• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Idris ya buƙaci masu rubutu a gidan yana da masu ƙirƙirar abubuwan intanet su rungumi aikin jarida cikin ɗa’a

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
July 21, 2026
in Labarai
A A
0
Idris ya buƙaci masu rubutu a gidan yana da masu ƙirƙirar abubuwan intanet su rungumi aikin jarida cikin ɗa’a
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da mahalartan Taron Masu Rubutun Gidan Yana, Masu Wallafa Labarai a Intanet da Masu Ƙirƙirar Abubuwan Intanet na Jihar Neja da aka gudanar a ranar Litinin a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da mahalartan Taron Masu Rubutun Gidan Yana, Masu Wallafa Labarai a Intanet da Masu Ƙirƙirar Abubuwan Intanet na Jihar Neja da aka gudanar a ranar Litinin a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci masu rubutu a gidan yana, da masu ƙirƙirar abubuwan da ake wallafawa a intanet, da kuma masu tasiri a soshiyal midiya da su rungumi aikin jarida cikin ɗa’a, ta hanyar bayar da labarai cikin gaskiya, yayin da suke gina ra’ayin jama’a a wannan zamani na fasahar dijital.

Da yake jawabi a wajen Taron Masu Rubutun Gidan Yana, Masu Wallafa Labarai a Intanet da Masu Ƙirƙirar Abubuwan Intanet na Jihar Neja da aka gudanar a ranar Litinin a Abuja, ministan ya ce dandamalin dijital yana samar da damarmaki masu tarin yawa wajen ƙirƙire-ƙirƙire da kuma ƙarfafa shigar da jama’ar ƙasa a al’amurran yau da kullum.

Sai dai ya jaddada cewa dole ne a yi amfani da su yadda ya dace domin bunƙasa tsare gaskiya, haɗin kan ƙasa da kuma tattaunawa mai amfani ga jama’a.

Ministan ya ce: “Babu wani tsarin dimokiraɗiyya da zai bunƙasa ba tare da kafafen yaɗa labarai da suka san ya-kamata ba. Ba za ku iya ɗaukar ‘yancin faɗar albarkacin baki ba sannan ku yi watsi da nauyin da ke tattare da shi.”

Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana ci gaba da jajircewa wajen kare ‘yancin kafafen yaɗa labarai tare da ƙarfafa aikin jarida mai ɗa’a.

Idris ya buƙaci masu rubutun intanet da masu ƙirƙirar abubuwan gidan yana da su tabbatar da sahihancin bayanai kafin su wallafa, su guji yaɗa labaran ƙarya da na yaudara, sannan su yi amfani da dandamalin su wajen ilmantarwa, zaburarwa da kuma inganta cigaban ƙasa.

Ya kuma buƙaci matasan Nijeriya da su ɗauki ƙirƙirar abubuwan da ake wallafawa a intanet ba kawai a matsayin hanyar samun kuɗin shiga ba, har ma a matsayin wata hanya ta shiga cikin harkokin al’umma da gina ƙasa.

Ya jaddada cewa sadarwa mai ɗa’a tana da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da kuma haɓaka amincewar jama’a.

Haka zalika, ministan ya yi tsokaci kan kafa Cibiyar Ilimin Kafafen Yaɗa Labarai da Bayanai ta Ƙasa da Ƙasa (IMILI), wadda ita ce cibiyar farko ta UNESCO ta rukuni na biyu a duniya da aka keɓe gaba ɗaya domin ilimin kafafen yaɗa labarai da bayanai.

Ya bayyana hakan a matsayin wani babban mataki na bunƙasa ilimin dijital da amfani da intanet yadda ya kamata.

Daga ƙarshe, ya buƙaci masu sha’awar rubutun gidan yana da ‘yan kasuwar intanet da su ci gaba da bunƙasa ƙwarewar su, tare da kiyaye ƙa’idojin aiki da za su ƙara inganta sahihanci da amincin kafafen yaɗa labarai na intanet a Nijeriya.

Tags: 'yan jaridaintanetMohammed IdrisNejasoshiyal midiyataro
Previous Post

Gwamnati Tarayya ta musanta karɓar sabon bashin tiriliyan ₦80 cikin shekaru uku

Next Post

CBN ya sake jaddada aniyar sa ta tabbatar da daidaiton farashi, ya ce tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da bunƙasa

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
CBN ya sake jaddada aniyar sa ta tabbatar da daidaiton farashi, ya ce tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da bunƙasa

CBN ya sake jaddada aniyar sa ta tabbatar da daidaiton farashi, ya ce tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da bunƙasa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!