• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci a binciki kisan shugaban Miyetti Allah na Binuwai

ALI KANO by ALI KANO
June 27, 2026
in Tsaro
A A
0
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci a binciki kisan shugaban Miyetti Allah na Binuwai
Mariganyi Alhaji Arɗo Risku Muhammad

Mariganyi Alhaji Arɗo Risku Muhammad

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Nijeriya da su gaggauta gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci kan kisan gillar da aka yi wa Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Nijeriya  (MACBAN) na Jihar Binuwai, Alhaji Arɗo Risku Muhammad, da wani abokin sa.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Asabar, ƙungiyar ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici matuƙa, tana mai cewa abin damuwa ne yadda halartar taron zaman lafiya ya koma tarko na mutuwa.

Amnesty International ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa hukumomin Ƙaramar Hukumar Ohimini sun gayyaci Arɗo Risku zuwa wani taron tsaro da aka gudanar ranar Juma’a, 26 ga Yuni, 2026, domin tattauna batutuwan da suka shafi zaman lafiya da tsaro a yankin.

Ƙungiyar ta ce kimanin awa guda bayan kammala taron, yayin da marigayin da abokin sa suke kan hanyar su ta komawa gida, sai wasu da ake zargin mahara ne suka tare su a ƙauyen Okudu, inda aka ce sun harbe su sau da dama kafin daga bisani suka kashe su.

Amnesty International ta ce hotunan gawarwakin waɗanda aka kashe da ta samu sun nuna mummunan ta’addanci da ya wuce misali.

Ƙungiyar ta bayyana cewa wannan hari ya biyo bayan wani hari da aka kai wa ɗaya daga cikin ‘ya’yan marigayin mako guda da ya gabata, wanda aka bar shi da munanan raunuka masu barazana ga rayuwar sa.

Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa rashin gudanar da cikakken bincike kan lamarin zai ƙara ƙarfafa al’adar rashin hukunta masu aikata laifuffuka.

Ta ce: “Ba za a bari a yi biris da wannan lamari ba. Dole ne hukumomin Nijeriya su gaggauta gudanar da bincike mai inganci kan wannan kisan tare da gurfanar da duk waɗanda ake zargi da hannu a ciki.”

Ƙungiyar ta buƙaci hukumomi da su tabbatar da cewa iyalan waɗanda aka kashe sun samu adalci da kuma hanyoyin biyan haƙƙin su.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, gwamnatin Jihar Binuwai da hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa kan zarge-zargen da Amnesty International ta yi ba.

Tags: Arɗo Risku MuhammadBinuwaikisata'addancitsaro
Previous Post

Tinubu ya rattaba hannu kan Dokar NIMC ta 2026, ya ƙarfafa tsarin shaidar ɗan ƙasa na dijital

Next Post

Yadda CBN ke ƙoƙarin rage yawan tsabar kuɗi naira tiriliyan 5.2 da har yanzu ke hannun jama’a 

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Next Post
Yadda CBN ke ƙoƙarin rage yawan tsabar kuɗi naira tiriliyan 5.2 da har yanzu ke hannun jama’a 

Yadda CBN ke ƙoƙarin rage yawan tsabar kuɗi naira tiriliyan 5.2 da har yanzu ke hannun jama'a 

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!