• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Atiku ya biya Ghali Na’Abba Naira miliyan 5 domin su tsige ni, inji Obasanjo; Atiku ya yi raddin cewa har yanzu Obasanjo na jin haushin hana shi yin wa’adi na uku

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
July 24, 2026
in Siyasa
A A
0
Atiku ya biya Ghali Na’Abba Naira miliyan 5 domin su tsige ni, inji Obasanjo; Atiku ya yi raddin cewa har yanzu Obasanjo na jin haushin hana shi yin wa’adi na uku
Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar

Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar

Wani sabon takun-saƙa ya ɓarke tsakanin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar kan zargin wani shirin tsige Obasanjo daga mulki a lokacin gwamnatin sa.

Obasanjo ya yi zargin cewa Atiku ya bai wa marigayi tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na’Abba, Naira miliyan biyar domin ya fara shirin tsige shi daga muƙami a wa’adin sa na farko.

Tsohon shugaban ya yi wannan zargi ne yayin da yake mayar da martani ga kalaman tsohon gwamnan Jihar Ogun, Olusegun Osoba, kan wasu al’amurran siyasa da suka gabaci babban zaɓen shekarar 2003.

A cewar Obasanjo, shirin tsige shi ya samo asali ne daga cikin fadar shugaban ƙasa bayan Atiku ya yi wata ganawar sirri da Na’Abba.

Ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya shawo kan marigayi kakakin cewa ya kamata ya yi wa’adi ɗaya kacal a matsayin shugaban ƙasa, sannan ya ƙarfafa masa gwiwar fara shirin tsige shi.

“Shirin tsige ni da Na’Abba ya fara ya samo asali ne a fadar shugaban ƙasa ta hannun mataimakin shugaban ƙasa, wanda a ranar Juma’a lokacin da ban kasance a ofis ba, ya gayyaci Na’Abba zuwa ofishin sa, ya kuma shawo kan sa kamar yadda ya shawo kan kan sa da wasu kaɗan marasa tasiri cewa ya kamata in yi wa’adi ɗaya kacal a matsayin shugaban ƙasa,” inji Obasanjo.

“A ranar Juma’ar, Atiku ya gayyaci Na’Abba, ya ba shi Naira miliyan biyar domin ya fara aikin tsige ni. An lura da komai, an rubuta komai, sannan babban jami’in ma’aikata na, wanda ƙwararren jami’in leƙen asiri ne, ya kai min rahoto.”

Obasanjo ya ce an rubuta bayanan taron da kuma yadda aka yi cinikin kuɗin, kuma babban jami’in ma’aikatan sa ne ya sanar da shi, wanda ya bayyana a matsayin ƙwararren jami’in leƙen asiri.

Ya ƙara da cewa bai damu da barazanar tsige shi ba saboda ya yi imanin babu wani dalili bisa kundin tsarin mulki da zai ba da damar cire shi daga muƙami.

Raɗaɗin Atiku

Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da babban mataimakin sa na musamman kan hulɗa da jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar a yau Juma’a, Atiku ya soki Obasanjo kan yin wannan zargi bayan rasuwar Na’Abba, yana mai cewa marigayin ba ya raye domin ya kare kan sa.

Ya ce: “A matsayin mu na ’yan Afrika, mun san muhimmancin faɗin gaskiya game da mamata.”

“Saboda haka, abin damuwa ne matuƙa yadda tsohon Shugaba Obasanjo ya zaɓi wannan lokaci don yin zargin cewa na bai wa marigayi Rt. Hon. Ghali Umar Na’Abba cin hanci domin ya tsige shi.

“Idan wannan zargi gaskiya ne, me ya sa bai taɓa bayyana shi ba lokacin da Rt. Hon. Na’Abba yake raye? Me ya sa sai bayan mutuwar mutumin da shi kaɗai zai iya tabbatar ko ƙaryata wannan zargi?

“Ta hanyar jingina wannan babban zargi ga mutumin da ya rasu a matsayin babbar shaida, tsohon Shugaba Obasanjo ya hana ’yan Nijeriya damar jin ɗaya ɓangaren labarin.”

Atiku ya ce zargin bai yi wa tarihin Na’Abba adalci ba domin tsohon kakakin ba zai iya kare mutuncin sa ko mayar da martani ga zargin karɓar cin hanci ba.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi tambayar dalilin da ya sa ba a taɓa ɗaukar wani matakin shari’a a kan sa ba idan da gaske akwai hujjojin da ke tabbatar da zargin.

Ya ce: “Idan har da gaske akwai hujjojin aikata laifi kamar yadda ake zargi, ’yan Nijeriya suna da haƙƙin tambayar dalilin da ya sa gwamnatin da ke da cikakken ikon ƙasa ba ta ɗauki wani mataki ba a lokacin.”

