• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, May 5, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Kiwon Lafiya

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin gaggawa na kula da lafiyar jarirai a Kano

Wakilin Mu by Wakilin Mu
September 18, 2025
in Kiwon Lafiya
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin gaggawa na kula da lafiyar jarirai a Kano
Uwa da ɗa (Hoto: UNICEF/Frank Dejongh)

Uwa da ɗa (Hoto: UNICEF/Frank Dejongh)

Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIA) ta ƙaddamar da wani sabon shiri na gaggawa domin rage mace-macen jarirai da ƙara samun damar kula da lafiyar su a asibitocin gwamnati a faɗin ƙasar nan.

An ƙaddamar da wannan shirin ne a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke jihar Kano, inda shugaban NHIA, Dakta Kelechi Ohiri, ta ce shirin zai mayar da hankali kan jarirai da ke fuskantar matsalolin gaggawa bayan haihuwa.

Ohiri, wanda Dakta Salawudeen Sikiru ya wakilta, ya bayyana cewa shirin ya samo asali daga wani tsari na kulawa da lafiyar iyaye mata da aka fara fiye da shekara guda da ta gabata.

“Mun fara wannan shiri ne don rage mace-macen iyaye mata da jarirai. Matakin farko ya shafi uwa, yanzu kuma mun ƙaddamar da ɓangaren jarirai domin magance matsalolin gaggawa bayan haihuwa,” inji shi.

Ya ce yanzu haka NHIA tana ɗaukar nauyin kuɗin magani ga jarirai a asibitocin gwamnati, inda asibitoci ke karɓar kuɗaɗen da suka kashe a kowane mako bayan an tabbatar da bayanan jinya.

Ya ce: “Ayyukan da shirin ya ƙunsa sun haɗa da kula da jariran da aka haifa ba su gama girma ba, matsalolin rashin numfashi bayan haihuwa, rawayar ido da fata (jaundice), cutar jini (sepsis) da matsalolin tiyata ga jarirai.”

Ya ƙara da cewa shirin ba zai tsaya kawai kan kulawar gaggawa ba, domin bayan an ceto jaririn za a yi masa rajista a kan inshorar lafiya ta ƙasa domin ya ci gaba da samun kulawa.

Shirin zai shafi iyalai marasa galihu ne kawai, tare da buƙatar lambar NIN domin tabbatar da sahihancin rajista.

A cewar sa, wannan matakin na farko zai gudana har zuwa shekarar 2027, tare da burin ganin kowane jariri mai buƙata ya samu kulawa a asibitocin da suka shiga cikin shirin.

Shugaban Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Farfesa Abdulrahman Sheshe, ya yaba wa Gwamnatin Tarayya da NHIA bisa wannan mataki, yana mai cewa zai taimaka wajen rage mace-macen jarirai da kuma ƙara inganta ayyukan lafiya a manyan asibitoci.

Ya yi kira ga gwamnati da ta ci gaba da ɗaukar nauyin irin waɗannan shirye-shirye na dogon lokaci, yana mai cewa su ne ginshiƙin tabbatar da tsarin kiwon lafiya da ya dace da buƙatun ’yan ƙasa.

Tags: AKTHFarfesa Abdulrahman SheshejariraiKelechi OhiriNHIA
Previous Post

Mun gaji da wulaƙanci a Kwankwasiyya, inji wasu matasan Ɗanbatta da suka canza sheƙa zuwa inuwar Sanata Barau Jibrin

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta yi jimamin rasuwar mutane a gobarar Benen Afriland a Legas

Related Posts

Tinubu ya naɗa Fatima Zuntu shugabar hukumar NBMA
Kiwon Lafiya

Tinubu ya naɗa Fatima Zuntu shugabar hukumar NBMA

April 20, 2026
Likitoci za su fara yajin aiki na gama-gari daga Talata
Kiwon Lafiya

Likitoci za su fara yajin aiki na gama-gari daga Talata

April 5, 2026
Uwargidan Shugaban Ƙasa ta ƙaddamar da Asusun Ciyarwar Abinci na Ƙasa, ta ba da gudunmawar naira miliyan 500
Kiwon Lafiya

Uwargidan Shugaban Ƙasa ta ƙaddamar da Asusun Ciyarwar Abinci na Ƙasa, ta ba da gudunmawar naira miliyan 500

April 3, 2026
Ranar Ji ta Duniya 2026: Dalilan da za a iya kauce wa suna ci gaba da haddasa naƙasar ji a tsakanin yara a Nijeriya – Minista
Kiwon Lafiya

Ranar Ji ta Duniya 2026: Dalilan da za a iya kauce wa suna ci gaba da haddasa naƙasar ji a tsakanin yara a Nijeriya – Minista

March 3, 2026
Nijeriya ta rattaba hannu kan babbar yarjejeniyar zuba jari a fannin kiwon lafiya
Kiwon Lafiya

Nijeriya ta rattaba hannu kan babbar yarjejeniyar zuba jari a fannin kiwon lafiya

February 5, 2026
Amurka za ta kashe dala miliyan 200 na tallafi kai-tsaye ga fiye da asibitoci 900 na mabiya addinin Kirista a Nijeriya
Kiwon Lafiya

Amurka za ta kashe dala miliyan 200 na tallafi kai-tsaye ga fiye da asibitoci 900 na mabiya addinin Kirista a Nijeriya

December 21, 2025
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta yi jimamin rasuwar mutane a gobarar Benen Afriland a Legas

Gwamnatin Tarayya ta yi jimamin rasuwar mutane a gobarar Benen Afriland a Legas

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!