Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya taya tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, murnar cika shekaru 85 da haihuwa, inda ya bayyana shi a matsayin dattijo kuma jagora abin koyi.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran sa, Bologi Ibrahim, ya fitar ranar Lahadi, Gwamna Bago ya bayyana Babangida a matsayin jagora mai hangen nesa, kishin ƙasa da jajircewa, wanda gudunmawar sa ga cigaban Nijeriya har yanzu tana da muhimmiyar rawa.
Gwamnan ya yaba da jarumtaka, kwarjini da jajircewar Babangida wajen yanke shawara, musamman a lokacin da yake shugaban mulkin soja na Nijeriya, yana mai cewa shugabancin sa ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da daidaito a ƙasar.
A cewar Bago, wasu manufofi da aka ƙaddamar a lokacin mulkin Babangida sun taimaka wajen ci gaban ƙasar, inda wasu daga cikin amfanin su har yanzu ake ci da su.
Ya kuma yaba wa tsohon shugaban mulkin soja saboda ci gaba da mai da hankali da jajircewa wajen bayar da gudunmawa ga cigaban ƙasa, shekaru da dama bayan ya bar aikin gwamnati na soja.
Gwamnan ya ce: “Janar Babangida ya ci gaba da bayar da shawarwari masu amfani domin ci gaban al’umma, kuma ya zama fitila mai haskakawa da hasken fata ga matasa.”
Bago ya bi sahun iyalan Babangida, abokan sa da masu yi masa fatan alheri wajen gode wa Allah bisa ni’imomin da Ya yi wa tsohon shugaban mulkin sojan, tare da yi masa addu’ar Allah Ya ci gaba da ba shi ƙarfi da lafiya.
Ya kuma roƙi Allah Ya ƙara wa Babangida shekaru domin ya ci gaba da bayar da gudunmawa ga bil’adama da ci gaban ƙasa.







