Kafin na fara gani da sanin Hajiya Hakama Sidi-Ali cikin 1990 a farkon shiga ta Jami’ar Bayero (BUK), an taɓa yin wata mata a garin mu Barkiya mai suna Hakama tun muna yara. Da yake ban yi wayon sanin mijin ta ba tun daga tasowa ta cikin shekarun ƙarshen saba’o’i (1970s), sai ake kiran gidan da Hakama take da suna gidan Hajiya Hakama.
A Barkiya da kewaye, har ma da duk garuruwan da na taɓa zuwa ko zama, ban ƙara jin sunan Hakama ba, sai da na shiga Jami’ar Bayero. Hakama ɗin da na sani a jami’ar ita kaɗai ce ɗaya tilo mai wannan suna. Kuma daga ita har yau ban ƙara ji ko ganin mai suna irin nata ba.
Hakama ɗin da na fara sani a Barkiya, attajirar ƙauye ce, domin a karkarar mu rankatakaf ita ce mace ta farko da ta fara zuwa Hajji. Ko a cikin maza ma waɗanda suka je Hajji a ƙasa ne kaɗai suka riga ta zuwa sauke farali. A gefen gidan Hajiya Hakama kuma a gefen hanya, akwai rijiya wacce ko ruwan ƙorama bai fi ruwan ta daɗi ba. Dalili kenan idan matafiya suka isa wurin sukan yada zango su sha ruwa, su yi alwala, su shayar da dawaki ko jakunan su, kuma su ɗiba su yi guziri, sannan su nausa gaba.
Kamar Hajiya Hakama ta Barkiya kamar Hajiya Hakama da na sani a Jami’ar Bayero. Hakamar Barkiya ita kaɗai ce mai irin sunan duk karkarar mu, a zamanin ta. Haka ma ita ma Hakama ta Jami’ar Bayero, ita kaɗai ce mai sunan, kuma har yau ita kaɗai na sani mai suna Hakama a Kano, birnin da aka taɓa yin mai suna Kundila shi ɗaya tilo.
Wannan Hakama dai a yanzu ita ce Kakakin Yaɗa Labarai, Daraktar Riƙo a Sashen Sadarwa da Hulɗa da Masu Zuba Jari a Babban Bankin Nijeriya (CBN).
Hakama Sidi Ali ta kasance mace ta farko wadda ta riƙe wannan muƙami a CBN. Muƙami ne mai matuƙar muhimmanci a ƙasa. Kamar yadda kowace jiha ke da gwamna, haka ma CBN ke da gwamna, wanda shi ne Hakama ke aiki a ƙarƙashin sa. Kai da ji an ce wance ita ce Kakakin Yaɗa Labarai ta CBN, kai ka san akwai maganar ƙwarewa ba taƙarƙarewa ba.
A fannin aikin jarida da ƙwarewa ta fannin hulɗar da jama’a, Hajiya hakama ta yi wa mata zarra. Mazan ma sai irin su wane da wane. Karan ta ya kai tsaikon da har aka ga cancantar naɗa ta muƙamin kakakin CBN.
Al’amarin Hakama akwai jajircewa, ba haƙiƙicewa ba. Mace ce mai himma ba hayaniya ba. Akwai ta da juriya, ba gaganiya ba. Ta yi kwasa-kwasai da dama, shi ya sa a aikin ta ba ta kwafsawa. Hakama ta san aiki, ba irin aikin ‘yan aikatau take yi ba. Ga ta da ƙoƙari, ba ci-da-ƙarfi take yi ba.
Hasken tauraruwar Hakama ya ƙara fito da annurin kyawawan manufofi da tsare-tsaren bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da CBN ke yi a ƙarƙashin jagorancin Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso. Kwarewar ta wajen iya hulɗa da jama’a ya ƙara fitowa fili duba da irin yadda ta yayata tsare-tsare da shirin ƙarfafa jarin bankuna, haskaka kyawawan manufofin CBN ga masu zuba jari na gida da na waje, da sauran manufofin bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya.
Yadda CBN yake shi ɗaya tilo a Nijeriya, haka Hakama take ita ɗaya tilo mai wannan suna da ta shahara a Nijeriya da wasu ƙasashe. A shekaru uku da ta yi kan muƙamin Kakakin Yaɗa Labarai ta CBN, ta samu lambobin yabon karramawa ba sau ɗaya ko sau biyu ba a Nijeriya. Har a Afrika ma Hakama ta ciri tuta. Kwanan nan ta karɓi kambin Tauraruwar Hulɗa da Jama’a ta 2026 a Nijeriya, a wani ƙasaitaccen taron da aka yi a otal ɗin NICON Luxury, Abuja.
A ƙarƙashin ofishin Hakama Sidi Ali, CBN ya bayyana manyan nasarori 30 da CBN ya samu cikin 2026, bayan wasu fiye da 20 da ya samu cikin 2025. Nasarorin 2026 sun haɗa da:
1. Samun nasarar kammala Shirin Ƙarfafa Jarin Bankuna, wanda zuwa adadin jarin bankunan Nijeriya ya ƙaru da fiye da naira tiriliyan 4 a ƙarshen Maris, 2026.
