiga Spain
Dandazon Hausawa daga jihohin arewa da kuma wasu ‘yan asalin Jamhuriyar Nijar, a kullum suna ƙoƙarin shiga ƙasashen Turai, musamman ta ƙasa kafin daga nan su dangana bakin ruwa, su tsallaka, ko kuma mai ƙarar kwana ya tsallaka zuwa lahira.
Yawancin masu ƙoƙari ko hanƙoron shiga ƙasashen Turai, suna tsallakawa ne cikin Morocco daga Aljeriya, daga nan za su keta Sahara, wata tafiya mai cike da hatsarin gaske, kafin su dangana bakin ruwa su samu kwale-kwale su haye. Waɗannan matasa na nuno irin tafiyar da suke yi a Sahara ko a surƙuƙin daji, duk a shafukan su na Tiktok.
Sukan kuma nuno hotunan bidiyon gawarwakin da suka ci karo da su a cikin Sahara. Suna nuno hotunan ƙwarangwal na kanun matafiyan da suka daɗe da mutuwa, ko sangalen ƙashin ƙauri ko kutolon ƙashin kwankwaso. Haka kuma suna nuno gawarwakin matafiyan da ba su daɗe da mutuwa ba, waɗanda duk ga su nan kwance cikin yashin Sahara, tufafin su ma ba su kai ga lalacewa ba.
A haka ake samun masu sauran tsawon rai a gaba ke danganawa bakin ruwa, su shiga kwale-kwale. Mai rabon ganin baɗi ya kai gaci. Wanda kwanan sa ya ƙare kuwa, ya mutu a ruwa. Wanda ya tsallake kuma yana sauka, zai afka sabuwar wahalar yadda zai kurɗa cikin dokar-dajin ƙasashen Turai, har ya shiga malaɓa.






