Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana matuƙar alhini bisa rasuwar fitaccen ɗan siyasa a Jihar Neja, jagoran al’umma kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Ibrahim Wali, Garkuwan Kontagora.
Idris ya bayyana marigayin Wali a matsayin babban abokin hulɗa, amintaccen aboki kuma ɗan asalin Jihar Neja na ƙwarai, wanda rayuwar sa ta kasance cike da karamci, aminci da jajircewa wajen cigaban al’ummar sa.
Ya ce: “Na samu labarin rasuwar aboki na abin ƙauna ta kuma ɗan’uwa na, Alhaji Ibrahim Wali, Garkuwan Kontagora, cikin matuƙar alhini. Rasuwar sa babban rashi ne a gare ni, kuma babban rashi ne mai raɗaɗi ga al’ummar Masarautar Kontagora da Jihar Neja baki ɗaya,” inji ministan.
Ya ce marigayin ya yi fice wajen hidimta wa al’ummar sa tsawon shekaru, inda ya yi amfani da matsayin sa da dukiyar sa wajen tallafa wa jama’a da kuma inganta harkokin da suka taimaka wajen kyautata rayuwar su.
Ya ce: “Alhaji Ibrahim Wali mutum ne na jama’a a haƙiƙanin ma’anar kalmar. Ya fahimci cewa gata da tasiri suna tattare da nauyin taimaka wa wasu. Ya taɓa rayuwar mutane da dama ta hanyar ayyukan jinƙai, tallafa wa ilimi, ƙarfafa marasa galihu da kuma jajircewa wajen cigaban al’ummar sa.”
Idris ya ƙara da cewa Wali ya sauke nauyin da ke kan sa na sarautar gargajiya a matsayin Garkuwan Kontagora cikin mutunci da sadaukarwa, inda ya kasance mai kusanci da muradun jama’a tare da kasancewa amintaccen mai magana kan al’amurran da suka shafi Masarautar Kontagora da Jihar Neja.
“Zan yi kewar abotar sa, shawarar sa, kyakkyawar mu’amalar sa da kuma irin bajintar sa ta haɗa kan jama’a daga sassa daban-daban na al’umma. Mun yi rashin amintaccen aboki kuma ɗan kishin ƙasa wanda da gaske yake son cigaban al’ummar sa,” inji ministan.
Idris ya miƙa ta’aziyyar sa ga iyalan marigayin, Sarkin Sudan na Kontagora da ɗaukacin Masarautar Kontagora, da kuma Gwamnati da al’ummar Jihar Neja.
Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayi Garkuwan Kontagora kurakuransa, Ya saka masa da Aljannatul Firdausi bisa kyawawan ayyukan sa, sannan Ya ba wa iyalan sa da duk waɗanda rasuwar ta shafa ƙarfin haƙurin jure wannan rashi.






