• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Ƙungiyar Boko Haram ta fitar da bidiyon ta’aziyyar mai ɗaukar mata hoto da sojoji suka bindige

ALI KANO by ALI KANO
July 22, 2026
in Tsaro
A A
0
Ƙungiyar Boko Haram ta fitar da bidiyon ta’aziyyar mai ɗaukar mata hoto da sojoji suka bindige
Mariganyi Abu Salim al-Barnawi a bakin aiki

Mariganyi Abu Salim al-Barnawi a bakin aiki

Ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta fitar da wani bidiyon ta’aziyya ga ɗaya daga cikin masu ɗaukar bidiyo da hotunan ta, mai suna Abu Salim al-Barnawi, wanda dakarun sojin Nijeriya suka kashe yayin wani hari da ya ci tura kan wani sansanin soji.

Bidiyon, mai tsawon mintuna uku da daƙiƙa uku, wanda wakilin mu ya samu a ranar Laraba, an yi shi ne da harshen Larabci, kuma ya nuna Abu Salim al-Barnawi yana ɗaukar bidiyon hare-haren Boko Haram tare da shiga ayyukan ƙungiyar.

Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa-maso+Gabas, Operation Haɗin Kai, Kyaftin Muhammed Goni, wanda ya wallafa bidiyon, ya ce mamacin ya taba jagorantar hare-hare a ƙasar Kamaru kafin daga bisani ya koma sashen yaɗa labarai na ƙungiyar.

Abu Salim al-Barnawi cikin shirin faɗa

Rubutun da aka haɗa da bidiyon ya ce: “‘Yan ta’addan Boko Haram sun fitar da ta’aziyya kan jagoran kai hari kuma mai ɗaukar hoton bidiyo, Abu Salim al-Barnawi.”

An kuma ƙara da cewa:“An kashe shi a makon da ya gabata a hannun sojojin Nijeriya lokacin da ƙungiyar ta’addanci ta kai hari kan sansanin sojojin Nijeriya. Shi ne mai ɗaukar hoto da bidiyo na ƙungiyar. A baya ya jagoranci hare-hare zuwa ƙasar Kamaru kafin daga bisani ya shiga sashen yaɗa labarai na ƙungiyar ta’addancin..”

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da dakarun Operation Haɗin Kai suka bayyana kashe wani da ake zargin mai ɗaukar bidiyo ne na Islamic State West Africa Province (ISWAP) a lokacin da ‘yan ta’addan suka yi yunƙurin kutsawa yankin Cross Kauwa da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno, amma harin ya ci tura.

A cewar Kyaftin Goni, ‘yan ta’addan sun yi ƙoƙarin amfani da duhun dare domin mamaye sansanin sojoji tare da kwashe kayayyakin maganin cutar kwalara, amma dakarun sojin suka fatattake su.

Ya ce a yayin aikin an ƙwato kyamarar bidiyo ta Sony, harsasai masu yawa na PKT da 7.62mm Special, kayan sanye na ‘yan ta’adda da sauran kayayyakin yaƙi.

Abu Salim al-Barnawi tare da wani abokin ta’addancin shi

Goni ya kuma bayyana cewa bidiyoyin da aka ƙwato a yayin aikin sun nuna akwai wasu baƙi uku da ke taimaka wa ƙungiyar ta’addancin, ciki har da wani Bafalasɗine da ake bayyana a matsayin mai horaswa, da kuma wani ɗan ƙasar Morokko da ke aiki a matsayin likitan ƙungiyar a Jihar Borno.

Tags: Abu Salim al-BarnawiBoko Haramsojojita'addancita'aziyya
Previous Post

‘Yan Majalisar Wakilai sun karɓi rahoton gyaran kundin tsarin mulki kan dokar kafa ‘yan sandan jihohi

Next Post

Gwamna Mohammed Umaru Bago: Maraba da Bayyanar Sabon Tauraron Arewa

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Gwamna Mohammed Umaru Bago: Maraba da Bayyanar Sabon Tauraron Arewa

Gwamna Mohammed Umaru Bago: Maraba da Bayyanar Sabon Tauraron Arewa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!