Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) na Jihar Neja, Mista Suberu Siyaka Aniviye, tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan mutuwar wasu mutane da aka kama bisa zargin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a Minna.
Rahotanni sun ce an kama mutanen ne a yayin wani samame da jami’an hukumar suka gudanar a yankin M.I. Wushishi/Lukoto tsakanin ranakun 15 zuwa 16 ga Satumba, 2026.
An gano cewa mutanen sun mutu ne a safiyar ranar 17 ga Satumba, inda adadin waɗanda suka rasa rayukan su ya kai 37, kamar yadda Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayyana.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwar mutanen.
Ya kuma tabbatar da cewa Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, wanda lamarin ya faru a ƙarƙashin kulawar sa, zai ci gaba da kasancewa cikin dakatarwa har sai an kammala binciken.
Ministan ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankula tare da bai wa hukumomin da abin ya shafa damar gudanar da binciken cikin gaskiya da bin ƙa’idojin doka.
Haka kuma, NSCDC ta kafa wani kwamitin bincike na musamman domin gudanar da bincike kan lamarin.
Kwamitin zai duba halin da waɗanda aka kama suke ciki a lokacin da aka kama su, yanayin tsarewar da aka yi musu, irin kulawar lafiyar da suka samu, da kuma sauran abubuwan da ka iya kasancewa da alaƙa da mutuwar su.
Hukumar ta bayyana cewa duk wani jami’i da bincike ya tabbatar da cewa ya karya doka ko ƙa’idojin aiki zai fuskanci matakin da ya dace, wanda zai iya haɗawa da hukuncin ladabtarwa ko kuma na shari’a, gwargwadon abin da binciken ya tabbatar.
A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya tabbatar da cewa an kafa wani kwamitin bincike na musamman domin gano musabbabin mutuwar mutanen.
Ya ce an kuma fara gudanar da gwaje-gwajen lafiya da binciken gano musabbabin mutuwa (autopsy) domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar.
Gwamnan ya yi kira ga jama’a da su guji ɗaukar doka a hannun su, yana mai cewa har yanzu ba a tabbatar da ainihin musabbabin mutuwar mutanen ba, don haka ya kamata a bai wa hukumomin da ke gudanar da bincike damar kammala aikin su.






