Jam’iyyar APC a Jihar Katsina ta naɗa Arc. Ahmed Musa Ɗangiwa a matsayin Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu/Dikko na 2027, yayin da aka naɗa Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa a matsayin shugaban kwamitin.
An kafa kwamitin ne gabanin babban zaɓen shekarar 2027 domin daidaita harkokin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar, ƙarfafa tsarin tafiyar ta da kuma jagorantar wayar da kan al’umma da jawo masu kaɗa ƙuri’a a faɗin jihar.
An shirya ƙaddamar da kwamitin ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2026, da ƙarfe 11 na safe, a babban ɗakin taro na sabuwar sakatariyar APC ta jiha da ke kan Babban Titin Dutsin-ma, kusa da Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE), Katsina.
A tsarin shugabancin da jam’iyyar ta bayyana, Mataimakin Gwamna, Malam Faruk Lawal Jobe, zai zama mataimakin shugaban kwamitin na farko, yayin da Sanata Hadi Abubakar Sirika zai zama mataimakin shugaban na biyu, Dakta Mustapha Muhammad Inuwa kuma mataimakin shugaban na uku.
An naɗa Hon. Dakta Bashir Gambo Saulawa a matsayin mataimakin shugaban kwamitin, yayin da Hon. Abdulƙadir Mohammed Nasir zai zama Mataimakin Darakta-Janar mai kula da ayyuka, tare da taimakon Hajiya Sadiya Shehu Kafin Dangi.
Haka kuma, an naɗa Alhaji Bala Abu Musawa a matsayin Mataimakin Darakta-Janar mai kula da daidaita ayyuka, yayin da Hon. Adnan Nahabu zai kula da harkokin gudanarwa.
Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Alhaji Sani Aliyu Ahmed a matsayin sakataren tsare-tsare da shirya ayyuka, da Hon. Abdullahi Aliyu Turaji a matsayin babban sakataren kwamitin.
An kuma naɗa daraktocin shiyyoyi uku, inda Hon. Bature Umar Masari zai kula da Katsina ta Kudu, Rt. Hon. Ya’u Umar Gwajo-Gwajo zai kula da Katsina ta Arewa, yayin da Farfesa Badamasi Lawal Charanchi zai kula da Katsina ta Tsakiya.
Tsarin kwamitin ya ƙunshi manyan masu ba da goyon baya da suka haɗa da tsofaffin gwamnoni, ‘yan majalisun da ke kan mulki da waɗanda suka taɓa riƙe muƙaman majalisa, masu ruwa da tsaki a siyasa, tsofaffin masu riƙe da muƙaman gwamnati da sauran fitattun mutane a jihar.
Tsofaffin gwamnonin Katsina, wato Aminu Bello Masari da Ibrahim Shehu Shema, suna cikin waɗanda aka lissafa a matsayin manyan masu goyon bayan kwamitin, tare da sanatoci, tsofaffin mataimakan gwamnoni, tsofaffin ministoci da sauran jiga-jigan siyasa.
An kuma kafa kwamitin ba da shawara, wanda Alhaji Abdullahi Imam zai jagoranta, Alhaji Tanimu Yakubu Kurfi ya zama mataimakin shugaban, yayin da Barr. Murtala Aliyu Kankia zai zama sakatare.
Domin gudanar da ayyukan sa yadda ya kamata, kwamitin ya kafa sassa daban-daban da suka haɗa da gudanarwa, kuɗi, bincike da ƙididdiga, tsare-tsare da dabarun aiki, yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, harkokin shari’a, lafiya, tsaro da tattara bayanan sirri, ma’aikatan gwamnati, ladabi da tarbar baƙi, hulɗa da jama’a da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, walwala da kayan aiki, wayar da kan mata da matasa, harkokin addini, masarautu da shugabannin gargajiya, fasahar sadarwa, ƙungiyoyin goyon baya, ƙungiyoyin ’yan asalin jihar, nishaɗi da kuma masu buƙatu na musamman.
