An gurfanar da wata tsohuwar ma’aikaciyar wani bankin zamani, Madam Chinonso Akujobi, a gaban Babbar Kotun Jihar Legas da ke zaman ta a Ikeja bisa zargin satar kuɗaɗe har Naira miliyan 294.5.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC reshen Legas Zonal Directorate 2 ce ta gurfanar da Akujobi a ranar Alhamis a gaban Mai Shari’a I.O. Ijelu kan tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi zargin sata, wanda adadin ta ya kai N294,595,992.
A cewar EFCC, ana zargin Akujobi ta aikata laifukan ne tsakanin watan Janairu da Disamba na shekarar 2025 lokacin da take aiki a Bankin Access.
Hukumar ta bayyana wa kotun cewa Akujobi ta yi zargin tura kuɗaɗe daga asusun babbar ma’ajiyar bankin ba tare da izini ba zuwa wani asusun Bankin Access mai lamba 0036668871, wanda ke ɗauke da sunayen Chinonso A., Uchechi A. da Florence A.
EFCC ta ce ɗaya daga cikin tuhumar na zargin cewa ta karkatar da N109,325,566.86 domin amfanin kan ta ba tare da izini ba, lamarin da hukumar ta ce ya saɓa wa Sashe na 280 kuma ake hukunta shi ƙarƙashin Sashe na 287 na Dokar Laifuffuka ta Jihar Legas ta shekarar 2015.
Akujobi ta musanta dukkan tuhume-tuhumen guda biyar lokacin da aka karanta mata su a kotu.
Bayan ta musanta zargin, lauyan masu gabatar da ƙara, S.M. Yabo, ya roƙi kotun da ta sanya ranar fara shari’a tare da bayar da umurnin tsare wadda ake tuhuma a gidan gyaran hali har zuwa lokacin ci gaba da shari’ar.
Daga nan Mai Shari’a Ijelu ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 8 ga Oktoba, 2026 domin sauraron buƙatar beli da kuma fara shari’ar.
Kotun ta kuma ba da umurnin a tsare Akujobi a Gidan Gyaran Hali na Ikoyi har zuwa lokacin da za a ci gaba da shari’ar.








