• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Sojoji sun kashe fitaccen shugaban ‘yan bindiga Sani Yellow a Zamfara

New Citizen Hausa by New Citizen Hausa
July 12, 2026
in Tsaro
A A
0
Sojoji sun kashe fitaccen shugaban ‘yan bindiga Sani Yellow a Zamfara
Sojoji suna jan gawar Sani Yellow a ƙasa. A dama kuma shi ne a lokacin wani taron sulhu

Sojoji suna jan gawar Sani Yellow a ƙasa. A dama kuma shi ne a lokacin wani taron sulhu

GUSAU – Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun tabbatar da kashe wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga da aka fi sani da Kachalla Sani Yellow a Jihar Zamfara, bayan wani samame da aka gudanar bisa bayanan sirri.

Majiyoyin suka ce an kashe Sani Yellow ne a wani shiri na musamman da dakarun tsaro na haɗaka, masu aiki tare da jami’an tsaro, suka aiwatar bayan samun bayanan sirri daga mazauna yankin.

An ce an yi masa kwanton ɓauna ne yayin da ake zargin ya je wata kasuwa domin karɓar kuɗaɗen shanun da aka sace da kuma kuɗin fansa daga mutanen da aka yi garkuwa da su.

Bayan kashe shi, rahotanni sun ce wasu daga cikin dakarun haɗakar sun ja gawar sa a ƙasa kan babur yayin da suke murnar nasarar da suka samu kan ɗaya daga cikin shugabannin ‘yan bindigar da suka daɗe suna addabar yankin.

A cewar majiyoyin, rundunar haɗakar ta ƙunshi masu sa-kai daga al’umma da kuma wasu tsofaffin mayaƙan Boko Haram da suka tuba, waɗanda ke aiki tare da jami’an tsaro wajen tattara bayanan sirri da kuma kai hare-hare kan sansanonin ‘yan bindiga a wasu yankunan Arewa-maso-Yamma.

An bayyana Sani Yellow a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagororin ‘yan bindiga da ke gudanar da hare-hare a dazukan ƙananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Maru da kuma wasu sassan Jihar Zamfara.

Ana zargin sa da jagorantar hare-haren da suka yi sanadin rasa rayuka, sace mutane domin neman kuɗin fansa, satar dabbobi da kuma tilasta dubban mazauna karkara barin muhallan su.

Wasu majiyoyin al’umma sun kuma zarge shi da jagorantar ƙungiyar da ke cin zarafin waɗanda aka sace, ciki har da mata, musamman idan iyalan su sun gaza biyan kuɗin fansa.

Rahotanni sun kuma nuna cewa Sani Yellow yana da alaƙa da marigayi Kachalla Yellow Ɗanbokolo, wani shahararren shugaban ‘yan bindiga da aka ruwaito an kashe a shekarar 2025 tare da sama da mayaƙan sa 170 a wani samame da dakarun sa-kai na yankin Shinkafi suka kai.

Bayan aukuwar lamarin, jami’an tsaro sun ƙara tsaurara matakan sa-ido a yankunan da abin ya shafa domin daƙile duk wata yiwuwar harin ramuwar gayya daga sauran ‘yan ƙungiyar.

Haka kuma an ƙara tura jami’an tsaro zuwa wuraren da ake ganin na cikin haɗari domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance game da kashe Sani Yellow ba.

Tags: 'yan bindigaSani Yellowsojojita'addanciZamfara
Previous Post

An gurfanar da tsohuwar ma’aikaciyar banki a kotu kan zargin satar Naira miliyan 294.5 a Legas

Next Post

Sojoji sun kashe mai ɗaukar bidiyon ISWAP, sun gano muhimman bayanai kan ƙwararrun ‘yan ta’addan ƙasashen waje

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Sojoji sun kashe mai ɗaukar bidiyon ISWAP, sun gano muhimman bayanai kan ƙwararrun ‘yan ta’addan ƙasashen waje

Sojoji sun kashe mai ɗaukar bidiyon ISWAP, sun gano muhimman bayanai kan ƙwararrun 'yan ta'addan ƙasashen waje

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!