Dakarun rundunar Operation Haɗin Kai sun daƙile wani yunƙurin hari da mayaƙan ƙungiyar ISWAP suka kai a yankin Cross Kauwa da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa a Jihar Borno, inda suka kashe mai ɗaukar bidiyon ƙungiyar tare da ƙwato kyamarar bidiyo mai ɗauke da muhimman bayanai kan ayyukan ta.
Mai riƙon muƙamin Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Kyaftin Muhammed Goni, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi.
A cewar sa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:20 na daren jiya Asabar lokacin da mayaƙan ISWAP suka yi yunƙurin kutsawa sansanin sojoji domin sace magungunan cutar kwalara.
Sai dai, inji sanarwar, dakarun sun gano shirin tun kafin maharan su cimma manufar su, inda suka buɗe musu wuta mai ƙarfi. Hakan ya tilasta wa mayaƙan tserewa bayan sun yi asarar mutane da dama.
Bayan kammala artabun, sojojin sun ƙwato wata kyamarar bidiyo kirar Sony, harsasai, kayan yaƙi da kuma wasu kayayyakin mayaƙan ƙungiyar.
Sanarwar ta ce binciken farko da aka gudanar kan bidiyon da ke cikin kyamarar ya nuna cewa hare-haren ISWAP na samun jagoranci daga manyan kwamandojin ƙungiyar huɗu tare da taimakon wasu ƙwararrun ‘yan ta’adda uku daga ƙasashen waje.
Daga cikin waɗanda aka gano akwai Abu Ishaq, wani Bafalasɗine da ake zargin shi ne babban mai horas da mayaƙan ISWAP, da kuma Abu Thaiba, wani ɗan ƙasar Morokko da ke aiki a matsayin likitan ƙungiyar. Haka kuma, an gano wani ɗan ƙasar Larabawa na uku, sai dai har yanzu ba a tantance ƙasar da ya fito ba.

Rundunar ta bayyana cewa bayanan da aka samu sun ƙara tabbatar da rahotannin sirri da ke nuna cewa ISWAP tana ci gaba da samun tallafi da ƙwararrun ma’aikata daga wajen Nijeriya.
Har ila yau, sanarwar ta ce bayanan sirrin sun nuna yiwuwar ɓarkewar cutar kwalara a sansanonin ƙungiyar, abin da ake zargin ya sa mayaƙan suka yi yunƙurin sace magungunan cutar daga sansanin sojoji.
Ta ƙara da cewa hotunan tauraron ɗan’adam da sauran bayanan sirri sun tabbatar da cewa mayaƙan sun kwashe gawarwakin wasu daga cikin waɗanda aka kashe tare da janye waɗanda suka jikkata daga filin artabu.
Sai dai, sojoji biyu sun samu raunukan harbin bindiga a yayin musayar wutar, kuma an garzaya da su ta jirgin sama domin samun kulawar likitoci. Rundunar ta ce suna ci gaba da jinya cikin yanayi mai kyau.
Operation Hadin Kai ta jaddada aniyar ta ta ci gaba da gudanar da hare-haren da suka dace domin lalata ragowar sansanonin ‘yan ta’adda da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa-maso-Gabashin Nijeriya.







