Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta gurfanar da wasu mutane 24 a gaban Kotun Majistare da ke mahaɗar NDA a Kaduna bisa zargin su da hannu a kisan gillar da aka yi wa wata mata a Maraban Jos.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Mansir Hassan, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar yau Talata a Kaduna.
Ya ce an tuhumi waɗanda ake zargin da laifukan haɗa baki domin aikata laifi, tunzura tarzomar jama’a, aikata ɓarna, lalata kadarorin gwamnati da na ‘yan sanda, da kuma kisan kai.
A cewar sa, gurfanar da waɗanda ake zargin ya biyo bayan cikakken bincike da aka gudanar kan lamarin da ya faru a ranar 21 ga Yuni 2026, inda ake zargin wani taron jama’a da suka fusata suka kashe matar bayan an fitar da ita daga hannun ‘yan sanda.
Hassan ya ce an fara sauraron shari’ar a gaban kotun, sannan aka ɗage ta zuwa ranar 21 ga Yuli domin ci gaba da shari’ar.
Ya ƙara da cewa kotun ta bayar da umurnin tsare dukkan waɗanda ake zargin a gidan gyaran hali har sai an kammala shari’ar.
Kakakin rundunar ya ce rundunar ta yi Allah-wadai da ɗaukar doka a hannu da kuma hukunta mutane ba tare da bin ƙa’ida ba, yana mai gargaɗin cewa duk wanda ya ɗauki doka a hannun sa za a kama shi kuma a gurfanar da shi bisa tanadin doka.
Ya kuma bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da binciken sama da wasu mutum 100 da ake zargin suna da hannu a lamarin.
“Za a kuma gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a gaban kotu,” inji shi.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, CP Muhammad Rabi’u, ya tabbatar wa da al’umma cewa rundunar ta himmatu wajen tabbatar da adalci ga mariganyiyar tare da ci gaba da wanzar da doka da oda a faɗin jihar.
Ya buƙaci jama’a da su riƙa kai rahoton laifuka ko koke-koken su ta hanyoyin da doka ta tanada maimakon amfani da tashin hankali.
Rundunar ‘yan sandan ta sake jaddada aniyar ta ta tabbatar da cewa an hukunta duk masu hannu a wannan lamari, tare da kira ga mazauna jihar da su ba hukumomin tsaro haɗin kai wajen yaƙi da laifuffuka da ayyukan da suka saɓa wa doka.







