• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Tsaron Cikin Ƙasa: Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar ƙarfafa haɗin gwiwa don zaman lafiya da cigaba – Idris

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
August 14, 2026
in Tsaro
A A
0
Tsaron Cikin Ƙasa: Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar ƙarfafa haɗin gwiwa don zaman lafiya da cigaba – Idris
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Tsaron Cikin Ƙasa, Manjo Janar Adeyinka Famadewa (mai ritaya), da sauran manyan jami'an gwamnati a lokacin ziyarar 

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Tsaron Cikin Ƙasa, Manjo Janar Adeyinka Famadewa (mai ritaya), da sauran manyan jami'an gwamnati a lokacin ziyarar 

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, hukumomin gwamnati da al’ummomi domin inganta zaman lafiya, tsaro da cigaban ƙasa.

Idris ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Tsaron Cikin Ƙasa, Manjo Janar Adeyinka Famadewa (mai ritaya), ya kai masa ziyarar ban-girma a Abuja.

Ministan ya tarbi tawagar, yana mai bayyana ziyarar a matsayin wata dama ta ƙara fahimtar ayyuka da nauyin da sabon Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Tsaron Cikin Ƙasa ke da shi, da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa wajen sanar da ‘yan Nijeriya manufofi da shirye-shiryen gwamnati kan tsaro.

Ya ce: “Zaman lafiya da tsaro muhimman abubuwa ne; a haƙiƙa, su ne tubalan da duk wani cigaba zai iya ginuwa a kan su a ko’ina.”

Ya jaddada cewa ba za a iya magance ƙalubalen tsaron Nijeriya ta hanyar matakin soji kaɗai ba, sai an ƙara haɗin gwiwa tsakanin rundunonin soji, hukumomin tsaro, gwamnatoci a dukkan matakai, al’ummomi, kafafen yaɗa labarai da sauran jama’a.

“Ba za ku iya magance wannan matsala da harbin bindiga kawai ba. Tsaro yana buƙatar haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, rundunonin soji da sauran jama’a,” inji shi.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Tsaron Cikin Ƙasa, Manjo Janar Adeyinka Famadewa (mai ritaya), lokacin ziyarar a Abuja

Ministan ya bayyana irin faɗin aikin da Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) da sauran hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar suke yi a matakin al’umma, yana mai cewa suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen ƙarfafa juriyar al’umma, inganta ɗaukar nauyin ɗan ƙasa da tabbatar da cewa jama’a na samun sahihan bayanai a kan lokaci.

Ya bayyana labaran ƙarya, bayanan da ba su da inganci da kuma yaɗa bayanan ƙarya da gangan a matsayin sababbin ƙalubalen tsaron ƙasa, yana mai jaddada buƙatar sadarwa mai ɗaukar nauyi da kuma ƙara wayar da kan jama’a kan kafafen yaɗa labarai da bayanai.

Tun da farko, Famadewa ya ce ya kawo ziyarar ne domin gina kyakkyawar alaƙar aiki da ma’aikatar, yana mai bayyana bayanai da wayar da kan jama’a a matsayin muhimman ginshiƙai na tsaron cikin gida na zamani.

Ya ce ofishin sa zai mayar da hankali kan haɗa bayanan sirri da sa-ido, ƙarfafa tsaron iyakokin ƙasa, inganta gano barazanar tsaro, da kuma samar da ingantattun matakai na bayar da rahoto da mayar da martani ga rikice-rikice.

“Bayanai suna da muhimmiyar rawar da suke takawa a yaƙin da ake yi ta hanyoyin da ba na gargajiya ba. Wanda ya fara magana shi ne ke yin galaba, kuma ba za mu zauna mu ƙyale wasu su tsara mana yadda mutane za su fahimce mu ba,” inji Famadewa.

 

Idris ya tabbatar wa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawarar cewa ma’aikatar za ta ba da cikakken haɗin kai, yana mai cewa ƙarfafa haɗin gwiwa, ingantacciyar sadarwa da taka rawar gani da ‘yan ƙasa za su yi za su taimaka wajen cimma hangen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganin Nijeriya ta zama ƙasa mai ingantaccen tsaro, zaman lafiya da wadata.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Babbar Sakataren Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dakta Binyerem C. Ukaire; Mai Bai wa Minista Shawara na Musamman kan Harkokin Gudanarwa, Dakta Sunday Baba; Daraktan Sadarwar Jama’a da Wayar da Kai, Henshaw Ogubike; Daraktan Hulɗa da Jama’a da Ƙa’idojin Gudanarwa, Dakta Suleiman Haruna; Mai Kula da Sashen Leƙen Asiri da Nazari, Manjo Janar Emmanuel Ndagi (mai ritaya); Mai Kula da Ayyuka, Manjo Janar Hassan Dada (mai ritaya); Darakta-Janar na Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC), Dakta Charles Ebuebu; Darakta-Janar na Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA), Dakta Salihu Abdulhamid Dembos; Darakta-Janar na Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; Darakta-Janar na Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), Malam Ali Muhammad Ali; da sauran manyan jami’ai daga Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Tsaron Cikin Ƙasa da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai.

Tags: Manjo Janar Adeyinka FamadewaMohammed Idristsaron cikin ƙasa
Previous Post

Nijeriya da Amurka sun ƙarfafa haɗin gwiwa don yaƙi da ta’addanci

Next Post

Hukumar ilimi ta N-SUBEB za ta dasa bishiyoyi a makarantu 150 a Neja

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Hukumar ilimi ta N-SUBEB za ta dasa bishiyoyi a makarantu 150 a Neja

Hukumar ilimi ta N-SUBEB za ta dasa bishiyoyi a makarantu 150 a Neja

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!