• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Zaɓen 2027: Idris ya yi gargaɗi kan sayen ƙuri’u, rashin fitowar masu zaɓe da rikicin zaɓe

Ashafa Murnai Barkiya by Ashafa Murnai Barkiya
October 16, 2026
in Labarai
A A
0
Zaɓen 2027: Idris ya yi gargaɗi kan sayen ƙuri’u, rashin fitowar masu zaɓe da rikicin zaɓe
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Alhaji Mohammed Idris, tare da Darakta-Janar na Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA), Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, da sauran manyan baƙi a wurin ƙaddamar da yaƙin wayar da kan al’umma a faɗin ƙasa domin zaɓen shekarar 2027, a ranar 15 ga Oktoba, 2026, a Abuja. (Mai hoto: Khalid Ahmed/FMINO)

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su guji halin ko-in-kula da zaɓe, da sayar da ƙuri’u, da kuma tashin hankali a lokacin zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.

Idris ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin ƙaddamar da gangamin wayar da kan al’umma da Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) ta fara a faɗin ƙasar domin shirye-shiryen zaɓen 2027.

Ya ce zaɓe yana bai wa ’yan ƙasa damar zaɓar wakilan su da kuma taka rawa wajen tsara makomar ƙasar, yana mai gargaɗin cewa rashin shiga harkokin zaɓe, sayar da ƙuri’u da tashin hankali na raunana dimokiraɗiyya.

Ya ce: “Idan masu kaɗa ƙuri’a suka ƙaurace wa zaɓe, suka sayar da ƙuri’un su ko suka tada hankali, hakan na raunana tsarin dimokiraɗiyya baki ɗaya.”

Idris ya ce Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen ƙarfafa tsarin dimokiraɗiyya a Nijeriya ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya yi nuni da Dokar Zaɓe ta 2026, wadda ya ce ta kawo sauye-sauye domin inganta gaskiya da riƙon amana, tare da ƙara amincewar jama’a da zaɓe.

Ministan ya yaba wa Darakta-Janar na NOA, Malam Lanre Issa-Onilu, da ma’aikatan hukumar bisa ƙaddamar da gangamin, yana mai jaddada cewa nasarar sa za ta dogara ne da haɗin gwiwar hukumomin gwamnati, hukumomin zaɓe, jami’an tsaro, shugabannin al’umma da kuma ’yan ƙasa.

Issa-Onilu ya ce NOA za ta yi amfani da ofisoshin ta da ke jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja, wajen isar da saƙonnin gangamin zuwa ga al’umma ta hanyar amfani da harsunan gida, shirye-shiryen rediyo, tattaunawa da jama’a, wasan kwaikwayo da kuma kafafen sadarwa na zamani.

Ya ce gangamin zai ƙarfafa jama’a su shiga zaɓe, ya hana sayen ƙuri’u da tashin hankali a lokacin zaɓe, tare da wayar da kan jama’a kan muhimmancin yaɗa sahihan bayanai yadda ya kamata.

Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya sake jaddada aniyar hukumar ta gudanar da sahihin zaɓe da zai bai wa kowa dama. Ya ce cimma wannan buri yana buƙatar fara shirye-shirye tun da wuri, haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki da kuma shigar jama’a cikin harkokin zaɓe.

Manufar gangamin ita ce shawartar ’yan Nijeriya su yi zaɓen 2027 yadda ya kamata, su mutunta zaɓin wasu, tare da ƙin duk wani mataki da zai jefa rayuka cikin haɗari, ya kawo barazana ga haɗin kan ƙasa ko ya raunana dimokiraɗiyya.

Tags: INECJoash Ojo AmupitanLanre Issa-OniluMohammed IdrisNOAzaben2027
Previous Post

APC ta naɗa Ɗangiwa Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu/Dikko na 2027 a Katsina

Next Post

2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki a fakaice

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki a fakaice

2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki a fakaice

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!