• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, May 14, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shirin ƙarfafa noma: Gwamnan CBN ya ƙaddamar da Kwamitin Asusun Bada Bashi ga Manoma

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
December 14, 2025
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Shirin ƙarfafa noma: Gwamnan CBN ya ƙaddamar da Kwamitin Asusun Bada Bashi ga Manoma
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, yana jawabi a wurin ƙaddamar da Kwamitin Asusun Bada Bashin Bunƙasa Harkokin Noma ga ƙananan manoma (ACGSF)

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, yana jawabi a wurin ƙaddamar da Kwamitin Asusun Bada Bashin Bunƙasa Harkokin Noma ga ƙananan manoma (ACGSF)

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya ƙaddamar da membobin Kwamitin Asusun Bada Bashin Bunƙasa Harkokin Noma ga ƙananan manoma (ACGSF).

Da yake ƙaddamar da kwamitin a ranar Laraba a hedikwatar CBN a Abuja, Cardoso ya tabbatar da ƙudirin bankin wajen ƙara inganta harkokin noma a Nijeriya.

Ya jaddada muhimmancin aikin asusun tun daga shekarar 1977, wajen rage haɗarin da ke tattare da bayar da rancen kuɗaɗen noma.

Ya yi kira da a rungumi sabbin dabarun ƙirƙira na zamani, waɗanda suka haɗa da amfani da fasaha da kuma hanyoyin da za su haɗa mata da matasa a cikin tsarin tallafin manoma.

Daga hagu: Mista Olayemi Cardoso tare da shugaban kwamitin na ACGSF, Dakta Olusegun Oshin

Ya ce wannan asusu ya ci gaba da nuna tasiri mai ƙarfi tare da kaso na biyan bashi da ya kai tsakanin kashi 90 zuwa 98 bisa 100.

Sabon kwamitin, wanda ke ƙarƙashin shugabancin Dakta Olusegun Oshin, zai ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa, sa-ido sai kuma bin-diddigi da bibiyar ayyuka a zahiri, domin ƙarfafa samar da kayayyakin noma da inganta rayuwar al’ummun karkara.

Sabon kwamitin na ACGSF da aka ƙaddamar ɗin ya ƙunshi Dakta Olusegun Oshin a matsayin Shugaba, sai membobi da suka haɗa da: Farfesa Murtala Sabo Sagagi, Dakta Nneka Onyeali-Ikpe, Injiniya Frank Satumari Kudla, Olusola Sowemimo, Adetoun Abbi-Olaniyan, sai Mista Wondi da kuma Philip Ndanusa.

Sauran waɗanda suka halarci taron ƙaddamarwar sun haɗa da Mataimakan Gwamnan Bankin, Daraktoci na Sassa da sauran ma’aikata.

Membobin kwamitin

Yayin ƙaddamarwar, CBN ya ce wannan gagarumin shirin Bayar da Bashin Bunƙasa Harkokin Noma, yana da tasiri sosai, shi ya sa na aka naɗa masa waɗannan membobi na Kwamitin Asusun Sa-ido kan Shirin Bada Bashi ga Manoma.

Wannan shiri dai zai fi bada fifiko ne wajen ƙarfafa ƙananan manoma, domin ƙasa wadata ƙasa da abinci.

Da yake ƙaddamar da kwamitin, Cardoso, ya ce wannan shiri yana daga cikin tsare-tsaren da Gwamnatin Tarayya ta sa gaba, domin ɗora harkokin noma kan turbar ciyar da ƙasa da ‘yan ƙasa gaba, bunƙasa yankunan karkara da kuma faɗaɗa hanyoyin inganta tattalin arziki.

Tags: CBNkwamitimanomaOlayemi Cardoso
Previous Post

Ba gudu ba ja da baya kan zanga-zangar gama-gari kan matsalar tsaro – NLC

Next Post

Bankwana da 2025: Kamfanin BUA ya yi wa ma’aikata 510 watandar naira biliyan 30

Related Posts

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai

May 12, 2026
Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lamiɗo Yuguda, sabon Mataimakin Gwamnan CBN ya shiga ofis

May 12, 2026
Yadda tsare-tsaren CBN ke daƙile hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙwaƙudumar kasa biyan tulin bashin da manyan bankuna suka bayar laifin daraktoci da manyan masu hannayen jarin su ne, ba laifin CBN ba

May 8, 2026
Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tsauraran matakai da ƙa’idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya

May 7, 2026
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda ƙarfin laƙani da dafa’in CBN ke hana girgizar tattalin arzikin duniya yi wa Nijeriya barazana

May 6, 2026
Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris

May 5, 2026
Next Post
Bankwana da 2025: Kamfanin BUA ya yi wa ma’aikata 510 watandar naira biliyan 30

Bankwana da 2025: Kamfanin BUA ya yi wa ma’aikata 510 watandar naira biliyan 30

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!