Atiku ya ce lokacin da Obasanjo ya fito da wannan zargi ya nuna cewa manufar sa ita ce ɓata masa suna tare da bai wa ɗan takarar sa fifiko a gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

“A wannan lokaci da siyasar da za ta kai ga babban zaɓen 2027 ke fara ɗaukar salo, a bayyane yake manufar ita ce a ɓata mini suna da mutunci tare da bai wa ɗan’uwan tsohon shugaban ƙasa wata fa’idar siyasa da bai cancanta ba,” inji shi.

“Amma ’yan Nijeriya sun fi haka wayewa. Ba za a iya ruɗar su da tsofaffin zarge-zarge da aka sake tayarwa saboda wata manufa ta siyasa ba.”

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ce ci gaba da ƙin jinin da Obasanjo ke nuna masa ya samo asali ne daga yadda ya yi adawa da yunƙurin wa’adi na uku da tsohon shugaban ya nemi yi.

“Laifi na shi ne na tsaya tsayin daka wajen adawa da yunƙurin wa’adi na uku wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulki. A matsayi na na ɗan dimokiraɗiyya, na zaɓi bin kundin tsarin mulki da doka,” inji shi.

“Maimakon in sadaukar da ƙa’idojin dimokiraɗiyya saboda wata buƙata ta ƙashin kai, na kare kundin tsarin mulki, kuma na samu nasara a kotuna a wasu manyan shari’o’i da na yi da shugaban ƙasa mai ci a lokacin.

“Waɗannan shari’o’in sun zama wani ɓangare na tarihin dimokiraɗiyyar Nijeriya. A bayyane yake cewa har yanzu tsohon Shugaba Obasanjo bai rabu da ɗacin ran da ya samo asali daga wancan lokaci ba.”

Atiku ya ce ba zai bari a shagaltar da shi da rikice-rikicen siyasa na fiye da shekaru 20 da suka gabata ba, alhali ’yan Nijeriya suna fama da tsadar rayuwa, rashin tsaro, rashin aikin yi da kuma ƙaruwa a bashin gwamnati.

“Aikin da ke gaban shugabanni a yau ba wai sake rubuta tarihi ba ne, sai dai ceto makomar ƙasa. ’Yan Nijeriya sun fi son sanin dalilin da ya sa farashin abinci ke ci gaba da tashi, me ya sa bashin gwamnati ke ƙaruwa duk da ƙarin kuɗaɗen shiga, da kuma dalilin da ya sa gwamnatin yanzu ke fuskantar ce-ce-ku-ce iri-iri, fiye da komawa kan saɓanin siyasa na fiye da shekaru ashirin da suka gabata,” inji shi.

Ya ƙara da cewa Obasanjo na da ’yancin goyon bayan duk ɗan takarar da yake so a zaɓen 2027, amma ya kamata ya bayyana hakan a fili maimakon dogaro da zarge-zargen da ba za a iya tantancewa ba saboda babban shaidar ya rasu.

“Idan tsohon Shugaban Ƙasa Obasanjo ya zaɓi ɗaukar wata matsaya ta siyasa gabanin zaɓen 2027, ya kamata kawai ya bayyana ta a fili ya bar ’yan Nijeriya su yi hukunci a kan ta bisa cancantar ta, maimakon ƙoƙarin rinjayar ra’ayin jama’a ta hanyar zarge-zargen da ba za a iya gwada sahihancin su ba saboda babban shaidar ba ya raye,” inji shi.

“Har yanzu hankalin mu na kan gabatar da ingantattun zaɓuɓɓuka, kare dimokiraɗiyya, neman a tsare gaskiya, da kuma haɗa kai da dukkan ’yan Nijeriya masu kishin ƙasa domin dawo da shugabanci nagari, mai gaskiya da kuma mai sanya muradun jama’a a gaba.

“’Yan Nijeriya suna buƙatar mafita ga matsalolin yau, ba wai sake tada tsofaffin tatsuniyoyin siyasa na jiya ba.”

Tags: Atiku AbubakarGhali Umar Na'AbbaOlusegun ObasanjoOlusegun Osobazaɓen 2027
Previous Post

Sojoji sun kama mutum 5 da ake zargi da garkuwa da mutane a Yobe, sun ƙwato bindigogi

Next Post

Shettima ya jagoranci gwamnoni ziyarar duba masana’antu a Jamhuriyar Benin

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko
Siyasa

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu
Siyasa

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

September 10, 2026
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Siyasa

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

September 9, 2026
Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2
Siyasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

September 2, 2026
Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20
Siyasa

Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20

August 26, 2026
Siyasa

Tinubu ya janye jerin sunayen Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC – Rahoto

August 25, 2026
Next Post
Shettima ya jagoranci gwamnoni ziyarar duba masana’antu a Jamhuriyar Benin

Shettima ya jagoranci gwamnoni ziyarar duba masana'antu a Jamhuriyar Benin

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!