Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya shiga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a hukumance, watanni bayan ya bada sanarwar ficewar sa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
El-Rufai ya kammala rajistar sa tare da karɓar katin zama memba a ofishin ADC da ke Unguwar Sarkin Musulmi, Kaduna.
Shigar sa ADC yana nuna babban mataki a sabon shirin siyasar da yake yi, bayan murabus ɗin sa daga APC a ranar 10 ga Maris.
A wasiƙar murabus ɗin sa a lokacin, tsohon Ministan na Babban Birnin Tarayya ya ce ba zai iya ci gaba da zama cikin jam’iyyar da ya yi imanin ta kauce daga manufofin da aka kafa ta a kai ba.
El-Rufai ya zargi shugabannin APC da barin manufofin da aka kafa jam’iyyar a kai, yana gargaɗin cewa jam’iyyar ta zama mai watsi da matsalolin cikin gida, kuma ba ta wakiltar al’amurran sauyi da ta riƙa shelar karewa ba.
A cewar sa, tsawon shekaru biyu yana ta jan hankalin jam’iyyar — a fili da kuma a bayan fage — kan abin da ya bayyana a matsayin hanyar da jam’iyyar ke bi mai tayar da hankali, amma ana ta watsi da ƙorafin sa.
El-Rufai, wanda ya taka muhimmiyar rawa a haɗewar jam’iyyun adawa a 2013 da ya haifi APC, ya ce jam’iyyar ta rabu da hangen nesa na farko da aka kafa ta a kai.
Ya lura da cewa abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan sun nuna ƙarancin niyyar shugabannin jam’iyyar wajen gane ko magance abin da ya kira yanayin cikin gida “mai rashin lafiya”.
Shigar sa a hukumance cikin ADC na nuna sabon babin siyasar sa, wanda ke ƙara ƙarfin jam’iyyar a Jihar Kaduna da ma ƙasa baki ɗaya yayin da ake ci gaba da samun sabon daidaitawar siyasa kafin zaɓukan gaba.







