Wasu ƙungiyoyin Musulmi sun kai fitaccen malamin addinin Musulunci mazaunin Kano ɗin nan, Lawan Abubakar Triumph, Kotun Shari’a ta Ƙoli da ke Ƙofar Kudu, Kano, bisa zargin aikata saɓo.
Lamarin ya fara bayyana a gaban kotun da ke cikin birnin Kano, inda lauyan masu ƙara, Barista Aliyu Usman Hajj, ya shaida wa alƙalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, cewa waɗanda yake wakilta sun shigar da ƙarar laifi kai-tsaye kan malamin.
Barista Hajj ya roƙi kotun da ta aika da ƙarar ga Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano domin gudanar da bincike.
Sai dai lauyan wanda ake ƙara, Barista Abdurrazak A. Ahmad, ya nemi a ba shi lokaci domin nazarin zarge-zargen da ake yi wa wanda yake karewa tare da gabatar da martanin kariya.
Lauyan ya kuma ƙalubalanci hurumin kotun na sauraron shari’ar. Barista Ibrahim Umar na cikin tawagar lauyoyin da ke kare Malam Lawan.
A yayin zaman, masu ƙarar sun kuma nemi kotun ta bayar da umarnin rufe masallacin da Lawan ke jagoranta har sai an kammala shari’ar.
Sai dai kotun ta yi watsi da buƙatar, tana mai cewa ba ta da hurumin bayar da umarnin rufe masallacin.
Bayan sauraron bahasin ɓangarorin biyu, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 24 ga Satumba, 2026, domin kotun ta bayyana matsayin ta kan batun.
Zarge-zargen da ake yi wa Malam Lawan dai har yanzu suna gaban kotu, kuma ba a tabbatar da su ba.







