Nijeriya da Amurka sun sake jaddada aniyar ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da yaƙi da ta’addanci, yayin da manyan jami’an ƙasashen biyu suka gudanar da taron ƙungiyar haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka kan yaƙi da ta’addanci a Washington DC.
Tawagar Nijeriya a taron tana ƙarƙashin jagorancin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, yayin da tawagar Amurka take ƙarƙashin jagorancin Allison Hooker, Mataimakiyar Sakataren Harkokin Waje ta Amurka mai kula da harkokin siyasa.
Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, da Ƙaramar Ministar Harkokin Waje, Ambasada Sola Enikanolaiye, suna cikin tawagar Nijeriya da suka halarci taron.
Taron ya mayar da hankali ne kan duba cigaban da aka samu a haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci tsakanin ƙasashen biyu, da kuma tsara matakan da za su ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro a nan gaba.
Wannan shi ne karo na biyu da ake gudanar da taron ƙungiyar haɗin gwiwar, bayan taron farko da aka gudanar a Abuja a watan Janairu 2026, a wani mataki na ƙarfafa musayar bayanan sirri da haɗin gwiwa wajen tunkarar matsalolin tsaro.

A yayin taron, ƙasashen biyu na duba hanyoyin ƙara kare al’ummomin da ke cikin haɗarin fuskantar tashe-tashen hankula da ake dangantawa da rikicin addini, da kuma sauran batutuwan da suka shafi moriyar ƙasashen biyu.
Haka kuma taron yana duba shirin dawo da mutanen da suka rasa matsugunan su sakamakon rikice-rikice zuwa gidajen su, tare da ƙara tabbatar da kariyar su da samar da yanayin da zai ba su damar komawa cikin aminci.
Daga cikin batutuwan da ake tattaunawa akwai inganta tattara bayanan sirri da haɗa ayyukan hukumomin tsaro, da kuma ƙarfafa matakan daƙile hanyoyin samun kuɗaɗen da ake amfani da su wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci.
Ƙasashen biyu suna kuma duba hanyoyin tabbatar da hukunta masu aikata laifukan ta’addanci, da ƙarfafa kula da iyakokin ƙasa domin daƙile safarar kayayyaki, mutane da albarkatun da ba su dace ba.
Bugu da ƙari, taron zai yi bitar taswirar shirye-shiryen tsaro da harkokin tsaro na Nijeriya da Amurka domin tabbatar da cewa haɗin gwiwar ƙasashen biyu ya dace da sabbin ƙalubalen tsaro da ake fuskanta.
Taron yana daga cikin matakan da Nijeriya da Amurka ke ɗauka domin ƙara inganta dangantakar tsaro da tsaron ƙasa, tare da samar da ingantaccen haɗin gwiwa wajen kare al’ummomi da tabbatar da zaman lafiya.







