• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Yadda CBN ke ƙoƙarin rage yawan tsabar kuɗi naira tiriliyan 5.2 da har yanzu ke hannun jama’a 

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
June 29, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Yadda CBN ke ƙoƙarin rage yawan tsabar kuɗi naira tiriliyan 5.2 da har yanzu ke hannun jama’a 
Tulin kuɗi

Tulin kuɗi

Wani binciken da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar kwanan nan, ya bayyana cewa yanzu haka tsabar kuɗin da ke wajen tsarin bankuna a Nijeriya ya ƙaru zuwa Naira tiriliyan 5.19 a watan Mayu 2026, duk da ci gaba da ƙoƙarin da CBN ɗin ke yi na bunƙasa amfani da biyan kuɗi ta hanyar zamani da kuma shigar da mutane cikin harkokin hadahadar kuɗi bisa tsarin ajiyar kuɗaɗe a banki da kuma dijital.

Sababbin alƙaluman ƙididdigar kuɗi da lamuni daga CBN sun nuna cewa kuɗin da ke wajen bankuna ya ƙaru da naira biliyan 109.34, wato kashi 2.15 cikin ɗari, daga naira tiriliyan 5.08 a watan Afrilu 2026 zuwa naira tiriliyan 5.19 a watan Mayu.

Wannan adadi ya kuma nuna ƙarin naira biliyan 559.16, ko kuma kashi 12.07 cikin ɗari, idan aka kwatanta da naira tiriliyan 4.63 da aka samu a watan Mayu 2025, abin da ke nuna cewa har yanzu dai ‘yan Nijeriya suna riƙe da maƙudan kuɗi a waje da tsare hanyoyin banki na hukuma.

Bayanan sun kuma nuna cewa jimillar kuɗin da ke yawo a ƙasa ya tashi daga naira tiriliyan 5.65 a watan Afrilu zuwa naira tiriliyan 5.69 a watan Mayu 2026, wanda ya nuna ƙarin naira biliyan 43.59, ko kashi 0.77 cikin ɗari. Idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kuɗin da ke yawo ya ƙaru da naira biliyan 675.19, wato kashi 13.46 cikin ɗari, daga naira tiriliyan 5.01 a watan Mayu 2025.

Wannan yana nufin kashi 91.27 cikin ɗari na duk kuɗin da ke yawo a Nijeriya suna hannun mutane ne a wajen bankuna a watan Mayu 2026. Wannan ya fi kashi 90.03 da aka samu a watan Afrilu 2026, amma ya ragu daga kashi 92.40 da aka samu a watan Mayu 2025.

Wannan yanayi na nuna cewa duk da ɗan raguwar kaso idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, har yanzu tattalin arzikin Nijeriya yana dogaro sosai da amfani da tsabar kuɗi.

Wannan lamari ya faru ne duk da yaɗuwar hanyoyin biyan kuɗi na zamani, yawaitar hanyar hadahada ta wayar hannu, ayyukan kamfanonin fasahar kuɗi (fintech), da kuma ƙoƙarin CBN na rage dogaro da tsabar kuɗi a tattalin arziki.

Bayanan sun kuma nuna cewa ajiyar bankuna ya ragu daga naira tiriliyan 34.60 a watan Afrilu zuwa naira tiriliyan 33.76 a watan Mayu 2026, wato raguwar naira biliyan 840.77 ko kashi 2.43 cikin ɗari.

Sai dai idan aka kwatanta da watan Mayu 2025, ajiyar bankuna ya ƙaru da naira tiriliyan 2.90, wato kashi 9.39 cikin ɗari, daga naira tiriliyan 30.86, wanda ke nuna ƙaruwar ƙarfin kuɗin da bankuna ke da shi cikin shekara guda.

A watan Disamba 2025, kuɗin da ke wajen bankuna ya kai naira tiriliyan 5.41 kafin ya sauka zuwa naira tiriliyan 5.25 a watan Janairu 2026 da kuma naira tiriliyan 5.19 a watan Fabrairu. Daga baya ya sauka zuwa naira tiriliyan 5.08 a watan Afrilu kafin ya sake ƙaruwa a watan Mayu.

Wannan tsari yana nuna cewa yawan kuɗin da ke wajen bankuna har yanzu yana da yawa, duk da sauye-sauyen da ake samu daga wata zuwa wata.

Yawan kuɗin da ake riƙewa a wajen bankuna na iya zama ƙalubale ga manufofin kuɗi na gwamnati, domin kuɗin da ba ya shiga tsarin banki yana rage damar bankuna wajen tara ajiya da bayar da rance ga jama’a da ‘yan kasuwa.

Rahotanni sun nuna cewa CBN ya ƙaddamar da wani babban shiri na dawo da kuɗin da ke wajen tsarin banki zuwa hanyoyin kuɗi na hukuma tare da faɗaɗa shigar mutane cikin harkokin kuɗi ta hanyar shigar da sabbin mutane miliyan 50 cikin tsarin kuɗi nan da shekarar 2028.

Wannan buri na daga cikin manufofin da Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana a Abuja, yayin da babban bankin ke ƙoƙarin ƙarfafa hanyoyin biyan kuɗi ta zamani, ƙara amincewar jama’a ga tsarin kuɗi, rage dogaro da tsabar kuɗi, da kuma mayar da Nijeriya cibiyar biyan kuɗi a Afirka.

Cardoso ya bayyana cewa CBN na da niyyar rage kuɗin da ke wajen tsarin banki zuwa ƙasa da kashi 40 cikin ɗari na duk kuɗin da ke yawo kafin shekarar 2028.

Ya ce: “Ina son ganin yanayi inda za mu rage kuɗin da ke wajen tsarin banki zuwa ƙasa da kashi 40 cikin ɗari na kuɗin da ke yawo.”

Irin wannan sauyi zai iya taimakawa wajen inganta yadda manufofin kuɗi ke aiki, ƙara yawan kuɗin da bankuna ke da shi, ƙarfafa bayar da rance da kuma taimaka wa masu ba da lamuni su tallafa wa ci gaban tattalin arziki.

Tags: bankiCBNNaira
Previous Post

Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci a binciki kisan shugaban Miyetti Allah na Binuwai

Next Post

Manyan nasarori 25 da CBN ya samu cikin watanni shidan farko na 2026

Related Posts

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ƙananan ’yan kasuwa 5,000 ‘sun amfana da shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya a Borno’

November 25, 2026
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin tallafa wa manoma 500,000

November 22, 2026
Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tinubu ya bayyana shirin samar da motoci masu amfani da gas guda 300, tare da alƙawarin rage kuɗin sufuri da kashi 40

November 19, 2026
CBN ya naɗa kamfanoni takwas domin kula da fitar da ɗanyen mai da iskar gas
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN da NNPCL sun ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa tattalin arziki da samar da kuɗaɗen zuba jari a ɓangaren makamashi

November 18, 2026
CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya fitar da sabbin ƙa’idojin adana bayanan kwastomomi ga bankunan Access, Zenith, OPay, PalmPay da sauran su

November 17, 2026
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoba – NBS

November 16, 2026
Next Post
Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

Manyan nasarori 25 da CBN ya samu cikin watanni shidan farko na 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!