Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kan ta (ICPC) ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, tare da tsohon Babban Mai Ba Shi Shawara, Mista Jimi Adebisi Lawal, da wasu kamfanoni biyar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna bisa zargin cin hanci da rashawa, dulmiyar kuɗaɗe da sauran laifuka masu alaƙa da hakan.
An gurfanar da waɗanda ake tuhuma ne a kan sabuwar takardar tuhume-tuhume mai ƙunshe da laifuka 11, mai lamba FHC/KD/93C/2026, a gaban Mai Shari’a Hauwa’u Buhari.
Kamfanonin da aka ambata a cikin ƙarar sun haɗa da Singularity Network Security Limited, Solar Life Nigeria Limited, Knowledge Investment Nigeria Limited, Intercellular Nigeria Limited da Noble Coast Resources Limited.
A cewar ICPC, Bashir El-Rufai, wanda yayan tsohon gwamnan ne kuma ake nema ruwa a jallo, yana ɗaya daga cikin waɗanda aka ambata a tuhume-tuhumen.
Hukumar ta yi zargin cewa El-Rufai, lokacin da yake gwamnan Jihar Kaduna, ya amince ba bisa ƙa’ida ba da bayar da kwangilar bincike, tsarawa, zane na ƙarshe da girka na’urorin sa ido na CCTV a cikin birnin Kaduna, wadda aka sake tantance kuɗin ta zuwa Naira biliyan 8.68.
ICPC ta ce an bai wa kamfanin Singularity Network Security Limited wannan kwangilar duk da cewa, a cewar ta, ba shi da ƙwarewa ko cancantar da ake buƙata, lamarin da ya saɓa wa dokokin bayar da kwangilolin gwamnati.
Hukumar ta kuma yi zargin cewa an riƙa tura kuɗaɗen da aka samu daga wannan aiki ta hanyar wasu kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane, inda tuhume-tuhumen suka haɗa da mallaka, karɓa da kuma safarar kuɗaɗen da ake zargin an samo su ne daga haramtattun ayyuka, waɗanda suka kai biliyoyin nairori.
A cewar ICPC, waɗanda ake tuhuma sun karɓi ko suka mallaki fiye da Naira biliyan biyu ta hanyar mu’amaloli da suka shafi kamfanonin Singularity Network Security Limited, Solar Life Nigeria Limited, Knowledge Investment Nigeria Limited, Intercellular Nigeria Limited da Noble Coast Resources Limited tsakanin shekarun 2017 da 2022.
Hukumar ta bayyana cewa laifukan da ake zargin sun saɓa da tanade-tanaden Dokar Hanawa da Haramta Dulmiyar Da Kuɗaɗe ta shekarar 2022.
Ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen ya zargi El-Rufai da taimakawa wajen aikata cin hanci da rashawa ta hanyar amincewa da bayar da kwangilar CCTV ga wani kamfani da ake zargin bai cika sharuɗɗan cancanta ba, wanda hakan ya saɓa wa tanade-tanaden doka.
Lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen a kotu, El-Rufai da Lawal sun musanta aikata dukkan laifukan da ake zargin su da su.
Daga nan ne Mai Shari’a Hauwa’u Buhari ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 1 ga Yuli 2026 domin yanke hukunci kan buƙatar bayar da belin waɗanda ake tuhuma.







