• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tasiri da manufofin CBN dangane da buɗe rajistar gwajin sabbin fasahohi ga bankuna, kamfanonin fintech da na kirifto

Ashafa Murnai Barkiya by Ashafa Murnai Barkiya
August 13, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Tasiri da manufofin CBN dangane da buɗe rajistar gwajin sabbin fasahohi ga bankuna, kamfanonin fintech da na kirifto
Bankin CBN ya shiga daidaita harkokin sababbin fasahohin musanyar kuɗaɗe (Hoto: New Citizen Hausa)

Bankin CBN ya shiga daidaita harkokin sababbin fasahohin musanyar kuɗaɗe (Hoto: New Citizen Hausa)

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya buɗe rajistar shiga rukuni na biyu na tsarin muhallin gwajin sabbin fasahohi a ranar 12 ga Agusta, 2026.

Shirin ya ƙunshi hanyoyi biyu da aka tsara domin masu ba da sabis na kadarorin dijital (VASPs) da kuma kamfanonin da ke amfani da bayanai wajen samar da ayyukan kuɗi.

Ƙaddamar da sabon rukunin shirin na zuwa ne bayan umarnin zartarwa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar 18 ga Yuli, wanda ya samar da tsarin bai-ɗaya na tsara harkokin kadarorin dijital a Nijeriya.

Cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Daraktar Riƙo ta Sashen Sadarwa, Hajiya Hakama Sidi Ali, wadda aka fitar a ranar Talata, CBN ya gayyaci bankuna, kamfanonin fintech, masu bada sabis na kadarorin dijital (VASPs), cibiyoyin kuɗi da kamfanonin fasaha domin su gwada sabbin hanyoyin samar da ayyukan kuɗi a ƙarƙashin kulawar hukumomin da suka dace.

An buɗe rajistar shiga rukuni na biyu a ranar 12 ga Agusta, kuma za a rufe ta a ranar 31 ga Agusta, lamarin da ya bai wa kamfanonin da suka cancanta ɗan takaitaccen lokaci na gabatar da buƙatun su.

An tsara shirin ne domin bai wa masu ƙirƙire-ƙirƙire damar gwada sabbin kayayyakin hadahadar kuɗi, ayyuka, tsarin kasuwanci da fasahohi a cikin wani yanayi mai takaitaccen iko, tare da bai wa hukumomin sa-ido damar fahimtar haɗurran da ka iya tasowa da kuma damar da sabbin fasahohin ke samarwa.

Hanyoyi biyu ga masu neman shiga

Sabon rukuni na shirin sun ƙunshi manyan hanyoyi guda biyu. Hanya ta farko ita ce ‘Virtual Asset Service Provider’ (VASP), wadda aka tanada domin kamfanonin da ke ƙirƙira ko samar da ayyukan kuɗin dijital, hanyoyin biyan kuɗi da kammala mu’amalolin kuɗi, adana kadarorin dijital, walet da sauran abubuwan more rayuwa na kuɗin dijital.

Hanya ta biyu ita ce ‘Data-Enabled Financial Services’ (Non-VASP), wadda aka tsara domin kamfanonin da ke amfani da amintattun hanyoyin dijital da raba bayanai bisa izni, domin inganta biyan kuɗi, bada rance, sarrafa ƙalubalen da aka iya fuskanta, inganta ayyukan cikin gida da faɗaɗa amfani da ayyukan kuɗi.

CBN ya ce shirin muhallin gwajin sabbin fasahohi zai ba masu ƙirƙire-ƙirƙire da hukumomin da ke sa ido damar yin hulɗa a duk tsawon lokacin gwaji.

Wannan zai taimaka wajen samar da sabbin hanyoyin kuɗi cikin tsari, tare da kare masu amfani da kuma tabbatar da daidaiton tsarin kuɗi.

CBN da Hukumar SEC sun ƙara tsaurara sa ido kan kadarorin dijital:

Ƙaddamar da shirin na zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriya ke ƙoƙarin samar da ƙarin fayyacewar dokoki da iyakokin kulawa kan masana’antar kadarorin dijital da ke saurin bunƙasa.

A ƙarƙashin tsarin da ake samarwa, CBN zai kula da kadarorin dijital da ake amfani da su wajen biyan kuɗi, ciki har da kuɗaɗen kirifto, abubuwan more rayuwa na biyan kuɗi da kammala mu’amala, da kuma ayyukan adana kadarori da walet.

A nata ɓangaren, Hukumar Kula da Kasuwar Hannun Jari ta Nijeriya (SEC) za ta kula da kadarorin dijital, wato waɗanda doka ta ɗauka a matsayin hannun jari ko makamantan su.

CBN ya riga ya fara gwada tsarin sa-ido ta hanyar wani shirin gwaji da ya shafi kuɗaɗen kirifto, inda aka zaɓi wasu kamfanonin fintech ciki har da Flutterwave, Paystack da Juicyway.

Sabon shirin muhallin gwajin sabbin fasahohi ya zo ne domin ya haɗa kai da tsarin ARIP na SEC, wanda ya riga ya karɓi wasu kamfanonin kadarorin dijital domin gwajin ayyukan su a ƙarƙashin kulawar hukumomi.

Hukumar Haraji ta Nijeriya (NRS) da SEC ne ke matsayin mataimakan shugabannin majalisar, yayin da Hukumar Bin Diddigin Safarar Kuɗaɗe (NFIU) da Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa a Fannin Tsaro (ONSA) su ma suke a matsayin mambobi.

An tsara wannan tsarin ne domin rufe giɓin da ke akwai a dokoki, ƙarfafa matakan yaƙi da safarar kuɗaɗen haram, inganta kariyar masu amfani da kuma yaƙi da zamba.

Previous Post

CBN ya sake buɗe damar gwajin sabbin fasahohin hadahadar kuɗi da kadarorin zamani

Next Post

Sojoji sun ceto mutane 23, sun hallaka ’yan ta’adda 19 cikin kwana ɗaya

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Sojoji sun ceto mutane 23, sun hallaka ’yan ta’adda 19 cikin kwana ɗaya

Sojoji sun ceto mutane 23, sun hallaka ’yan ta’adda 19 cikin kwana ɗaya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!