• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Cewar Shettima: Noman alfafa a Jigawa zai taimaka wajen kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya

Wakilin Mu by Wakilin Mu
July 16, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Cewar Shettima: Noman alfafa a Jigawa zai taimaka wajen kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, yana jawabi a taron Tattalin Arziki da Zuba Jari na Jihar Jigawa (J-Invest 2026), wanda aka gudanar a birnin Dutse ranar Laraba

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, yana jawabi a taron Tattalin Arziki da Zuba Jari na Jihar Jigawa (J-Invest 2026), wanda aka gudanar a birnin Dutse ranar Laraba

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa aikin noman ciyawar Premium Alfalfa wadda kamfanin Jigawa El-Meena Farms (JEFs) ke aiwatarwa a Jihar Jigawa na iya zama mafita mai ɗorewa ga rikicin manoma da makiyaya a Nijeriya.

Shettima ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci rumfar baje kolin kamfanin a taron Tattalin Arziki da Zuba Jari na Jihar Jigawa (J-Invest 2026), wanda aka gudanar a birnin Dutse.

Wani sashe na mahalartan taron

Ya ce samar da ciyawar alfafa a babban sikeli zai tabbatar da wadataccen abincin dabbobi, rage dogaro da kiwon dabbobi a fili, tare da inganta tsarin kiwo na zamani a faɗin ƙasar.

“Tare da wannan gagarumin aikin noman ciyawar alfafa mai inganci da kamfanin Jigawa El-Meena Farms ke gudanarwa, rikicin manoma da makiyaya zai iya zama tarihi,” inji Mataimakin Shugaban Ƙasar.

Ya ƙara da cewa irin wannan zuba jari zai taimaka wajen bunƙasa samar da abinci, ƙarfafa zaman lafiya, da kuma haɓaka tattalin arzikin ƙasa.

Masana sun bayyana cewa wadataccen abincin dabbobi mai inganci zai ƙarfafa tsarin kiwon dabbobi na zamani, tare da rage matsin lamba kan filayen noma da albarkatun ruwa, waɗanda galibi ke haddasa rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya.

A cewar su, aikin noman alfafa yana da muhimmiyar rawa wajen inganta harkokin kiwo, ƙara yawan amfanin dabbobi da kuma samar da zaman lafiya tsakanin al’ummomin manoma da makiyaya.

Kamfanin Jigawa El-Meena Farms yana da burin samar da ciyawar alfafa domin biyan buƙatun masana’antun sarrafa madara da masu kiwon dabbobi, tare da mayar da Jihar Jigawa cibiyar samar da abincin dabbobi da fitar da shi zuwa ƙasashen Yammacin Afrika.

Taron J-Invest 2026 ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, masu zuba jari, abokan hulɗar ci gaba da shugabannin kasuwanci, inda aka baje kolin damarmakin zuba jari a fannoni daban-daban na tattalin arziki.

Har ila yau, Shettima ya jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na samar da kyakkyawan yanayi ga masu zuba jari tare da tallafa wa ayyukan da za su bunƙasa samar da abinci, samar da ayyukan yi da kuma ci gaban tattalin arzikin Nijeriya.

Shettima tare da sauran manyan baƙi a wurin taron
Tags: alfafabajekoliJigawaKashim Shettimanoma
Previous Post

EFCC ta ƙwace jami’a, gidan rediyo da wasu kadarori 46 na tsohon Minista Abubakar Malami

Next Post

2027: Tinubu zai yi nasara da gagarumin rinjaye, inji Minista

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
2027: Tinubu zai yi nasara da gagarumin rinjaye, inji Minista

2027: Tinubu zai yi nasara da gagarumin rinjaye, inji Minista

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!