Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Olayemi Cardoso, tare da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Harkokin Bankuna, Inshora da sauran Hukumomin Kuɗi, Sanata Mukhail Adetokunbo Abiru, lokacin da ya gabatar da rahoton CBN na watannin shidan farkon shekarar 2026, a majalisar a ranar Laraba
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Olayemi Cardoso, ya gabatar wa Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Harkokin Bankuna, Inshora da sauran Hukumomin Kuɗi rahoton CBN na watannin shidan farkon shekarar 2026, wato daga watan Janairu zuwa Yuni.
A cikin bayanin wanda Cardoso ya gabatar a jiya Laraba, yayin gabatar da rahoton, Cardoso ya bayyana manyan nasarorin da CBN ya samu a watanni shida na farkon shekarar 2026. Ya ce an samu ci gaba wajen rage hauhawar farashin kayayyaki, tabbatar da daidaiton kasuwar musayar kuɗaɗen ƙasashen waje, ƙara yawan ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje, ƙarfafa juriyar ɓangaren bankuna, da aiwatar da sauye-sauye a tsarin kasuwannin kuɗi.

Ya kuma bayyana nasarar kammala shirin ƙarawa da ƙarfafa yawan jarin bankuna a matsayin babban ci gaba da ya ƙara wa bankunan Nijeriya ƙarfi, ƙarfin gudanarwa da kuma gasa a matakin cikin gida da na ƙasa da ƙasa.
Da yake duba kan abin da aka sa gaba kuwa, Cardoso ya sake jaddada aniyar CBN na ci gaba da dawo da daidaiton farashin kayayyaki tare da cimma manufar rage hauhawar farashin kaya zuwa adadi mai mafi ƙanƙanta, wato da lamba ɗaya, a cikin matsakaicin lokaci. Ya ce za a cimma hakan ne ta hanyar manufofin kuɗi da suka dogara da hujjoji da kuma inganta yadda manufofin ke aiki.
Ya kuma bayyana manyan abubuwan da CBN zai mayar da hankali a kan su a cikin sauran watanni shidan shekarar 2026, wato daga watan Yuli zuwa Disamba.
Waɗannan, kamar yadda Cardoso ya fayyace, sun haɗa da sa-ido kan bankuna bayan kammala shirin ƙara jarin su, ci gaba da gyaran kasuwar musayar kuɗaɗen ƙasashen waje, aiwatar da manufofin rage hauhawar farashin kayayyaki, aiwatar da shirin PSV 2028, ƙarfafa tsaron yanar gizo hadahadar kuɗaɗe ta yanar gizo, da kuma tabbatar da ɗorewar karsashi da tabbataccen daidaiton tsarin kuɗi na ƙasa wanda ba ya fuskantar barazana, wato mai jure ƙanana da manyan ƙalubale.

Cardoso ya bayyana ƙwarin gwiwar sa game da makomar tattalin arzikin Nijeriya, yana mai cewa CBN zai ci gaba da yanke hukunci bisa hujjoji da kuma bin dokar da ta kafa bankin, tare da fifita muradun al’ummar Nijeriya na dogon lokaci.
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Bankuna, Inshora da sauran Hukumomin Kuɗi, Sanata Mukhail Adetokunbo Abiru, ya yaba wa CBN kan ƙoƙarin da yake yi wajen tabbatar da daidaito a kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje, inganta wadatar kuɗi a kasuwa da kuma rage tangarɗar da ta daɗe tana addabar kasuwar.







