Hukumar Hadahadar Kuɗi ta Akrika (Africa Finance Corporation AFC) ta naɗa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Olayemi Cardoso, a matsayin sabon Shugaban Kwamitin Daraktoci.
Ma’ana da manyan ayyukan AFC shi ne samar da kuɗi, zuba jari da ƙwarewar gudanarwa domin gina muhimman ababen more rayuwa da bunƙasa masana’antu a Afrika, tare da samun ribar da ta dace ga masu hannun jarin ta.
Cardoso ya maye gurbin Ireti Samuel-Ogbu, wadda ta kammala wa’adin ta na shugabancin kwamitin, amma za ta ci gaba da kasancewa mamba a cikin kwamitin.
Ƙwarewar Cardoso a harkokin kuɗi da tattalin arziki ce ta sa aka ga cancantar naɗa shi wannan muƙami, kamar yadda sanarwar AFC ta bayyana.
“Cardoso na da ƙwarewa a harkokin banki na ƙasa da ƙasa, kula da zuba jari, tsara manufofin tattalin arziki da gudanar da ayyukan gwamnati.
Tun bayan naɗin sa a matsayin Gwamnan CBN a watan Satumban 2023, ya jagoranci sauye-sauye a tsarin kuɗi da bankuna, da nufin daidaita tattalin arzikin Nijeriya, ƙarfafa amincewar masu zuba jari da inganta tsarin gudanar da bankin.”
Daga cikin matakan da CBN ya ɗauka ƙarƙashin jagorancin Cardoso, akwai gyaran kasuwar musayar kuɗaɗen ƙasashen waje, magance tsofaffin basussukan musayar kuɗi da ƙarfafa tasirin manufofin kuɗi.
Haka kuma CBN ya kammala shirin ƙara jarin bankunan Nijeriya, domin ƙarfafa ƙarfin tsarin hada-hadar kuɗi.
Tarihin aiki da karatun sa dai kafin ya zama gwamnan CBN, Cardoso ya shafe shekaru 12 yana shugabantar Citibank, sannan ya riƙe muƙamin Kwamishinan Tsare-tsaren Tattalin Arziki da Kasafin Kuɗi na Jihar Legas.
Ya yi karatun digirin sa na farko a Jami’ar Aston da ke Birtaniya, sannan ya samu digiri na biyu a fannin gudanarwar gwamnati daga Makarantar Gwamnati ta Harvard Kennedy da ke Amurka, inda ya taɓa zama mamba a kwamitin tsofaffin ɗalibai.
AFC na sa ran samun gudummawar Cardoso, kamar yadda
Shugaban AFC kuma Babban Daraktan Gudanarwar ta, Samaila Zubairu, ya bayyana cewa ƙwarewar Cardoso za ta taimaka wajen ciyar da manufofin ƙungiyar gaba, musamman wajen tattara jari da bunƙasa ababen more rayuwa da masana’antu a Afirka.
Zubairu ya ce ƙungiyar na da burin aiwatar da shirin ta na ‘The Africa We Build 2050’, wanda ke mayar da hankali kan amfani da jarin Afirka wajen gina ababen more rayuwa, bunƙasa masana’antu da samar da ayyukan yi.
Ya kuma gode wa tsohuwar shugabar kwamitin, Ireti Samuel-Ogbu, bisa gudummawar da ta bayar a lokacin shugabancin ta.
Cardoso ya jaddada muhimmancin samar da ayyukan yi a lokacin da yake tsokaci kan naɗin nasa.
Gwamna Cardoso ya ce bunƙasa ƙarfin samar da kayayyaki da ayyuka zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka.
Ya bayyana cewa zai yi aiki tare da kwamitin, shugabannin gudanarwa da ƙasashe mambobin AFC domin ciyar da shirin ‘The Africa We Build 2050’ gaba.
A cewar sa, ya kamata a auna nasarar shirin bisa ƙarfin samar da kayayyaki da aka gina, masana’antun da aka taimaka aka kafa da kuma ayyukan yi da aka samar.
Daga cikin ayyukan more rayuwa da AFC ke tallafawa, ƙungiyar na daga cikin manyan hukumomin da ke samar da kuɗaɗe domin ayyukan more rayuwa da masana’antu a nahiyar Afirka.
Daga cikin manyan ayyukan da ƙungiyar ta tallafa wa kwanan nan akwai kammala yarjejeniyar samar da kuɗaɗen aikin layin dogo na Lobito Corridor a Angola, wanda ya kai dala miliyan 753.
Aikin ya shafi gyara da inganta layin dogon mai tsawon kilomita 1,300, tare da tabbatar da gudanar da ayyukan sa na dogon lokaci.
Zuba jari a masana’antu da ababen more rayuwa na dijital na daga abin da ƙungiyar AFC ta tallafa wajen samar da dala miliyan 600 domin faɗaɗa shirin samar da takin zamani na Kamfanin Dangote, wanda ya kai dala biliyan bakwai.
Bugu da ƙari, ƙungiyar ta yi alƙawarin zuba jari tare da ‘Vision Invest’, inda za su haɗa jarin dala miliyan 300 a kamfanin WIOCC Group domin faɗaɗa muhimman ababen more rayuwa na dijital a faɗin nahiyar.
A cewar AFC, waɗannan ayyuka na da nufin haɗa kasuwanni, ƙarfafa hanyoyin samar da kayayyaki na masana’antu da jawo ƙarin jari domin bunƙasa tattalin arzikin Afrika.







