• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

EFCC ta ƙwace jami’a, gidan rediyo da wasu kadarori 46 na tsohon Minista Abubakar Malami

ALI KANO by ALI KANO
July 15, 2026
in Labarai
A A
0
EFCC ta ƙwace jami’a, gidan rediyo da wasu kadarori 46 na tsohon Minista Abubakar Malami
Wasu rukunan gidaje na Abubakar Malami da kotu ta ƙwace a yau

Wasu rukunan gidaje na Abubakar Malami da kotu ta ƙwace a yau

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta samu umurnin kotu na ƙwace kadarori 48 da mallakar tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, har abada ga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya.

A yau Laraba, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa EFCC ta tabbatar da cewa kadarorin ana zargin an mallake su ne da kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya, kuma ba a samu hujjar cewa an saye su ne daga halastattun hanyoyin samun kuɗi ba.

Daga cikin kadarorin da kotun ta ba da umurnin ƙwacewa akwai Jami’ar Rayhaan da ke Jihar Kebbi, wadda ta haɗa da harabar ta ta dindindin, harabar wucin-gadi, haraba ta uku, gidan Mataimakin Shugaban Jami’ar da kuma gidan rediyon Rayhaan Radio da ke kan titin Sani Abacha Bypass a Birnin Kebbi.

Sauran kadarorin da aka ƙwace sun haɗa da katafaren gida mai hawa biyu da ke Amazon Street, Maitama, Abuja; da wani babban gini mai hawa uku a Area 11, Garki, Abuja, wanda a da ake kira Harmonia Hotels Limited; da otal ɗin Meethaq Hotels da ke Jabi mai ɗakuna 53; da wani ginin gidaje a Asokoro; da otal ɗin Meethaq da ke Maitama mai ɗakuna 15; da wani fili a titin Yakubu Gowon Crescent, da ke unguwar Asokoro a Abuja.

Jami’ar Rayhann da kotu ta ƙwace a yau

Har ila yau, an ƙwace shaguna da gine-ginen kasuwanci a Abuja da Kano, wani katafaren filaza kusa da kasuwar Birnin Kebbi, da filaye biyu masu girman hekta 100-100 a kan hanyar Birnin Kebbi zuwa Jega, da wasu gidaje da shaguna a Abuja, Kaduna da Birnin Kebbi.

Sauran kadarorin sun haɗa da gidaje da shaguna a Gesse Phase II da ke Birnin Kebbi, Vegas Mall da ke Wuse Market a Abuja, gidaje a BUA Estate, EFAB Estate, Karsana da Apo Legislative Quarters, tare da kadarorin Khadimiyya for Justice & Development Initiative da suka haɗa da gidaje 12 da fili mai girman hekta 5.4 a Academic Garden City da ke Birnin Kebbi.

Kotun ta kuma ba da umurnin ƙwace masana’antar Rayhaan Agro Allied Factory da ke Kebbi tare da gine-ginen ta, injuna, kayan masana’anta, masallaci, gidajen ma’aikata da Rayhaan Bustan Building.

Haka kuma an ƙwace kadarorin Azbir Arena da suka haɗa da Azbir Hotel, gidan buga takardu, gallery, lambuna, masallaci, Azbir Clothing da Azbir Pharmacy and Supermarket.

Sauran kadarorin da aka ƙwace sun haɗa da Al-Afiya Energy Tanker Garage, Rayhaan Security House, wani gini mai hawa biyu da ba a kammala ba kusa da Babbar Tashar Mota a Birnin Kebbi, ginin gidan mai na Amasdul Oil and Gas Ltd., da kuma kadarorin Zeennoor Hotel mai ɗakuna 131, Zeennoor Mosque da tsohon ginin Zeennoor Hotel da ke Kabuga Satellite Town a Kano.

Idan an tuna, a ranar 6 ga Janairu, 2026 ce Mai Shari’a Emeka Nwite ya ba da umurnin ƙwace kadarorin na wucin-gadi bayan ƙarar da lauyan EFCC, Ekele Iheanacho, SAN, ya shigar ba tare da sanar da waɗanda abin ya shafa ba.

Bayan samun wannan umurni, EFCC ta wallafa sanarwar ƙwacewar a jaridun ƙasa kamar yadda kotu ta umurta, inda ta gayyaci duk wani da’awar mallakar kadarorin da ya fito ya gabatar da hujjojin da za su hana a ƙwace su har abada ga Gwamnatin Tarayya.

Daga bisani, hukumar ta shigar da buƙatar neman a mayar da ƙwacewar ta zama ta dindindin.

Sai dai Malami tare da wasu mutum 14, waɗanda galibin su ‘yan’uwan sa da abokan hulɗar sa ne, sun shigar da ƙorafe-ƙorafe suna neman kotun ta soke umurnin ƙwacewar wucingadi, tare da ƙalubalantar ikon kotun na bayar da irin wannan umurni da kuma roƙon ta da kada ta amince da ƙwacewar ta ƙarshe.

An saurari shari’ar a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik a ranar 27 ga Mayu, 2026, kafin daga bisani ta ɗage hukunci.

A hukuncin da ta yanke a yau Laraba, kotun ta ce EFCC ta gabatar da isassun hujjoji da suka nuna cewa akwai kyakkyawan dalilin zargin cewa an mallaki kadarorin 48 ne da kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya.

Wani kamfanin ɗab’i na Abubakar Malami da kotu ta ƙwace a yau

Kotun ta kuma ce waɗanda ake ƙara sun gaza sauke nauyin hujjar da doka ta ɗora musu domin sun kasa nuna sahihan hanyoyin da suka samu kuɗaɗen da aka yi amfani da su wajen sayen kadarorin.

Mai shari’ar ta ƙara da cewa bayyana kai tsaye cewa mutum shi ne mamallakin kadara ba tare da gabatar da hujjar yadda aka samo kuɗin sayen ta daga halastattun hanyoyi ba, bai wadatar ba a shari’o’in ƙwace kadara ba tare da hukuncin laifi ba.

Tags: Abubakar Malamicin hanciMai Shari’a Joyce Abdulmaliksataƙwace kadara
Previous Post

Gwamnatin Tinubu ta kashe Naira biliyan 758 kan basussukan fansho, ta ƙara kuɗin masu ritaya

Next Post

Cewar Shettima: Noman alfafa a Jigawa zai taimaka wajen kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Cewar Shettima: Noman alfafa a Jigawa zai taimaka wajen kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya

Cewar Shettima: Noman alfafa a Jigawa zai taimaka wajen kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!