• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya sake jaddada aniyar sa ta tabbatar da daidaiton farashi, ya ce tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da bunƙasa

ALI KANO by ALI KANO
July 21, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
CBN ya sake jaddada aniyar sa ta tabbatar da daidaiton farashi, ya ce tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da bunƙasa
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, yana jawabi a wurin kammala taron Kwamitin Manufofin Kuɗi (MPC) karo na 306 a Abuja a yau

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, yana jawabi a wurin kammala taron Kwamitin Manufofin Kuɗi (MPC) karo na 306 a Abuja a yau

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Olayemi Cardoso, ya sake jaddada ƙudirin bankin na tabbatar da daidaiton tattalin arziki ta hanyar aiwatar da manufofin kuɗi masu haɗin kai da suka dogara da bayanai, yana mai cewa tattalin arzikin Nijeriya yana ci gaba da kasancewa mai ɗorewa duk da rashin tabbas da ake fuskanta a tattalin arzikin duniya.

Cardoso ya bayyana hakan a ranar Talata yayin kammala taron Kwamitin Manufofin Kuɗi (MPC) karo na 306, inda kwamitin ya yi nazari kan halin tattalin arzikin cikin gida da na duniya tare da sake jaddada aniyar sa ta tabbatar da daidaiton farashi da kuma kare tsarin kuɗi na ƙasar nan.

A cewar sa, ana hasashen tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da samun ƙwarin bunƙasa a shekarar 2026, sakamakon ƙaruwa a yawan hako ɗanyen mai, ingantattun alƙaluman Purchasing Managers’ Index (PMI) da kuma tasirin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu take aiwatarwa.

Ya ce Kwamitin Manufofin Kuɗi yana ci gaba da kasancewa a shirye domin ɗaukar matakan manufofin kuɗi da suka dace don rage hauhawar farashin kayayyaki tare da mayar da shi zuwa kaso guda ɗaya cikin matsakaicin lokaci.

Game da harkar bankuna, Cardoso ya yaba da nasarar da aka samu wajen kammala shirin ƙara jarin bankuna, yana mai cewa hakan babban mataki ne na ƙarfafa tsarin kuɗi na Nijeriya.

Ya kuma tabbatar da cewa tsarin bankunan ƙasar nan yana ci gaba da kasancewa lafiya, mai ƙarfi kuma abin dogaro.

Ya bayyana cewa matakin da CBN ya ɗauka kwanan nan kan bankunan ƙananan kuɗi (Microfinance Banks) guda 46 ya zama dole ne domin magance take dokoki da rashin bin ƙa’idojin da suka daɗe suna faruwa.

Ya ce, “Kare kuɗaɗen masu ajiya shi ne babban abin da CBN ya fi bai wa muhimmanci.”

Gwamnan ya sake jaddada ƙudirin babban bankin na tabbatar da tsarin musayar kuɗaɗen waje mai gaskiya, mai wadataccen kasuwa kuma wanda ya dogara da ƙa’idar mai saye da mai sayarwa cikin yardar juna.

Ya ce sauyin darajar naira zai ci gaba da kasancewa bisa yanayin kasuwa, yayin da sauye-sauyen da ake aiwatarwa za su ƙara wa masu zuba jari ƙwarin gwiwa, su inganta gasa tare da ƙarfafa daidaiton tattalin arziki na dogon lokaci.

Cardoso ya yi tsokaci kan ƙaddamar da Nigeria Overnight Financing Rate (NOFR), yana mai bayyana shi a matsayin wani muhimmin cigaba da zai ƙara tsare gaskiya a tsarin kuɗi.

A cewar sa, sabon ma’aunin yana nuna ainihin mu’amalolin ba da rancen kuɗi na dare tsakanin bankuna masu cikakken kariya, kuma zai taimaka wa Monetary Policy Rate (MPR) wajen inganta isar da manufofin kuɗi da kuma tallafa wa tsarin rage hauhawar farashin kayayyaki.

Da yake magana kan ci gaban tsarin biyan kuɗi a ƙasar, Cardoso ya bayyana cewa takardar kuɗin naira ta ₦100 ta tunawa, da ta ₦100 ta yau da kullum, da kuma dukkan takardun kuɗin naira da CBN ya amince da su, har yanzu suna da cikakken matsayi na kuɗin doka.

Ya ƙara da cewa makomar tsarin biyan kuɗi tana ƙara karkata zuwa fasahar zamani, yana mai jaddada cewa CBN na ci gaba da ƙoƙarin gina tsarin biyan kuɗi na zamani, mai tsaro, wanda kowa zai iya amfani da shi kuma ya dace da ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.

Cardoso ya kuma bayyana farin ciki kan nasarar da CBN ya samu ta lashe Kyautar Babban Bankin Ƙasa ta 2026, yana mai cewa wannan karramawa shaida ce ta ƙwazo, ƙwarewa da jajircewar ma’aikata da shugabannin bankin.

Ya yaba wa kafafen yaɗa labarai na Nijeriya bisa goyon bayan da suke bai wa CBN, yana mai cewa wannan lambar yabo ta sake nuna irin nauyin da ke kan babban banki, kasancewar shawarwarin da yake yankewa suna shafar rayuwar miliyoyin ‘yan Nijeriya.

Gwamnan ya ƙara da cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da ake aiwatarwa a Nijeriya suna ci gaba da samun karɓuwa da yabon ƙasashen duniya, saboda suna ƙarfafa daidaiton tattalin arziki, suna ƙara wa masu zuba jari ƙwarin gwiwa tare da shimfiɗa tubalin bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa.

Tags: CBNfarashikwamitiMista Olayemi Cardoso
Previous Post

Idris ya buƙaci masu rubutu a gidan yana da masu ƙirƙirar abubuwan intanet su rungumi aikin jarida cikin ɗa’a

Next Post

Gwamnatin Ebonyi za ta ƙayyade kuɗin haya, kuɗin dillalai da kasuwancin tarkacen ƙarafa

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Gwamnatin Ebonyi za ta ƙayyade kuɗin haya, kuɗin dillalai da kasuwancin tarkacen ƙarafa

Gwamnatin Ebonyi za ta ƙayyade kuɗin haya, kuɗin dillalai da kasuwancin tarkacen ƙarafa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!