• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gwamnati Tarayya ta musanta karɓar sabon bashin tiriliyan ₦80 cikin shekaru uku

Wakilin Mu by Wakilin Mu
July 21, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
An Bayyana Waɗanda Ba Za Su Biya Haraji Ba A Nijeriya
Mista Taiwo Oyedele, Ministan Kuɗi

Mista Taiwo Oyedele, Ministan Kuɗi

Gwamnatin Tarayya ta musanta rahotannin da ke yawo cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta karɓi sabon bashi har tiriliyan ₦80 cikin shekaru uku, tana mai cewa adadin da ake yaɗawa ya samo asali ne daga kuskuren fahimtar yadda ake ƙididdige bashin ƙasa.

Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki na Ƙasa, Taiwo Oyedele, shi ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da bayani gaban Kwamitin Kuɗi na Majalisar Dattawa.

Oyedele ya ce mutane da dama suna kwatanta adadin bashin da gwamnatin Tinubu ta gada lokacin da ta hau mulki da wanda ake da shi a halin yanzu, sannan su ɗauka cewa duk bambancin da aka samu sabon bashi ne.

Ya ce a zahiri akwai manyan dalilai guda biyu da suka sa adadin bashin ya ƙaru a bayanan hukuma ba tare da hakan na nufin an karɓi sabon bashi ba.

A cewar sa, dalili na farko shi ne sake ƙididdige bashin ƙasashen waje bayan sauyin darajar naira. Ya bayyana cewa tun da ana bayyana bashin Najeriya da kuɗin naira, faɗuwar darajar kuɗin ƙasar ta sa ƙimar bashin ƙetare ta ƙaru da sama da tiriliyan ₦40 a cikin bayanan hukuma.

“Ba sabon bashi aka karɓa ba, ƙimar bashin da ake bin ƙasar ce kawai ta sauya sakamakon canjin darajar naira,” inji shi.

Ministan ya ce dalili na biyu shi ne bashin Ways and Means da gwamnatin da ta gabata ta karɓa daga Babban Bankin Nijeriya (CBN), wanda daga baya Majalisar Dokoki ta amince a mayar da shi cikin bashin gwamnati na hukuma.

Ya ce wannan mataki ya ƙara kusan tiriliyan ₦33 a cikin bayanan bashin ƙasa, amma ya jaddada cewa ba sabon bashi ba ne, domin bashin ya riga ya wanzu kafin gwamnatin Tinubu ta hau mulki.

Oyedele ya kuma bayyana cewa wani kaso mai yawa na bashin cikin gida da gwamnati ke karɓa a halin yanzu na sake fasalin tsofaffin basussuka ne (refinancing), inda gwamnati ke karɓar sabon bashi domin biyan tsohon da ya kai lokacin biya.

Ya ce irin wannan tsari ba yana nufin an ƙara sabon nauyin bashi ba.

Ministan ya ƙara da cewa bashin da gwamnatin Tinubu ke karɓa ana amfani da shi ne wajen aiwatar da manyan ayyukan ci gaban ƙasa da samar da ababen more rayuwa, tare da tabbatar da ɗorewar bashin Nijeriya domin kada ya zama nauyi ga tattalin arzikin ƙasa.

Saboda haka, Gwamnatin Tarayya ta ce ba daidai ba ne a ce ta karɓi sabon bashi har tiriliyan ₦80 cikin shekaru uku, tana mai cewa ƙarin da aka gani a bayanan bashin ya samo asali ne daga sauyin darajar naira, shigar da bashin Ways and Means cikin bayanan hukuma da kuma sake fasalin tsofaffin basussuka.

Tags: bashiShugaba Bola Ahmed TinubuTaiwo Oyedele
Previous Post

Gaskiyar yadda Abacha ya rasu, cewar tsohon jami’in DSS

Next Post

Idris ya buƙaci masu rubutu a gidan yana da masu ƙirƙirar abubuwan intanet su rungumi aikin jarida cikin ɗa’a

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Idris ya buƙaci masu rubutu a gidan yana da masu ƙirƙirar abubuwan intanet su rungumi aikin jarida cikin ɗa’a

Idris ya buƙaci masu rubutu a gidan yana da masu ƙirƙirar abubuwan intanet su rungumi aikin jarida cikin ɗa'a

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!