• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen yi wa kowane ɗan Nijeriya rajistar shaidar ɗan ƙasa ta dijital

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
July 8, 2026
in Labarai
A A
0
Gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen yi wa kowane ɗan Nijeriya rajistar shaidar ɗan ƙasa ta dijital
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da Babbar Darakta kuma Babbar Jami'ar Gudanarwa ta Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC), Dakta Abisoye Coker-Odusote, da tawagar ta, lokacin da suka kai masa ziyarar girmamawa a ofishin sa a Abuja yau Laraba 

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da Babbar Darakta kuma Babbar Jami'ar Gudanarwa ta Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC), Dakta Abisoye Coker-Odusote, da tawagar ta, lokacin da suka kai masa ziyarar girmamawa a ofishin sa a Abuja yau Laraba 

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da cewa an yi wa kowane ɗan Nijeriya rajistar shaidar ɗan ƙasa ta dijital a faɗin ƙasar, ta hanyar ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai da Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC).

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja yayin da ya karɓi baƙuncin Babbar Darakta kuma Babbar Jami’ar Gudanarwa ta NIMC, Dakta Abisoye Coker-Odusote, da tawagar ta, waɗanda suka kai masa ziyarar girmamawa domin gabatar da muhimman tanade-tanaden sabuwar Dokar NIMC ta 2026.

Ministan ya ce ingantaccen tsarin tantance shaidar ‘yan ƙasa yana da matuƙar muhimmanci wajen kyautata shugabanci, tsara cigaban ƙasa, bunƙasa harkokin kuɗi, haɓaka sauyin fasahar zamani da kuma aiwatar da Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce: “Tsarin tantance shaidar ‘yan ƙasa shi ne ginshiƙin ajandar sauye-sauyen Shugaban Ƙasa. Domin idan za a aiwatar da gyare-gyare, dole ne a san waɗanda ake yi wa. Idan ba a san adadin jama’a ba, da tsarin yawan su da yadda suka kasu, ta yaya za a tsara musu ingantattun tsare-tsare?”

Idris ya yaba wa shugabancin Dakta Coker-Odusote, yana mai cewa yi wa sama da mutum miliyan 136 rajista babban cigaba ne, amma har yanzu akwai kusan mutum miliyan 100 da ba a yi wa rajista ba.

Ya ce: “Mutum miliyan 136 da aka riga aka yi wa rajista babban cigaba ne, amma har yanzu akwai kusan ‘yan Nijeriya miliyan 100 da suka rage, kuma su ma ya kamata a yi musu rajista. Kowane ɗan Nijeriya ya cancanci a saka shi cikin tsare-tsaren cigaban ƙasa.”

Ministan ya ce cimma burin yi wa kowa rajista yana buƙatar ci gaba da wayar da kan jama’a, musamman a matakin ƙananan hukumomi da al’ummomi. Don haka ya buƙaci NIMC da ta ƙara haɗin gwiwa da Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), wadda ke da ofisoshi a dukkan ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan.

Ya ce: “Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa ita ce mafi dacewa wajen isa ga al’ummomin karkara. Ina roƙon ku da ku ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar ku da NOA domin mu duka mu tabbatar da cewa kowane ɗan Nijeriya ya fahimci muhimmancin tsarin shaidar ‘yan ƙasa.”

Haka kuma ya yaba wa NIMC bisa yadda ta kiyaye bayanan jama’a, yana mai cewa babu wani rahoton kutsen da ya yi sanadin fallasa bayanan masu rajista.

Ya ƙara da cewa: “Na yi farin cikin jin cewa ba ku taɓa fuskantar matsalar kutsen bayanai ko da sau ɗaya ba. Kare sirrin bayanai, gudanar da aiki cikin gaskiya da kuma amincewar jama’a su ne ginshiƙan nasarar tsarin shaidar dijital, kuma za mu ci gaba da amfani da dukkan kafafen yaɗa labarai na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai wajen tallafa wa shirye-shiryen wayar da kan jama’a.”

