Daraktar Riƙo a Sashen Sadarwa da Hulɗa da Masu Zuba Jari ta Babban Bankin Nijeriya (CBN), Hajiya Hakama Sidi-Ali, lashe lambar kyautar kambin Tauraruwar Hulɗa da Jama’a ta 2026 a Nijeriya.
An gudanar da wannan gagarumin biki a jiya Lahadi, a otal ɗin NICON Luxury da ke Abuja, inda taron ya samu halartar ɗimbin jama’a.
Wannan shi ne karo na shida kenan ana shirya wannan bikin bayar da lambobin yabo, wanda ake yi a tsakanin kakakin yaɗa labarai daban-daban a ƙasar nan.
Karramawar da aka yi wa Hakama Sidi-Ali wata gagarumar nasara ce da za a ce ta ƙara samu kenan har sau uku a jere, bayan ta zama ƙwararriyar jami’ar sadarwa ta farko da ta fara da lashe lambar yabo ta musamman ga ɓangaren da take aiki a kai sau biyu a jere, kafin daga bisani ta lashe babbar lambar yabo ta Jakadiyar Hulɗa da Jama’a ta Shekara.
Nasarar ta zo ne shekaru uku kacal bayan da ta kafa wani tarihi a shekarar 2023, lokacin da Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya naɗa ta a matsayin mace ta farko da ta taɓa zama mai magana da yawun CBN cikin tarihin shekaru 66 bayan kafuwar bankin.

An bayyana wannan karramawa ne yayin bikin bayar da lambar yabo ta shida ta National Spokespersons Awards da kuma lacca ta shekara ta huɗu ta mujallar Economic Confidential ke shiryawa, a ƙarƙashin Image Merchants Promotion Limited (IMPR), masu wallafa PRNigeria, Economic Confidential da Spokespersons Digest.
Sunan Hajiya Hakama a cikin manyan lambobin yabo na harkar sadarwa a Nijeriya ya kasance abin da aka gina bisa daidaito da kuma tasirin da za a iya auna shi.
A shekarar 2024, ta lashe lambar yabo ta Outstanding Spokesperson – Banking Sector inda ta zama mace ta farko a fannin sadarwar bankuna da ta samu wannan karramawa. Ta kuma sake riƙe wannan matsayi a shekarar 2025.
A shekarar 2026 ta taka muhimmiyar rawa wadda ta wuce fannin bankuna, da kuma rawar da ta taka wajen tsara sadarwar tattalin arzikin ƙasa, ƙarfafa amincewar jama’a ga CBN da kuma bayyana manufofin kuɗi na Nijeriya a duniya.
An bayar da lambar yabon ne bayan wani tsattsauran tsarin tantancewa da ya dogara da muhimman ƙa’idoji guda huɗu: tasiri, ƙirƙire-ƙirƙire da sabuwar dabara, yaɗuwar kamfen, da ingancin hujjojin da aka gabatar.
Shugabar masu tantancewar ta yaba da ƙoƙarin ta wajen gina tsarin sadarwa mai ɗaukar mataki tun da wuri a CBN bankin, ta hanyar gudanar da tarukan bayyana manufofin Kwamitin Manufofin Kuɗi na Bankin (MPC) a kai a kai, hulɗa da masu ruwa da tsaki, hulɗa da masu zuba jari, kula da kafafen yaɗa labarai da kuma wakiltar Nijeriya a fagen sadarwa na ƙasa da ƙasa.
Waɗannan matakai sun kuma jawo hankalin duniya, inda kamfen ɗin sadarwa na CBN ya zama ɗaya daga cikin waɗanda suka kai matakin ƙarshe a gasar duniya ta 2026 International Public Relations Association (IPRA) Golden World Awards.
A farkon wannan shekarar ce kuma aka karrama Hakama da lambar yabo ta gwarzayen mata na Afrika, wadda ake kira African Iconic Female Spokesperson of the Year a bikin African International Women Recognition Awards (AIWRA) 2026, bayan wata ƙuri’ar jama’a da aka gudanar a faɗin nahiyar Afrika.
Shugabar kwamitin alƙalan bayar da lambobin yabon, Farfesa Saudat Abdulbaqi, ta bayyana cewa a wannan shekarar ta 2026, an samu mutane 171 waɗanda aka tantace daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Ta ce bayan tantancewar farko, an bar waɗanda suka cika ƙa’idojin da suka shafi bayyana bayanai cikin tsari, tasirin da za a iya auna shi da kuma hujjojin da za a iya tabbatar da su, su ci gaba zuwa matakan tantancewa na gaba. A ƙarshe, aka samu ‘yan takara 30 daga fannoni 15.
A cewar Abdulbaqi, tsarin tantancewar ya kasance na gaskiya, ya dogara da hujjoji, kuma an tsara shi ne domin tabbatar da cewa lambar yabon ta nuna ƙwarewar aiki da aka tabbatar da ita, maimakon shahara ko suna kawai.
Da yake jawabi a wajen taron, Babban Daraktan IMPR, Alhaji Yushau A. Shuaib, ya ce an kafa wannan gasar ce domin inganta tattaunawar ƙasa mai ma’ana, karrama ƙwarewar aiki da kuma ƙarfafa dabarun sadarwa a Nijeriya.
Ya kuma sanar da cewa IPRA ta bai wa taron matsayin taron tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ƙasa, abin da ya ƙara ɗaukaka martabar taron a duniya tare da sanya shi cikin dandamalin ƙwararrun harkar sadarwa da duniya ta amince da su.
Bikin na shekarar 2026 ya karrama ƙwararrun jami’an sadarwa da ƙungiyoyi daga ɓangarorin gwamnati, kamfanoni da ƙungiyoyin sa-kai.
Shugaban ICPC, Dakta Musa Adamu Aliyu, wanda ya gabatar da babban jawabin taron, shi ma ya samu lambar yabo saboda rawar da ya taka wajen inganta yaƙi da cin hanci da rashawa.
Daga cikin waɗanda suka lashe wasu lambobin yabo akwai Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Abdurrahman Ahmed Bundi, Babban Mataimaki na Fasaha kan Sadarwar Dijital ga Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, yayin da Mataimakin Kwanturolan Kwastam na Ƙasa (ASC) Folusho Adeogun na Hukumar Kwastam ta Nijeriya ya tashi da shi lambar Matashin Jami’in Sadarwa na 2026.
Bayan waɗannan kuma an raba sauran kyaututtuka ga sauran waɗanda suka yi nasara a fannoni da dama.
Shugaban NIPR, Dakta Ike Neliaku, shi ne ya jagoranci bikin, wanda manyan jami’an gwamnati da ƙwararrun harkar sadarwa da dama suka halarta. Daga cikin su akwai Darakta-Janar na Muryar Nijeriya (VON), Jibrin Baba Ndace, wanda ya wakilci Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris; Farfesa Sule Ya’u Sule; jami’an diflomasiyya, shugabannin hukumomin tsaro, manyan ƙwararrun hulɗa da jama’a da malaman jami’a.







