Ƙaramin Ministan Raya Yankuna, Alhaji Uba Maigari, ya bayyana cewa yana da cikakken yaƙinin cewa babu wata jam’iyyar adawa ko haɗakar jam’iyyun siyasa da za ta iya hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a babban zaɓen shekarar 2027.
Maigari ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da aka gudanar a Jalingo, jihar Taraba.
A cewar sa, har yanzu jam’iyyun adawa ba su gabatar da wata gamsasshiyar mafita da za ta iya rinjayar ‘yan Nijeriya su ƙi sake zaɓen Shugaba Tinubu ba.
“Zan iya tabbatar muku cewa nasarar da za a samu a zaɓen 2027 za ta kasance mai gagarumin rinjaye. Ku dubi ‘yan takarar adawa, ban da yawan sauya jam’iyya daga wannan zuwa waccan, me suka yi da zai sa ‘yan Nijeriya su zaɓe su? Babu komai,” inji shi.
Ministan ya ce gwamnatin Tinubu ta aiwatar da manufofi da ayyukan ci gaba da dama waɗanda, a ra’ayin sa, suka sanya APC cikin kyakkyawan matsayi na samun nasara a babban zaɓe mai zuwa.
Ya lissafo bunƙasa ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, bunƙasa jarin ɗan’adam da kuma gyare-gyaren tattalin arziki a matsayin wasu daga cikin nasarorin da gwamnatin ta samu.
“Shugaban Ƙasa ya aza tubalin samun gagarumar nasara a zaɓen 2027 ta hanyar aiwatar da tsare-tsaren ci gaba a fannoni daban-daban na ƙasar nan,” inji Maigari.
Da yake tsokaci kan halin da ake ciki a jihar Taraba, Ministan ya yaba wa Gwamna Agbu Kefas bisa ƙoƙarin sa na haɗa kan membobin APC da kuma inganta haɗin kai da bai wa kowa dama a cikin jam’iyyar.
Ya bayyana ƙwarin gwiwar sa kan jagorancin gwamnan, yana mai cewa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar za su ci gaba da ba shi goyon baya domin ya samar da ingantaccen shugabanci.
Haka kuma, Maigari ya yi watsi da zarge-zargen da ke cewa APC na amfani da hukumomin gwamnati wajen tsoratar da jam’iyyun adawa.
“Hukumomin gwamnati suna da nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora musu. Idan suna bincike ko kuma suna gayyatar mutane kan wasu sahihan batutuwa, bai kamata a ɗauki hakan a matsayin tsangwama ta siyasa kai tsaye ba,” inji shi.
Taron masu ruwa da tsaki na APC da aka gudanar a Jalingo na daga cikin matakan da jam’iyyar ke ɗauka na ƙarfafa haɗin kai a cikin ta da kuma shirye-shiryen tunkarar ayyukan siyasa masu zuwa a jihar.







