• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu ya amince da kafa Kwamitin Aiki na haɗin gwiwar Amurka da Nijeriya

New Citizen Hausa by New Citizen Hausa
November 28, 2025
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tinubu ta musanta iƙirarin Shugaban Amurka wai ana tauye haƙƙin Kiristoci da karkashe su a Nijeriya
Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa ɓangaren Nijeriya na Kwamitin Aiki na Haɗin Gwiwar Amurka da Nijeriya, a matsayin wani mataki na zurfafa haɗin kai wajen magance matsalolin tsaro a ƙasar nan.

Wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Mista Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, ta ce tsarin kwamitin aiki na haɗin gwiwar yana daga cikin yarjejeniyar da aka cimma yayin ziyarar da wata tawaga ta manyan jami’an gwamnati daga Nijeriya, ƙarƙashin jagorancin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, suka kai Washington, DC, kwanan nan.

Ribadu zai jagoranci ɓangaren Nijeriya na kwamitin aikin, tare da goyon bayan tawagar manyan jami’ai daga hukumomi daban-daban da abin ya shafa.

Membobin kwamitin sun haɗa da Ministan Harkokin Waje, Jakada Yusuf Maitama Tuggar; Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar; Ministan Cikin Gida, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo; Ministan Harkokin Jinƙai, Dr Bernard M. Doro; Shugaban Ma’aikatan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Darakta-Janar na Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NIA), Jakada Mohammed Mohammed; da Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Mista Kayode Egbetokun.

Miss Idayat Hassan daga Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA) da Mista Paul Alabi daga Ofishin Jakadancin Nijeriya a Amurka za su yi aiki a matsayin sakatariya.

Tinubu ya shawarci membobin kwamitin da su yi aiki tuƙuru tare da takwarorin su na Amurka don tabbatar da ingantacciyar aiwatar da duk yarjejeniyoyi a fannoni daban-daban.

Tags: Amurkahaɗin gwiwakwamitiRibaduTinubutsaro
Previous Post

El-Rufai ya yanki katin shiga jam’iyyar ADC

Next Post

Tawagar Tinubu ta tafi Bauchi don halartar jana’izar Sheikh Ɗahiru Bauchi

Related Posts

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista
Siyasa

Shugaban NDC, Dickson ya yi wa Umar Arɗo raddi kan barazanar kai su kotu kan batun rajista

May 5, 2026
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya
Labarai

Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Nijeriya na neman a haɗa gwiwa a yaƙi masu yaɗa labaran ƙarya

May 4, 2026
Kwankwaso da Obi sun koma NDC
Siyasa

Kwankwaso da Obi sun koma NDC

May 3, 2026
Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi
Siyasa

Dalili na na ficewa daga ADC – Peter Obi

May 3, 2026
Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja
Labarai

Shettima ya ƙaddamar da jigilar maniyyatan Hajjin bana da kwashe alhazai 500 a Abuja

May 3, 2026
Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC
Siyasa

Binani ta fice daga ADC ta koma NDC watanni tara bayan barin APC

May 1, 2026
Next Post
Tawagar Tinubu ta tafi Bauchi don halartar jana’izar Sheikh Ɗahiru Bauchi

Tawagar Tinubu ta tafi Bauchi don halartar jana'izar Sheikh Ɗahiru Bauchi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!