Cole Palmer ya dawo da ƙwallo mai matuƙar muhimmanci yayin da Chelsea ta doke Everton da ci 2-0 a gasar Firimiya League a yau Asabar, inda hakan ya kawo ƙarshen jerin wasanni huɗu da ba su yi nasara ba a dukkan gasa.
Wannan nasarar da aka samu a dandalin Stamford Bridge ta ɗaga Chelsea ta koma cikin manyan ƙungiyoyi huɗu na kan gaba.
Ɗan wasan tsakiya mai kai hari Cole, wanda rauni ya dame shi, ya rasa wasan da Chelsea ta sha kashi a hannun Atalanta a gasar Champions League ranar Talata, yayin da yake murmurewa daga watanni biyu da ya yi a gefen fili.
Da farko Palmer ya samu matsalar raunin da samu a gaban sa, daga bisani kuma ya karya yatsan ƙafar sa lokacin da ya yi tuntuɓe da ƙofa a gidan sa.
Ɗan wasan mai shekaru 23 ya fara wasa a karon farko ne a ƙungiyar Blues tun watan Satumba a wasan da suka tashi 0-0 da Bournemouth a ƙarshen makon jiya.
Ɗan wasan na ƙasar Ingila ya karya shingen tsaro a wasan da Everton a minti na 21 a Stamford Bridge.
Malo Gusto ya ba Palmer kyakkyawar bugawa, inda Palmer ya doke ɗan wasan Ingila Jordan Pickford a kusa da mai tsaron gida.
Everton ta mamaye wasan, inda mai tsaron ragar Chelsea, Robert Sanchez, ya kama ƙwallo mai kyau da Jack Grealish ya harbo.
Duk matsin lambar da Everton ta yi bai ba su damar zura ƙwallon ramuwa ba, sannan Chelsea—duk da yadda wasan ke tafiya—ta ƙara ci na biyu a lokacin ƙarin lokaci na rabin farko, bayan wani zazzafan farmaki da ya ƙare da Gusto ya zura daga ƙwallon da Pedro Neto ya mayar daga gefe.
Everton ta samu damar rage ci zuwa 2-1 lokacin da Carlos Alcaraz ya lanƙwaso ƙwallo, amma Grealish da ba a kula da shi ba ya karkatar da ƙwallon ta wuce nesa.
Chelsea ta kusa ƙara ci na uku lokacin da bugun tazara na gaggawa daga Reece James ya kusa faɗawa raga amma Pickford ya ture ta sama da sandar raga.
Everton ta kusa samun damar farfaɗowa lokacin da Iliman Ndiaye ya kutsa cikin sashen bugun fanarati, to amma harbin nasa ya bugi cikin sandar raga ya dawo.







