• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Sarkin Lafiya ya yaba wa Bago kan nasarorin da yake samu a Neja

FATI ABDUL by FATI ABDUL
September 13, 2026
in Labarai
A A
0
Sarkin Lafiya ya yaba wa Bago kan nasarorin da yake samu a Neja
Daga dama: Sarkin Lafiya, Mai Shari’a Sidi Dauda Bage Muhammad II, yana gabatar da addu'a tare da Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, a lokacin ziyarar a Bida

Daga dama: Sarkin Lafiya, Mai Shari’a Sidi Dauda Bage Muhammad II, yana gabatar da addu'a tare da Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, a lokacin ziyarar a Bida

Sarkin Lafiya a Jihar Nasarawa, Mai Shari’a Sidi Dauda Bage Muhammad II, ya yaba wa Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, kan nasarorin da gwamnatin sa take samu.

Bologi Ibrahim, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, ya faɗa a wata sanarwa ga manema labarai a yau Lahadi, 13 ga Satumba, 2026, cewa Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da Gwamna Bago ya kai masa ziyarar ban-girma a Bida, inda Sarkin ya halarci bikin cika shekaru 23 da Sarkin Nupe kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Neja, Alhaji Yahaya Abubakar, ya yi kan karagar mulki.

Mai Shari’a Bage ya ce ya ji daɗin irin nasarorin da Gwamna Bago ya samu, musamman aikin gina babbar hanyar Minna zuwa Bida mai layuka biyu.

Sarkin ya bayyana jin daɗin sa kan yadda aikin hanyar yake gudana cikin sauri, tare da yin addu’ar Allah ya ci gaba da yi wa gwamnan jagora yayin da yake gudanar da aikin sa na yi wa al’ummar Jihar Neja hidima.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Neja da su mara wa Bago baya tare da ci gaba da ba shi dukkan goyon bayan da ya dace domin ba shi damar cimma manufofin gwamnatin sa.

Taron jama’a a lokacin ziyarar

A nasa jawabin, Gwamna Bago ya gode wa Sarkin bisa irin rawar da yake takawa wajen haɗa kan ’yan Nijeriya.

Ya ce zai ci gaba da neman shawarwarin sarkin na uba, yana mai cewa yana matuƙar girmama shi.

Haka kuma Bago ya kai irin wannan ziyarar ban-girman ga Sarkin Doma, wanda shi ma ya je Bida domin halartar bikin cika shekaru 23 da Sarkin Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, ya yi kan karagar mulki.

Tags: Gwamna Mohammed Umar BagoMai Shari’a Sidi Dauda Bage Muhammad IINejaSarkin Lafiyaziyara
Previous Post

Uwargidan Gwamnan Neja ta zama babbar uwar ƙungiyar BWI/RHA

Next Post

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!