An naɗa Alhaji Ahmed Abdulkadir Bakori a matsayin Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, tare da Alhaji Mansir Liman da Alhaji Isah Ame a matsayin mataimakan sa. Hon. Dakta Bala Salisu Zango zai zama sakataren sashen, yayin da Alhaji Sabo Musa Hassan aka naɗa a matsayin mai gabatar da shirye-shiryen taruka na hukuma.
Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Dakta Nasiru Mu’azu Ɗanmusa a matsayin Daraktan Tsare-tsare da Dabarun Aiki, Farfesa Umar Adamu Katsayal a matsayin Daraktan Bincike da Ƙididdiga, Hon. Malik Anas a matsayin Daraktan Kuɗi, da kuma tsohon mataimakin sufeto-janar na ’yan sanda, AIG Mustapha Bala Sandamu, a matsayin Daraktan Tsaro da Tattara Bayanai na Sirri.
Kwamitin ya kuma tanadi kafa kwamitocin da za su daidaita ayyuka a ƙananan hukumomi da gundumomi domin ƙarfafa hulɗa da jama’a da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a a duk faɗin jihar.
Jam’iyyar ta bayyana cewa za a fitar da sunayen mambobin kwamitocin ƙananan hukumomi da gundumomi, da sauran kwamitocin dindindin da ƙarin mambobin sassan aiki, nan gaba.
Ƙirƙirar kwamitin yaƙin neman zaɓen na Jihar Katsina na zuwa ne bayan ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC na 2027 a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja ranar Laraba.
A wani saƙo na daban, Gwamna Raɗɗa, wanda kuma shi ne mai kula da yaƙin neman zaɓen sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a jihar, ya taya ’yan asalin Katsina da aka rantsar a cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen na ƙasa murna, tare da kira a gare su da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan al’umma a matakin ƙasa da ƙasa.
Raɗɗa ya bayyana rantsar da su a matsayin nauyin da ya rataya a wuyan su na yi wa jam’iyya da al’umma hidima, inda ya buƙace su da su nuna ƙwazo, gaskiya, juriya da jajircewa wajen gudanar da ayyukan yaƙin neman zaɓen.
Ya ce: “Rantsar da ku ya zo da manyan nauye-nauye da kuma tsammanin al’umma daga gare ku. Ina umartar ku da ku yi amfani da gogewar ku, ƙwarewar jagoranci da hanyoyin hulɗar ku a siyasa wajen inganta wayar da kan al’umma, faɗaɗa hulɗa da jama’a da kuma ƙarfafa goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Tinubu.”
Gwamnan ya buƙaci mambobin kwamitin da su guji abubuwan da za su ɗauke hankalin su daga siyasa mai amfani da kuma rigingimun da ba su da muhimmanci, yana mai jaddada cewa haɗin kai, ladabi da kyakkyawan tsarin hulɗa su ne muhimman abubuwan da za su taimaka wajen cimma manufofin yaƙin neman zaɓen.
Ya kuma yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin sassan kwamitin, tare da ci gaba da yin aiki tare da shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki da magoya baya a matakin ƙasa da ƙasa a Jihar Katsina, Arewa-maso-Yamma da sauran sassan ƙasar.
A cewar sa, shirin Renewed Hope Agenda 2.0 wata dama ce ta ƙarfafa sauye-sauyen da ake yi a ƙasa, tare da bunƙasa damar tattalin arziki, raya ababen more rayuwa, inganta jin daɗin al’umma da tabbatar da cigaba mai haɗa kowa da kowa.
Raɗɗa ya bayyana amannar sa da cewa mambobin kwamitin za su bayar da gagarumar gudunmawa wajen ƙoƙarin jam’iyyar na jawo goyon bayan jama’a gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ya kuma buƙace su da su kasance masu gudanar da harkokin siyasa cikin mutunci da kuma kyakkyawan ɗabi’a.
Kafa kwamitin yaƙin neman zaɓen na Jihar Katsina ya samar wa APC da tsarin gudanar da ayyukan ta na zaɓen 2027 a jihar, inda aka raba nauyin aiki tsakanin shugabanci, kwamitin ba da shawara, sassa na musamman da kwamitocin da za su kula da ayyuka a matakin ƙananan hukumomi da gundumomi.







