Rundunar Sojin Nijeriya ta ce dakarun ta sun ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su, tare da hallaka ’yan ta’adda 19 a wasu ayyukan sintiri da samame da suka gudanar a sassan kasar cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
A Jihar Zamfara, dakarun Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 18 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Sabon Gari, karamar hukumar Kaura Namoda, bayan da suka mayar da martani ga kiran neman agaji. Rundunar ta ce ganin sojojin ya tilasta wa ’yan ta’addan tserewa, lamarin da ya ba da damar kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwar da su.
A Jihar Filato, sojoji sun kuma ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi daga Duguri a Jihar Bauchi. A wani samame da Operation ENDURING PEACE ta gudanar, an hallaka wani dan ta’adda tare da kwato bindigar AK-47 da harsasai biyu.
A Jihar Kebbi kuwa, dakarun Operation FANSAN YAMMA sun hallaka ’yan ta’adda 18 yayin da suka kai hari kan jami’an Mobile Police Special Intervention Squad a Makuku, karamar hukumar Sakaba. Sojojin sun kuma lalata babura biyar tare da kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu da aka kera a cikin gida.
A Borno, dakarun Operation HAƊIN KAI sun ceto mutane biyar da suka tsere daga wani sansanin ’yan ta’adda a yankin tsaunukan Mandara, bayan da rikici ya barke tsakanin ’yan ta’addan.
A Enugu kuma, sojoji sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda hudu, magazin guda bakwai da harsasan 7.62mm guda 133 daga wata maɓoyar masu garkuwa da mutane a dajin Umuchingu Ujenike.
A Jihar Taraba, dakarun sun kama mutane 19 da ake zargi da aikata laifuka a karamar hukumar Gashaka. An kuma kwato babura, injinan famfo, wayoyin hannu da kuma kuɗaɗe daga hannun su.
Rundunar Sojin ta ce waɗannan ayyuka wani ɓangare ne na ci gaba da ƙoƙarin ta na amfani da bayanan sirri, sintiri da samame domin daƙile ayyukan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijeriya.