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da Babbar Darakta kuma Babbar Jami’ar Gudanarwa ta Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC), Dakta Abisoye Coker-Odusote, da sauran jami’ai

Tun da farko, Darakta Janar na Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA), Mallam Lanre Issa-Onilu, ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da tallafa wa NIMC wajen wayar da kan jama’a ta hanyar cibiyoyin ta da ke faɗin ƙasar nan.

Ya ce: “Mun san muna aiki tare, amma ina fatan za ku ci gaba da tuntuɓar mu domin mu ga yadda za mu ƙara ba da gudunmawa. Muna da wakilci a wuraren da kuke son zuwa domin wayar da kan jama’a da faɗakar da su.”

A nata jawabin, Babbar Darakta ta NIMC, Dakta Abisoye Coker-Odusote, ta ce sabuwar Dokar NIMC ta 2026 ta sabunta tsarin kula da shaidar ɗan ƙasa a Nijeriya, inda ta ƙunshi tanade-tanade kan kare bayanai, tsaron intanet, inganta tsarin bayanan gwamnati na zamani da kuma ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin dijital.

Ta ce: “Shugaban Ƙasa ya umurce mu da mu fara rajistar jama’a daga unguwa zuwa unguwa, domin yana son tabbatar da cewa mutanen karkara da na matakin al’umma ba a hana su cin gajiyar duk wani shirin tallafin gwamnati ba.”

Ta bayyana cewa hukumar ta fara gangamin rajista a dukkan unguwanni 8,809 na Nijeriya domin tabbatar da cewa an yi wa kowane ɗan ƙasa rajista, ciki har da mata, yara, masu naƙasa, mazauna karkara, ‘yan gudun hijira, baƙin da ke zaune bisa doka da kuma ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje.

A nasa jawabin, Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na NIMC, Dakta Kayode Adegoke, ya ce sabuwar dokar ta sauya tsarin kula da shaidar ɗan ƙasa a Nijeriya baki ɗaya.

Ya ce: “NIMC ta wuce matsayin mai adana bayanai kawai, ta zama babbar hukuma ta ƙasa da ke da alhakin kula da tsarin shaidar dijital. A yanzu, NIMC ita ce kaɗai hukumar da aka ba ikon kula da tsarin shaidar dijital a Nijeriya.”

Ya ƙara da cewa dokar ta samar da tsarin doka na Digital Public Infrastructure (DPI) da Public Key Infrastructure (PKI), tare da ƙarfafa kariyar bayanan jama’a da faɗaɗa amfani da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) a ayyukan gwamnati da kamfanoni masu zaman kan su.

A cewar sa, NIMC ta haɗa tsarin ayyukan ta da fiye da ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati 250, tare da ƙaddamar da sababbin fasahohi da suka inganta ayyukan rajista tare da rage lokacin da ake ɗauka wajen yi wa jama’a rajista.

Ziyarar ta samu halartar Darakta Janar na NOA, Mallam Lanre Issa-Onilu; Babbar Darakta kuma Babbar Jami’ar Gudanarwa ta NIMC, Dakta Abisoye Coker-Odusote; Daraktan Sashen Samarwa, Wallafe-wallafe da Adana Takardu, Mista Ibidapo Okunnu; Mataimakiyar Darakta mai kula da Hulɗa da Jama’a da Ladabi, Misis Fatoke Folasade, da sauran manyan jami’an Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai da na Hukumar NIMC.

Previous Post

Sojoji sun ceto mutanen da aka sace, sun daƙile harin ISWAP, sun kama masu kai wa ‘yan ta’adda kayan aiki a Arewa-maso-gabas

Next Post

Gani Ya Kori Ji: Aikin layin dogo na Kano-Maraɗi zai sauya tattalin arzikin Arewa — Jami’ai

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Gani Ya Kori Ji: Aikin layin dogo na Kano-Maraɗi zai sauya tattalin arzikin Arewa — Jami’ai

Gani Ya Kori Ji: Aikin layin dogo na Kano-Maraɗi zai sauya tattalin arzikin Arewa — Jami'ai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!