Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, a yau Juma’a ya jagoranci wasu gwamnonin jihohin Nijeriya a wata ziyarar aiki ta duba da tantance Yankin Masana’antu na Glo-Djigbé (GDIZ) da ke birnin Kwatano, Jamhuriyar Benin, a wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnati na bunƙasa masana’antu a Nijeriya.
A yayin ziyarar, tawagar ta saurari bayani kan tsarin yankin masana’antun, ƙarfin samar da kayayyaki da damar zuba jari daga Ministan Yawon Buɗe Ido da Harkokin Kasuwancin Waje na Jamhuriyar Benin mai kula da masana’antu da bunƙasa zuba jari masu zaman kansu, Mista Olushegun Adjadi Bakari.
Tawagar ta kuma zagaya cibiyoyin sarrafa masaku da kayayyakin amfanin gona na yankin, inda ake sarrafa audugar da ake nomawa a cikin ƙasar zuwa zare, yadudduka da tufafin da aka kammala. Haka kuma sun duba masana’antun da ke sarrafa goro da sauran amfanin gona domin kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Shettima ya ce lokaci ya yi da ƙasashen Afirka za su karɓi cikakken iko kan albarkatunsu da kasuwancin duniya ta hanyar amfani da dimbin albarkatun ƙasa da Allah Ya hore wa nahiyar.
Ya jaddada cewa ya zama wajibi ƙasashen Afirka su mayar da hankali wajen ƙara wa albarkatun ƙasa ƙima ta hanyar sarrafa su a cikin gida maimakon fitar da su ba tare da an sarrafa su ba.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da ci gaban masana’antu a kowane yanki na Nijeriya.
Ya tabbatar da cewa muddin Bola Ahmed Tinubu na kan karagar mulkin Nijeriya, babu wani yanki da za a bari a baya a shirin gwamnatin tarayya na farfaɗo da bunƙasa masana’antu.
Ziyarar na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Nijeriya na nazarin nasarorin da wasu ƙasashen Afrika suka samu a fannin masana’antu da kuma binciko hanyoyin ƙarfafa zuba jari, kasuwanci da haɗin gwiwar tattalin arziki da ƙasashe maƙwabta.






