Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen sa na jam’iyyar APC gabanin babban zaɓen 2027, inda ya buƙaci shugabannin jam’iyyar da membobin kwamitin su haɗa kai, su kasance masu jajircewa da kuma mayar da hankali wajen ganin an sake zaɓen sa karo na biyu.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin bikin ƙaddamar da kwamitin a Cibiyar Taro ta Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ya ce a shirye APC take ta sabunta alƙawarin ta da ‘yan Nijeriya.
Shugaban ya ce nasarar zaɓen da ya gabata ba za ta wadatar ba har sai jam’iyyar ta sake samun nasara a zaɓen 2027, yana mai cewa dole ne shugabanni da masu ruwa da tsaki su tabbatar da samun ƙuri’u a mazaɓu, ƙananan hukumomi da jihohin su.
Ya jaddada cewa duk da yadda kwamitin zai ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a da neman goyon baya, gwamnatin sa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan mulki da aiwatar da manufofin Ajandar Sabuwar Fata.


Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yaba da jajircewar Tinubu wajen zurfafa dimokiraɗiyya, yayin da ya soki tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar kan kalaman da ya ce suna rage martabar ofishin shugaban ƙasa.
Shettima ya soki ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, bisa zargin amfani da alƙaluma marasa inganci da kuma kwatanta Nijeriya da wasu ƙasashe ba tare da la’akari da bambancin yanayin su ba.
A nasa ɓangaren, Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce kwamitin zai gudanar da yaƙin neman zaɓe daga mazaɓu zuwa jihohi, tare da bayyana nasarorin gwamnati da manufofin ta ga jama’a.
Gwamnan Jihar Imo kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC, Hope Uzodimma, ya ce manufofin gwamnatin Tinubu za su taimaka wajen sauƙaƙa aikin yaƙin neman zaɓen, yana mai yaba wa shugaban kan cire tallafin man fetur da sauye-sauyen tsarin musayar kuɗaɗen waje da haraji.
Ya ce waɗannan matakai sun taimaka wajen bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya zuwa kashi 4.43 cikin 100, daga kashi 4.23 cikin 100 a shekarar da ta gabata, duk da cewa sun jawo wasu matsaloli ga jama’a.
Uzodimma ya ce yaƙin neman zaɓen zai mayar da hankali kan manufofi da nasarorin da aka samu.

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, Gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo, da Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, sun bayyana goyon bayan su ga sake zaɓen Tinubu a 2027.
Wike, wanda ɗan jam’iyyar PDP ne, ya ce yana goyon bayan shugaban ne saboda jajircewar sa wajen fuskantar matsalolin da gwamnatocin baya suka kasa magancewa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da wasu manyan jiga-jigan ƙasa su ma sun buƙaci ‘yan Nijeriya da su mara wa Tinubu baya domin ya kammala ayyukan da ya fara.









