• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Hanyar Sakkwato zuwa Badagiri mai tsawon kilomita dubu za ta bunƙasa noma a Arewa – Idris

WAKILIN MU by WAKILIN MU
August 13, 2026
in Labarai
A A
0
Hanyar Sakkwato zuwa Badagiri mai tsawon kilomita dubu za ta bunƙasa noma a Arewa – Idris
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da tawagar masu yaɗa labarai na gwamnatin jihar ta kai masa ziyarar ban-girma a ofishin sa a Abuja yau Alhamis

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da tawagar masu yaɗa labarai na gwamnatin jihar ta kai masa ziyarar ban-girma a ofishin sa a Abuja yau Alhamis

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce aikin babbar hanyar Sakkwato zuwa Badagiri mai tsawon kilomita dubu zai taimaka wajen bunƙasa noma da buɗe sababbin damar tattalin arziki ga al’ummomi da jihohin da hanyar za ta ratsa, ciki har da Jihar Kebbi.

Idris ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da tawagar masu yaɗa labarai na Gwamnatin Jihar Kebbi, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Alhaji Yakubu Birnin-Kebbi, ta kai masa ziyarar ban-girma.

Ya ce kusan kilomita 250 daga cikin hanyar za ta ratsa ta cikin Kebbi ne, wanda hakan zai bai wa jihar damar ƙara faɗaɗa harkokin noma, kasuwanci da sauran ayyukan tattalin arziki.

Ministan ya ce aikin ba wai hanya ce kawai ta haɗa garuruwa da jihohi ba, domin ana sa ran samar da madatsun ruwa kusan 63 a kan layin hanyar, waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa noma, samar da wutar lantarki da sauran ayyukan tattalin arziki.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da tawagar masu yaɗa labarai na gwamnatin jihar ta kai masa ziyarar ban-girma a ofishin sa a Abuja yau Alhamis

Ya yaba wa gwamnatin Kebbi kan haɗin gwiwar da take yi da Gwamnatin Tarayya a fannonin noma, ababen more rayuwa da tsaro.

Ya ce irin waɗannan manyan ayyukan more rayuwa suna daga cikin ƙoƙarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kai cigaba kusa da jama’a, tare da samar da yanayin da zai bai wa ‘yan kasuwa da al’umma damar bunƙasa.

A cewar sa, yawancin al’ummar Najeriya suna zaune ne a jihohi, ba Abuja ba, don haka ya zama wajibi a kai cigaba inda suke.

A nasa jawabin, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kebbi ya ce tawagar ta je Abuja ne domin gabatar wa ministan da bayanai kan nasarorin da gwamnatin jihar ta samu tare da ƙarfafa alaƙar ta da Gwamnatin Tarayya.

Ya ce Kebbi tana da babbar dama a fannonin noma, ilimi, lafiya, ababen more rayuwa da tsaro, kuma jihar tana so ta ci gaba da haɗa hannu da Gwamnatin Tarayya domin amfani da wannan damar wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Tags: KebbiMohammed Idris
Previous Post

Sojoji sun ceto mutane 23, sun hallaka ’yan ta’adda 19 cikin kwana ɗaya

Next Post

Nijeriya da Amurka sun ƙarfafa haɗin gwiwa don yaƙi da ta’addanci

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Nijeriya da Amurka sun ƙarfafa haɗin gwiwa don yaƙi da ta’addanci

Nijeriya da Amurka sun ƙarfafa haɗin gwiwa don yaƙi da ta'addanci

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!