2. Ɗaga darajar irin su Opay, Moniepoint, Palmpay zuwa cikakkun bankunan hadahadar kuɗi.
3. Tumbatsar asusun ajiyar kuɗaɗen waje zuwa kusan dala biliyan 53.
4. Fito da tsarin magance yawan samun tangarɗa da matsalolin katin ATM da na’urorin ATM.
5. Yadda Tarayyar Turai (EU) ta bi sahun hukumar FATF, ta cire sunan Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ke da hatsarin safarar kuɗi.
6. Kafa Kwamitin PSPC, wanda zai sa-ido kan tsarin biyan kuɗi ta hanyar fasahar zamani.
7. Batun kafa kwamitin sulhu domin warware rikice-rikicen masu taurin-bashi a bankuna.
8. Yadda CBN ya bankaɗo ‘yan damfara masu ƙoƙarin kutsen satar kuɗin ajiyar kwastomomin bankuna.
9. Gindaya sharuɗɗa kan BVN domin tsaurara matakan kare kuɗaɗen kwastomomi a bankuna.
10. Ci gaba da danne malejin hauhawar farashi domin hana shi cillawa sama.
11. Yabon da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, kan nasarorin sauye-sauyen tsarin kuɗi da shirin ƙarfafa yawan jarin bankuna.
12. Shan laƙani da dafa’i masu ƙarfin hana girgizar tattalin arzikin duniya yi wa Nijeriya barazana.
13. Ci gaba da gindaya ƙa’idoji da sharuɗɗan hana wasu bankuna raba ribar ƙarshen shekara, sanadiyyar ƙaƙudubar bashin naira tiriliyan 2.9 da suka bai wa Nestoil, bayan kamfanin ya kasa biyan kuɗin.
14. Gargaɗi da jan-kunne ga gwamnatocin jihohi tare da nuna masu illar ciwo bashin alaƙaƙai mai zame wa jihohi jangwangwama.
15. Ambaliyar masu zuba jari cikin Nijeriya, bayan sun yi amanna da nagartattun sauye-sauyen manufofin tattalin arziki da CBN ya bijiro da su.
16. Ƙaddamar da sabon kundin dokokin canjin kuɗaɗen waje.
17. Samun jinjina da ƙarin daraja daga S&P, kamfanin tantace daraja ko naƙasun manufofin kuɗi na ƙasashen duniya.
18. Ƙin amincewa da kiraye-kirayen komawa tsohon tsarin bayar da tallafin lamuni.
19. Shirin rage yawan takardun naira da ke hannun jama’a zuwa ƙasa da kashi 40 cikin 100, nan zuwa ƙarshen 2028.
20. Kafa wa bankuna sharaɗin riƙa bibiyar dalilin yadda kwastomomi ke tura kuɗaɗe daga asusun ajiyar su na kuɗaɗen waje.
21. Jinjina da yabon da Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF) ya yi wa CBN, sakamakon nasarar shirin ƙarfafa jarin bankuna.
22. Yadda CBN ya haskaka birnin Landan da duniya yayin da bankin ya lashe Kyautar Gwarzon Babban Banki na Shekara.
23. Fitar da sabbin ƙa’idojin bayar da lasisi da sa-ido kan kamfanonin rukunin harkokin kuɗi (HoldCos).
24. Saisaita gejin ribar rancen dare ɗaya biya washegari da sassafe a tsakanin bankuna (NOFR).
25. Gaggauta kulle asusun ajiya da kadarorin waɗanda gwamnatin tarayya ta zarge su da tallafa wa ta’addanci.
26. Shirin fara aikin wallafa bayanan sauye-sauyen tattalin arziki da nasarorin da CBN ya samu daga 2023 zuwa 2026.
27. Buɗe rajistar gwajin sabbin fasahohin bankuna, kamfanonin fintech da na kirifto.
28. Bijiro da damammakin da suka kamata ƙasashen Afirka su runguma yayin da duniya ke fuskantar barazanar jijjigar tattalin arziki.
29. Matakan daƙile kaka-gidan kamfanonin fintech.
30. Bayyana bin-diddigin gudanar da hadahadar naira tiriliyan 372 cikin 2025 a Nijeriya.
Tabbas idan aka yi nazari da la’akari da waɗannan nasarori 30 na wannan shekara, alamomi na ci gaba da nuna yadda Hakama Sidi Ali ke bada himma, ƙwazo da nuna rashin kasala wajen yaɗa kyawawan manufofi da tsare-tsaren CBN.
Idan har za a riƙa yi wa CBN kirari cewa shi ne ‘jagoran bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya’, to ya cancanta a riƙa yi wa Hajiya Hakama jinjina da kirarin ‘tauraruwar haskaka manufofin CBN’.






