• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamna Bago na so Hukumar Raya Arewa ta Tsakiya ta ba matsalolin tsaro da sauyin yanayi fifiko

* Ya ba da shawarar a kira taron gaggawa na gwamnonin yankin

Wakilin Mu by Wakilin Mu
July 25, 2026
in Labarai
A A
0
Gwamna Bago na so Hukumar Raya Arewa ta Tsakiya ta ba matsalolin tsaro da sauyin yanayi fifiko
Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Mohammed Umaru Bago, yana musabaha da shugabannin Hukumar Raya Yankin Arewa ta Tsakiya (NCDC) waɗanda suka kai masa ziyara a Minna jiya Juma'a

Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Mohammed Umaru Bago, yana musabaha da shugabannin Hukumar Raya Yankin Arewa ta Tsakiya (NCDC) waɗanda suka kai masa ziyara a Minna jiya Juma'a

Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Mohammed Umaru Bago, ya buƙaci Hukumar Raya Yankin Arewa ta Tsakiya (NCDC) da ta bai wa matsalolin tsaro, rikice-rikicen manoma da makiyaya, da illolin sauyin yanayi muhimmanci a cikin shirye-shiryen ta na bunƙasa yankin.

Bago ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin Shugaban Hukumar NCDC, Cosmas Akighir, da Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na hukumar, Cyril Tsenyil, tare da sauran membobin ta, a ziyarar girmamawa da suka kai masa ranar Talata a Minna.

Gwamnan ya yaba wa shugabannin sabuwar hukumar kan fara rangadin jihohin Arewa ta Tsakiya da take yi domin gano hanyoyin haɗin gwiwa, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen shimfiɗa tubalin cigaban yankin.

Ya buƙaci hukumar da ta mayar da hankali kan manyan matsalolin da suka addabi yankin, musamman rashin tsaro da rikice-rikicen manoma da makiyaya, waɗanda ke ci gaba da haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

Haka kuma ya ba da shawarar a kira taron gaggawa na gwamnonin jihohin yankin domin tattauna ƙalubalen cigaban yankin tare da tsara alƙiblar ayyukan hukumar.

A cewar sa, irin wannan taro zai taimaka wa hukumar wajen tsara shirye-shiryen da suka dace da ainihin buƙatun al’ummar yankin.

Da yake magana kan sauyin yanayi, gwamnan ya bayyana cewa ambaliyar ruwa da ke biyo bayan cikar madatsun ruwan lantarki guda huɗu da ke Jihar Neja tana ci gaba da lalata al’ummomi, gonaki da muhimman kayayyakin more rayuwa a duk shekara.

Ya ce wannan ne ya sa jihar ke neman Gwamnatin Tarayya da ta ba ta kashi 13 cikin ɗari na kuɗaɗen shiga daga albarkatun man fetur a matsayin diyya saboda ɗaukar nauyin madatsun ruwa da ke samar da wani kaso mai yawa na wutar lantarkin Nijeriya.

Bago ya kuma buƙaci NCDC da ta zuba jari sosai a ɓangarorin noma da ilimi, yana mai cewa su ne ginshiƙan cigaba mai ɗorewa, bunƙasar tattalin arziki da tabbatar da zaman lafiya.

Ya tabbatar wa da hukumar cewa gwamnatin Jihar Neja za ta ci gaba da ba ta cikakken goyon baya, ciki har da samar da ofishin hulɗa da sauran abubuwan da za su sauƙaƙa mata wajen gudanar da ayyukan ta.

A nasa jawabin, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na NCDC, Cyril Tsenyil, ya ce ziyarar wani ɓangare ne na ƙoƙarin hukumar na ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohin Arewa ta Tsakiya tare da gano muhimman buƙatun cigaban yankin.

Ya bayyana Neja a matsayin jiha mai matuƙar muhimmanci saboda albarkatun noma, ma’adinai da makamashi da take da su, waɗanda ke da tasiri sosai ga tattalin arzikin yankin da Nijeriya baki ɗaya.

Tsenyil ya ce hukumar, wadda aka kafa ƙarƙashin manufar Ajandar Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda) ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, za ta yi aiki tare da gwamnatocin jihohi wajen aiwatar da shirye-shiryen cigaba a ɓangarorin sufuri, lafiya, ilimi, noma, albarkatun ruwa, wutar lantarki, masana’antu da sadarwa.

Ya ƙara da cewa hukumar na tsara hanyoyin jawo jarin masu zaman kan su zuwa muhimman ɓangarorin tattalin arzikin yankin.

Haka kuma, ya bayyana aniyar hukumar ta haɗa kai da gwamnatin Jihar Neja wajen bunƙasa noma, ban-ruwa, hanyoyin karkara, sarrafa amfanin gona, makamashi da masana’antu.

Tsenyil ya kuma jajanta wa gwamnatin jihar kan asarar rayuka da dukiyoyin da hare-haren ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro suka haifar, tare da tabbatar da cewa NCDC za ta yi aiki tare da masu ruwa da tsaki wajen tallafa wa zaman lafiya, farfaɗo da al’ummomin da abin ya shafa da kuma bunƙasa cigaban Arewa ta Tsakiya.

Shi ma Shugaban hukumar NCDC, Cosmas Akighir, ya ce ziyarar ta kasance ne domin gabatar da sababbin shugabannin hukumar ga jihohin yankin da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar da za ta taimaka wajen cimma manufofin da aka kafa hukumar domin aiwatarwa.

Ya yaba wa Gwamna Bago kan nasarorin da ya samu a ɓangarorin noma, gine-ginen more rayuwa da shugabanci, tare da jaddada ƙudirin hukumar na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin Jihar Neja domin bunƙasa ɗimbin damar cigaban da jihar ke da su.

Tags: Gwamna Mohammed Umaru BagoNCDCNejaziyara
Previous Post

Shettima ya jagoranci gwamnoni ziyarar duba masana’antu a Jamhuriyar Benin

Next Post

Gwamna Bago ya gana da ‘yan takarar APC da waɗanda suka faɗi zaɓen fidda gwani a Neja

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Gwamna Bago ya gana da ‘yan takarar APC da waɗanda suka faɗi zaɓen fidda gwani a Neja

Gwamna Bago ya gana da 'yan takarar APC da waɗanda suka faɗi zaɓen fidda gwani a Neja

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!