• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Tinubu ya rattaba hannu kan Dokar NIMC ta 2026, ya ƙarfafa tsarin shaidar ɗan ƙasa na dijital

IRO MAMMAN by IRO MAMMAN
June 26, 2026
in Labarai
A A
0
Tinubu ya rattaba hannu kan Dokar NIMC ta 2026, ya ƙarfafa tsarin shaidar ɗan ƙasa na dijital
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, yana sanya hannu kan Dokar Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa ta Ƙasa (NIMC) ta shekarar 2026, a Fadar Shugaban Kasa a Abuja ranar Juma'a 

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, yana sanya hannu kan Dokar Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa ta Ƙasa (NIMC) ta shekarar 2026, a Fadar Shugaban Kasa a Abuja ranar Juma'a 

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan Dokar Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa ta Ƙasa (NIMC) ta shekarar 2026 a jiya Juma’a, lamarin da ya kafa sabon tsarin shaidar ɗan ƙasa na zamani, mai tsaro kuma mai bai wa kowa dama, domin tallafa wa bunƙasar tattalin arzikin dijital na Nijeriya.

A cikin sanarwar da ya fitar, Shugaban Ƙasar ya ce sabuwar dokar ta maye gurbin tsohon tsarin doka da aka yi amfani da shi wajen gudanar da tsarin tantance shaidar ‘yan ƙasa na kusan shekaru ashirin, yana mai cewa tsohuwar dokar ba ta ƙara dacewa da burin Nijeriya na wannan zamani ba.

Tinubu ya ce sabuwar dokar ta bai wa Hukumar NIMC muhimmiyar rawa a Tsarin Ababen More Rayuwa na Jama’a na Dijital da kuma Tsarin Maɓallan Tsaro na Jama’a na Ƙasa, wanda zai samar da ingantaccen tushe na tabbatar da sahihancin shaidar mutane, gudanar da mu’amaloli cikin tsaro, sanya hannu ta hanyar dijital da kuma bunƙasa tattalin arzikin dijital.

Ya ce dokar ta ƙara ƙarfafa kariyar bayanan sirri na ‘yan ƙasa ta hanyar hana samun damar amfani da bayanan ba tare da ƙa’ida ba, amfani da su fiye da manufar da aka tattara su saboda ita, ko sarrafa su ba tare da yardar mai bayanan ko bin ƙa’idar doka ba.

“Ya zama wajibi a kare sirrin ‘yan Nijeriya, kuma wannan doka ta tabbatar da hakan,” inji Shugaba Tinubu.

Ya bayyana cewa a ƙarƙashin sabuwar dokar, Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) za ta zama muhimmiyar hanyar samun manyan ayyuka da hidimomi, ciki har da neman fasfo, rajistar masu zaɓe, buɗe asusun banki, cinikin filaye, ayyukan sadarwa, fansho, inshora, biyan haraji, samun rancen kuɗi da sauran ayyukan gwamnati.

Shugaban Ƙasar ya sake jaddada manufar gwamnati ta tabbatar da cewa kowane ɗan Nijeriya yana da shaida guda ɗaya mai inganci, yana mai bayyana hakan da kalmomin, “Mutum ɗaya. Shaida ɗaya. Lamba ɗaya.”

Tinubu ya ce ya bayar da takamaiman umurni cewa sabuwar dokar ta kare masu rauni, waɗanda ba su da cikakken damar samun ayyuka da kuma ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje, yana mai jaddada cewa bai kamata a hana kowane ɗan ƙasa samun damar cigaba saboda rashin ingantacciyar shaida ba.

Ya ƙara da cewa dokar ta inganta tsarin shugabanci a NIMC ta hanyar faɗaɗa wakilci a kwamitin gudanarwar hukumar, ƙarfafa tsarin riƙon amana da kuma tanadar da hukunci mai tsauri ga masu aikata laifukan satar bayanan shaida, yin rajista fiye da sau ɗaya, shiga tsarin ba tare da izini ba da kuma cin zarafin tsarin shaidar ɗan ƙasa.

“Ba za mu lamunci masu ƙirƙirar shaidun bogi, masu satar shaidar wasu ko masu cin zarafin wannan tsari ba,” inji shugaban.

Tinubu ya yaba wa Majalisar Dokoki ta Tarayya, Ministan Harkokin Cikin Gida, Hukumar NIMC, abokan hulɗar cigaba da dukkan ‘yan Nijeriya bisa gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da samar da wannan muhimmiyar doka.

Ya bayyana dokar a matsayin wani babban cigaba da zai taimaka wajen gina Nijeriya mai cikakken tsaro, wadda kowa yake da damar cin moriyar ta kuma mai bunƙasar tattalin arziki, tare da ciyar da manufofin gwamnatin sa na Renewed Hope Agenda gaba.

Tags: Dokar NIMC ta 2026dokar ɗan ƙasaShugaba Bola Ahmed Tinubu
Previous Post

An kashe shugaban Miyetti Allah na Binuwai a kwanton ɓauna bayan taron sulhu

Next Post

Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci a binciki kisan shugaban Miyetti Allah na Binuwai

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci a binciki kisan shugaban Miyetti Allah na Binuwai

Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci a binciki kisan shugaban Miyetti Allah na Binuwai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!